fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Obasanjo

Kune shuwagabannin yau ba na gobe ba>>Obasanjo ya gayawa matasa

Kune shuwagabannin yau ba na gobe ba>>Obasanjo ya gayawa matasa

Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyanawa matasa cewa kada su yadda wani rika ce musu sune shuwagabannin Gobe.   Yace sune shuwagabannin yau wanda ya kamata ace suna jan ragamar kasarnan. Obasanjo yace matasan kada su yi kasa a Gwiwa su tashi su nemi Ilimi da kuma inganta harkar ilimin. Ya kuma bayyana cewa akwai yara Miliyan 14 da aka kasa Basu Ilimin da zai amfani rayuwarsu da al'umma. Obasanjo ya bayyana hakane yayin ganawa dashi ta kafar sadarwar zamani a wajan wani taron yaye malaman makarantu.