fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Ogun

Ba fulani Makiyaya bane ke kawo mana hari a kasashen yarbawa ba>>Gwamnan Ogun ya fasa kwai

Ba fulani Makiyaya bane ke kawo mana hari a kasashen yarbawa ba>>Gwamnan Ogun ya fasa kwai

Siyasa
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana cewa ba fulani Makiyaya bane ke kaiwa jama'ar Yarbawa hari ba.   Ya bayyana hakane a fadar shugaban kasa, bayan ganawar da yayi dashi inda ya bashi ba'asi kan matsalar tsaron Jiharsa.   Yace Sarkin Filanin Yewa ya fishi ji  yarbanci kuma Fulani Makiyaya ba masu laifi bane, wasu 'yan ta'adda ne dake satar shanu suke kai musu hare-haren.   Yace suma kafafen watsa labarai basa kyautawa saboda yanda da an aikata abu sai su dorawa Fulanin.   “The Fulanis have lived with us in Ogun State for hundreds of years peacefully.   “The Sarkin Fulani from that particular corridor speaks Yoruba better than I do.   “One of the problems we have realised is ethnic profiling. Criminals are criminals. ...
Sunday Igboho: Fulani sun kai harin ramuwar gayya a jihar Ogun inda suka kashe mutane 2

Sunday Igboho: Fulani sun kai harin ramuwar gayya a jihar Ogun inda suka kashe mutane 2

Siyasa
A jiya, Alhamis wasu mahara da aka yi zargin Fulani Makiyaya ne sun kai hari a jihar Ogun inda suka kashe mutane 2.   Sun kai harinne wanda ake tsammanin na ramuwar gayyane akan harin da ake zargin dan taratsi, Sunday Igboho ya tunzura aka kai musu.   Harin ya wakana ne a karamar hukumar Yewa north dake jihar inda kuma bayan mutane 2 da suka rasu, wasu 4 sun bace ba'a san inda suke ba. Two corpses of locals have been found. Herders laid an ambush for locals on Owode Ketu-Ijoun-Tata road around 5a.m today and killed two. “Police from Eggua have evacuated the corpses.”
Yan sunda A jihar Ogun sun cafke wasu ‘yan kungiyar asiri Dauke da Gawa

Yan sunda A jihar Ogun sun cafke wasu ‘yan kungiyar asiri Dauke da Gawa

Uncategorized
Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta cafke wasu mutum biyar a jihar da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Asiri ne. Hukumar 'yan sandan jihar ce ta fitar da sanarwar cafke mutanan, biyo bayan wani bayanan sirri da rundunar ta samu a ranar litinin ta hannun ofishin hukumar dake yankin Sango. Wadanda ake zargin sun hada da Babatunde Shitu mai shekaru 25, Ayobami Morenikeji mai shekaru 15, da kuma Fidelis John, mai shekaru 23 tare da Abdullah Adegbenro mai shekaru 17 da kuma na karshan su Oyeyemi Bakare mai shekaru 20. Rundunar ta ce ta samu rahotan kiran wayane a dai-dai lokacin da mutanan da ake zargi suke kokarin guduwa da wata gawar wani yaro zuwa Ota. Hakanan hukumar ta ce, wadanda ake zargin an kama su da Makamai kamar adda da sauran su.
Da Duminsa:An sake yin garkuwa da ‘yansandan Najeriya 5

Da Duminsa:An sake yin garkuwa da ‘yansandan Najeriya 5

Tsaro
Rahotanni daga jihar Ogun na cewa wasu kauyawa sun yi garkuwa da 'yansandan Najeriya 5.   Hakan na zuwane daga kauyen Aba Tuntu dake Ijebu-Igbo. Shugaban kauyen me ya kaiwa 'Yansandan Najeriya korafin cewa akwai wasu mutane a kauyen dake rike da makamai suna farwa mutane lokaci zuwa Lokaci.   'Yansandan su 15 da hadin gwiwar Bilgilante 35 sun je kauyen inda kuma suka yi nasarar kama Bindigu da sauran makamai. Saidai a yayin da suke shirin barin kauyen,  Wasu kauyawa sun far musu inda suka harbesu da kuma kai musu hari da sauran makamai. An harbi DPO dake cikinsu da kuma karin wasu mutane.   Majiyar Daily Post tace 'yansanda 5 ne aka yi garkuwa dasu da Bigilante 3 da kuma tafiya da Bindigun AK47 2, da wata Bindiga da hayaki me sa Hawaye da kudi.   ...
Gwamnatin jihar Ogun bata aikawa shugaba Buhari Miliyan 250 ba>>Fadar Shugaban kasa

Gwamnatin jihar Ogun bata aikawa shugaba Buhari Miliyan 250 ba>>Fadar Shugaban kasa

Siyasa
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ba kamar yanda labarai ke yawo a shafukan sada zumunta ba, Gwamnatin jihar Ogun bata aikawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari Miliyan 250 ba.   Da yake karyata labarin, Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa labaran karyane wata kafar yanar gizo ta watsa.   Yace akwai rukunin gidaje a jihar ta Ogun da aka sakawa sunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda kuma ya je ya kaddamar dasu. Yace wannan ba yana nufin rukunin gidajen na shugaban kasar bane.   Yace kudin da aka gani suka nuna an turawa Rukunin gidajen me sunan Buhari su. Ba wai shugaba Buhari aka turawa ba, wani aikin kwangilane da aka yi aka gama shine aka biya. Fake news industry at work. A certain document showing the transfer of N12,500,...
Hadirin Mota ya lakume rayukan mutane 109 A jihar Ogun daga watan Janairu zuwa Ogusta

