
Mawuyacin abune ganin babban mafarkina yazo karshe>> Odion Ighalo
Kantirakin aron tauraron dan wasan Najeriya a kungiyar Manchesrer United, Odion Ighalo zai kare ne a karshen wannan watan inda zai koma kungiyar shi ta kasar Sin Shanghai Shenhua amma duk haka yana fatan United zata lashe Premier League da kofin FA a wannan kakar.
Ighalo yayi nasarar zira kwallaye biyar a wasanni 23 daya bugawa Manchester United tunda ya koma kungiyar a rana ta karshe da za'a kulle kasuwar yan wasan watan janairu ta kakar bara, amma wasanni biyu kacal ya fara bugawa Manchester a wannan kakar tun bayan da suka siya Edinson Cavani.
Ighalo ya bayyana cewa "Mawuyacin abune gamin babban mafarkina yazo karshe, amma ina godiya ga Allah wanda shine ya cika min burina na taka leda a mashahuriyar kungiya Manchester United."
Dan wasan wanda ya buga mintina 9 a wannan kakar y...