fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Olu falae

Mutum mai Gaskiya ba zai iya zama shugaban kasa a Najeriya ba>>Olu Falae

Mutum mai Gaskiya ba zai iya zama shugaban kasa a Najeriya ba>>Olu Falae

Siyasa
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 1999, Olu Falae ya bayyana cewa idan dai kai mutum ne me gaskiya to da wuya ka iya samun shugabancin Najeriya.   Olu Falae ya bayyana hakane a hirar da yayi da Independent inda yace idan kana da gaskiya ba zaka so bin hanyoyin da basu dace ba dan cin zabe. Yace to shi kuma wanda bashi da gaskiya zai iya bin kowace hanya dan ya kada ka, kaga kuwa da wuya ka iya dashi.   Yace koda a lokacin da ya fito takarar shugaban kasa wani ya sameshi yace indai a Najeriya ne da wuya ya iya cin zabe. Ya ce bai taba daukar 'yan bangar siyasa ba tunda yake.
Koda Buhari ya sauka daga Mulki ba lallaine matsalolin Najeriya su warware ba>>Olu Falae

Koda Buhari ya sauka daga Mulki ba lallaine matsalolin Najeriya su warware ba>>Olu Falae

Siyasa
Tsohon minista kuma dan takarar shugaban kasa a shekarar 1999, Olu Falae ya bayyana cewa koda shugaba Buhari ya sauka daga Mulki ba lallau matsalolin Najeriya su kwaranye ba.   Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai na Independent inda yake mayar da martani kan cewar da PDP ta yi wai shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sauka daga Mulki. Hutudole ya tattaro muku cewa, Falae yace ba zai yi inkarin kiran na PDP amma maganar itace idan Buhari ya sauka, waye zai maye gurbinsa? Yace babbar matsalar itace koma wanene ya hau mulkin kasarnan dole ya bi kundin tsarin mulkin Najeriya. Hutudole ya fahimci Falae yace kuma caccaki gwamnatin shugaba Buhari inda yace yawanci mutanen Katsina ya baiwa mukami.    
Yarbawa ne gam din dake rike da Najeriya>>Olu Falae

Yarbawa ne gam din dake rike da Najeriya>>Olu Falae

Uncategorized
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma ministan kudi, Olu Falae ya bayyana cewa yarbawa ne gam din dake rike da Najeriya.   Yace sun saka jari sosai wajan ganin kasar ta zama kasa daya al'umma daya dan haka babu maganar wai ace su shiga a yi rikin Raba kasa dasu.   Yacs suk wani rikici ko rashin jituwa idan ya zo kasar Yarbawa to ya mutu inda ya kara da cewa sune ke maraba da kowa da duk wanda yazo suka karbarshi.   Ya bayyana hakane a wata hira da yayi da Vanguard inda yace yawanci idan aka yi rikici a wani bangaren Najeriya, kasar Yarbawa ake zuwa neman mafaka. Yace sun zama kamar wani sansanin 'yan gudun hijirar Najeriya.   Ya kuma kara da cewa, zaman lafiyarsu ne ya kawo hakan inda yace rundunar tsaro ta Amotekun ba shirin ballewane daga Naj...