Hadirin Mota ya lakume rayukan mutane 109 A jihar Ogun daga watan Janairu zuwa Ogusta

Uncategorized
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, hukumar kiyaye haddura reshan jihar Ogun (TRACE), ta sanar da cewa, a kalla mutum 109 ne suka rasa rayukansu a hadurra da suka faru a fadin jihar Ogun tsakanin watan Janairu zuwa watan Agusta. Kwamandan rundunar Mista Seeni Ogunyemi ne ya bayyana hakan a wajen taron kwamandojin rundunar TRACE Corps na shekara-shekara karo na 5, wanda aka gudanar a Valley View, dake Abeokuta. Ya zargi cewa, gudun wuce sa"a da tuki cikin rashin bin doka sune ummul-aba'isin da su ke haifar da yawan hadarurruka akan hanyoyi wanda suke janyo mace-mace a jihar. A cewarsa, a kalla mutane 450 ne suka samu raunuka a hadurru mota daban-daban da su ka afku a tsakanin lokutan. Hakanan kwamandan rundunar ya yabawa gwamnatin jihar bisa gudunmawar da take bawa hukumar na k...
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta gargadi masu ababen hawa da su guji tuki cikin maye

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta gargadi masu ababen hawa da su guji tuki cikin maye

Tsaro, Uncategorized
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshan jihar Ogun, ta gargadi masu ababen hawa da su guji tuki cikin maye da sauran abubuwa masu sa maye don rage ya waitar hatsarurruka  a kan  hanya a wadannan watannin da su ka rage. Mista Ahmed Umar, kwamandan sashin, hukumar FRSC, na jihar Ogun, shine ya yi wannan gargadin yayin kaddamar da zagayan wayar da kan mutane game da kare lafiyar su, ta hanyar kaucewa yin tuki cikin maye a raguwar watanin da su ka rage. Taken shirin shine "A kiyaye Lafiya" wanda hukumar ta gudanar dashi a sassa daban daban na jihar.
Dan Allah ku dawo bakin aiki>>AIG Ahmad Ilyasu dake kula da Legas da Ogun ya roki ‘yansanda

Dan Allah ku dawo bakin aiki>>AIG Ahmad Ilyasu dake kula da Legas da Ogun ya roki ‘yansanda

Tsaro
AIG Ahmad Ilyasu dake kula da yankun Zone 2 ya roki jami'an 'yansanda su kkma aiki musamman a Legas da Ogun.   Ya bayyana cewa hakan na da muhimmanci wajan tabbatar da tsaro musamman saboda shagulgulan karshen shekara da za'a yi.   Yayi wannan kirane yayin wani taro a Onikan dake Legas.   Ya kuma yi kira da su manta da abinda aka musu a zanga-zangar SARS saboda kishin kasa, sannan su koma aiki su canja irin tunanin da mutane kewa aikin dansanda. Dailytrust ta ruwaito cewa.   “We must have a change of attitude to our duty and put the people as the centre point of our policing,” he said.
Rundunar ‘Yan sandan jihar Ogun sun cafke wani saurayi da ya kashe Budurwarsa a Otel

Rundunar ‘Yan sandan jihar Ogun sun cafke wani saurayi da ya kashe Budurwarsa a Otel

Tsaro
An zargi wani matashi mai matsakaicin shekaru da laifin kashe budurwarsa a dakin otal da ke Ibafo. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi shine ya tabbatar da hakan, inda ya ce rundunar ta kame matashin mai suna Rexlawson Johnson, mai shekaru 31 bisa laifin kashe budurwarsa mai suna Patricia john. Oyeyemi ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Juma’a bayan wani rahoto da manajan Otal din “MOLAYO HOTEL,” ya shaida ga hukumar. Ma'aikatan Otal din sun bayyana cewa, sun gano gawar Patrica a dakinta dauke da raunuka a wuyanta, inda su ke zargin maiyuwa an shaketa ne. Bayan cafke wanda a ke zargin, A yayin da rundunar ke tuhumar sa,  tuni ya amsa laifinsa. A karshe Rundunar ta sha'alwashin fadada bincike inda ta bada tabbacin gurfanar da mai laifin nan bada jimawa ...
Yan daba sun fasa rumbun ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Ondo, inda suka yi awon gaba da kayan, sannan suka cinna ma Rumbun wuta

Yan daba sun fasa rumbun ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Ondo, inda suka yi awon gaba da kayan, sannan suka cinna ma Rumbun wuta

Siyasa
Yan daba sun fasa cikin rumbunan ajiyar gwamnati a Akure, babban birnin jihar Ondo, kuma sun wawushe kayayyakin tallafi na COVID-19 da aka ajiye a can. A cewar rahotanni daga baya suka kone gidan ajiyar. Gidan ajiyar yana cikin harabar babban kotun majistare a cikin garin Akure. Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Gwamnatin Tarayya ce ta baiwa jihar tallafin. Gwamna Rotimi Akeredolu yayi bikin kaddamar da kayan tallafi na CA-COVID 19 a Akure, babban birnin jihar a ranar 10 ga watan Agustan wannan shekarar. Bayan samun bayanan sirri, an gano cewa 'yan daban sun afka cikin dakin ajiyar kayan ne suka fasa kofofin, suka yi awon gaba da kayan. Sai da sojoji suka shiga tsakani don kawo karshen lamarin a Akure, babban birnin jihar Ondo. Wani faifan bidiyo da ya nuna ...