fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Olusegun Obasanjo

“Kar ku zabi Atiku, Saraki, Peter Obi da kuma Tambuwal”>>Obasanjo ya fadawa yan Najeriya

“Kar ku zabi Atiku, Saraki, Peter Obi da kuma Tambuwal”>>Obasanjo ya fadawa yan Najeriya

Breaking News, Siyasa
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci yan kasar cewa kar wanda ya zabi duk wani shugaban daya fada cewa matasa ne suka saya masa fom. Yan siyasar da suka bayyana cewa matasa ne suka siya masu fom sun hada a Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Peter Obi da kuma Aminu Tambuwa duk a karkashin tutar PDP. Inda yace duk makaryata ne saboda babu ta yadda matasa zasu hada masa naira miliyan 40 su siya masa fom din takara. Ya bayyana hakan ne a jihar Legas inda ya halacci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar wani fasto.  
Na gudu daga marantar Islamiyya saboda tsoron bulala>> Obasanjo

Na gudu daga marantar Islamiyya saboda tsoron bulala>> Obasanjo

Uncategorized
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda ya kauracewa makarantar Islamiyya saboda bulala. Obasanjo, mai digiri a karatun kirista ya bayyana hakan ne yayin da ake gudanar da bikin nadin Sheikh Salis Adenekan a matsayin shuganan yan Tijjaniya na yarabawa, jihar Edo da Delta. Inda ya kara da cewa dole ne mutun yayi kokari kuma yayi aiki tukuru ya martaba addininsa sosai idan har yana so ya shiga Al-jannah a ranar kiyama.  
Obasanjo ya fadi abinda zai faru muddin aka raba Najeriya

Obasanjo ya fadi abinda zai faru muddin aka raba Najeriya

Siyasa
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa bai kamata a raba Najeriya ba, zamanta a matsayin kasa dsya yafi Amfani.   Yace yawanci manyan Kabilun Najeriya basuwa kananan Adalci. Yace idan Hausawa da Yarbawa da Inyamurai suna iya kafa kasashen su idan Najeriya ta rabe sauran kabilun ya zasu yi kenan?   Yace sauran kabilun za'a rika zalintarsu ne kawai ana muzguna musu idan aka raba Najeriya. Ya bayyana hakane a dakin karatunsa dake Ogun yayin ziyarar wata kabilar TIV ta kaimasa. “If the Yoruba can stand as a country, if the Igbos and the Hausa/Fulani can stand as separate countries, where do we want the minority groups to be? “Now, by virtue of the present situation, they are a little bit protected, but if Nigeria breaks up, they will be oppresse...
Gumi Ya Jagoranci Shugabannin Addini Zuwa Gidan Obasanjo Kan Matsalar Tsaro

Gumi Ya Jagoranci Shugabannin Addini Zuwa Gidan Obasanjo Kan Matsalar Tsaro

Siyasa
Shahararren malamin addinin Islama, Sheik Ahmad Gumi, yanzu haka yana cikin ganawa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a garin Abeokuta na jihar Ogun. Gumi, ya isa gidan tsohon shugaban wanda ke da dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta, da misalin karfe 11 na safe, kuma kai tsaye ya shiga taron. Mai taimaka wa Obasanjo kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi, wanda ya tabbatar da haka ga Aminiya, ya ce wasu shugabannin addinai ma na halartar taron. “Ee, gaskiya ne. Shi (Gumi) yanzu haka yana ganawa da Baba tare da sauran shugabannin addinai, ”in ji Akinyemi. A kwanakin baya malamin ya hadu da kungiyoyin 'yan fashi a jihohin Zamfara da Neja don sasanta wadanda aka sace. Gumi ya roki gwamnati da ta yi wa ‘yan fashin afuwa, Wanda hakan ...
Obasanjo ya goyi bayan gwamna Yahya Bello ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023

Obasanjo ya goyi bayan gwamna Yahya Bello ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023

