
Kabilar Okun na son Ballewa daga Arewa
Kabilar da ke magana da yaren Yarbanci ta bayyana ceea tana son ballewa daga Arewa ta koma bangaren Kudu Maso Yamma.
Kabilar tace tana son a mayar da ita cikin jihohin Ekiti, Ondo, da Kwara wanda tace rabata da wadannan jihohi ya jawo mata koma baya da rashin ci gaba.
Kabilar ta yi maganane karkashin kungiyarta ta OLA ta bakin shugabanta, Emmanuel Otitoju inda yace tuni har sun aikawa majalisa da wannan bukatar.
Yace gyaran kundin tsarin mulki da za'a yi yazo daidai gaba inda suka aika da bukatarsu majalisa a musu zaben raba gardama saboda suna son ballewa daga jihar ta Kogi.