fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Ohanaeze Indigbo

Idan aka bamu shugaban kasa a 2023 zamu yafe kisan da aka mana a yakin basasa>>Kungiyar kare muradun Inyamurai

Idan aka bamu shugaban kasa a 2023 zamu yafe kisan da aka mana a yakin basasa>>Kungiyar kare muradun Inyamurai

Siyasa
Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa idan duka jam'iyyun siyasar Najeriya suka tsayar da dan takarar shugaban kasa dan kabilarsu a shekarar 2023 kuma ya gaji shugaban kasa, Muhammadu Buhari to zasu yafe laifin da aka musu lokacin yakin Basasa.   Kungiyar ta bayyana hakane a lokacin da wasu wakilanta na kasashen waje suka ziyarce ta a Abia. Ta kuma ce ba zata lamunci wasu dake kokarin ganin an raba kungiyar kashi 2 ba.
Muna cikin wanda suka Kafa Najeriya dan haka ba zamu balle mubarwa bare ita ba>>Inyamurai

Muna cikin wanda suka Kafa Najeriya dan haka ba zamu balle mubarwa bare ita ba>>Inyamurai

Siyasa
Kungiyar dake kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze ta bayyana cewa babu inda zata, Inyamurai sunanan cikin Najeriya ba zasu balle su kafa kasarsu ba.   Kungiyar ta yi kira ga masu fafutukar ganin an kafa kasar Biafra da su hakura, maimakon haka su koma neman yiwa Inyamurai Adalci da kuma samun wakilci a sauran gurare. Kungiyar ta bayyana hakane ta bakin, mataimakin sakataren watsa labaranta, Mazi Chuks Igbegbu inda yace Iyaye da kakanninsu na cikin wanda suka samarwa Najeriya 'yancin kai dan haka ba zasu barwa bare kasar ba saidai su a bar musu.
Ka Hakura da takara ka goyi bayan mu, indai gaskiya za’a bi, Inyamurine zai gaji Buhari>>Kungiyar kare muradun Inyamurai ga Atiku

Ka Hakura da takara ka goyi bayan mu, indai gaskiya za’a bi, Inyamurine zai gaji Buhari>>Kungiyar kare muradun Inyamurai ga Atiku

Siyasa
Kungiyar kare muradun inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta jawo hankalin tsohon mataimakin shugaban masa wanda kuma shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar da ya hakura da takara a 2023.   Kungiyar ta hannun sakataren watsa labaranta, Chucks Ibegbu ta bayyana cewa kamata yayi Atikun kamar yanda Inyamurai suka goya masa baya a 2019 shima a 2023 ya goyi bayansu. Yace duk da yake dai yana da 'yanci a matsayinshi na dan kasa ya tsaya takara amma ana duba abinda ya kamata ne.   Kungiyar tace Arewa da yankin Yarbawa dana Naija Delta duk sun mulki kasarnan dan haka 2023 sai a barwa Inyamurai.