Siyasa
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan wanda zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023, Dan gidan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo watau, Olujonwo Obasanjo ya bayhana goyon bayansa ga gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello. Olujonwo ya bayyana Gwamna Yahya Bello a matsayin wanda zai zamarwa matasa jagora wajan samun shugabancin Najeriya. Ya bayyana cewa an bar matasa acan baya duk da yake cewa sune ke da yawa kuma ake amfani dasu wajan kaiwa ga matakan Mulki.   A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda Kamfanin mai na kasa, NNPC yace a shirya sayen Man fetur din da tsada “You must remain resolute, stoic and not give in to intimidation, name-calling or sort. Your audacity is a big reawakening to Nigerian youths and this has given us more hope and confidence t...
Zamu ci gaba da neman shawara a wajan Obasanjo>>Shugaba Buhari

Zamu ci gaba da neman shawara a wajan Obasanjo>>Shugaba Buhari

Uncategorized
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Najeriya zata ci gaba da neman shawara a wajan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a matsayin uban kasa.   Kakakin Shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa Shugaban ya bayyana hakane a sakon taya murnar cika shekaru 84 da shugaba Buharin ya aikewa Obasanjo.   Yace Obasanjo ya bautawa Najeriya tukuru sannan kuma yana tayashi murna da fatan Allah ya kareshi da Lafiya. “President Muhammadu Buhari felicitates with former President Olusegun Obasanjo on the occasion of his 84th birthday.   “On behalf of the government of Nigeria, President Buhari wishes the former President, who has served the country with loyalty and huge dedication, continued good health and happiness.   “President B...
Coronavirus/COVID-19 ta kama ni>>Obasanjo

Coronavirus/COVID-19 ta kama ni>>Obasanjo

Kiwon Lafiya
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa cutar Coronavirus/COVID-19 ta kamashi a kwanakin baya.   Yace amma bayan awanni 72 da aka sake masa gwaji sai aka ce ya warke.   Obasanjo ya bayyana hakane a wajan bikin zagayowar ranar haihuwarsa inda ya cika shekaru 84 da haihuwa.   Obasanjo yace amma cutar bata nuna wata Alama ba a jikinsa, kuma bayan nan an masa gwaji har sau 3 kuma duk sun nuna cewa bashi da cutar. “I called them to come and test me, they came on a Saturday, I didn’t get the result until Wednesday and it came out positive but I didn’t see any symptoms. “They came three days after they tested me and said I am negative – that is three days after I tested positive.
Yawancin ‘yan Najeriya suna aikata abinda suka ga dama kamar ba za’a yi tashin kiyama ba>>Obasanjo

Yawancin ‘yan Najeriya suna aikata abinda suka ga dama kamar ba za’a yi tashin kiyama ba>>Obasanjo

Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwa da cewa yawancin 'yan Najeriya na aika abinda suka ga dama kamar rayuwa a Duniya za'a yita a gama ta, Babu zuwa Lahira.   Obasanjo ya bayyana hakane a wajan taron tunawa da wani Moses Orimolade inda yace Kiristoci da dama suna aikata abinda suka ga dama ba tare da tunanin akwai ranar Hisabi ba.   Yace amma fa dolene a shirya, tana nan zuwa. “The situation we have in the country today does not show we are preparing for the Kingdom of God. “But we have to be prepared. There is always a day of reckoning.
Babu wani Jibrin dan Sudan, Buharin da aka sanine saidai ya canja>>Obasanjo

Babu wani Jibrin dan Sudan, Buharin da aka sanine saidai ya canja>>Obasanjo

Siyasa, Uncategorized
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya nesanta kansa da masu cewa wai ba shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ke mulki ba, wani ne Jibrin daga Sudan.   Obasanjo yace wannan ikirari shirmene. Yace kawai dai abinda ya sani shine Buhari da yayi aiki dashi a baya ba haka yake ba, watakila dai dama can bai mai sanin gaske bane ko kuma ya canja.   Ya baiwa matasa shawarar cewa su tashi tsaye saboda gyara Najeriya.  Yace ba sai sun bi hanyar tayar da hankali ba, cikin lumana zasu kori tsaffin shuwagabannin su kafa irin mulkin da suke so. “You (youths) have everything going for you and I don’t want you to feel discouraged. Things are bad in Nigeria but I believe it is only for a short while because it depends on you. “Whatever my generation might have done wrong –...