fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Tag: Olusegun Obasanjo

Ban saka Son rai a gwamnati na ba>>tsohon Shugaban kasa Obasanjo

Ban saka Son rai a gwamnati na ba>>tsohon Shugaban kasa Obasanjo

Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo, Murabus, ya bayyana cewa a lokacin mulkinsa na farar Hula bai saka son rai ba.   Obasanjo ya bayyana hakane a wata hira da yayi da jaridar The point inda yace ba wai ba su yi kuskure ba a lokacin mulkinshi, yace sun yi kuskure amma bana ganganci ba. Yace wasu shuwagabannin yarbawa sun sameshi inda suka ce mai be yiwa yankin Yarbawa komai ba a lokacin mulkinshi, amma sai ya tambayesu shin yawa Najeriya komai? Suka ce mai eh, dan haka yace to shikenan tunda dai Yarbawa a Najeriya suke to suma ya musu kenan.   Obasanjo ya kara da cewa idan aka ci gaba da jajircewa akan aikata abubuwan da suka kamata, Najeriya zata kai matsayin da ake son ta kai.
Kada ku tsaya neman aikin gwamnati, ku nemi sana’a>>Obasanjo ya baiwa matasan Najeriya shawara

Kada ku tsaya neman aikin gwamnati, ku nemi sana’a>>Obasanjo ya baiwa matasan Najeriya shawara

Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya baiwa matasan Najeriya shawarar cewa kada su tsaya cewa sai sun nemi aikin Gwamnati ko kuma aikin Ofis da baida tabbas, su je su koyi sana'a tafi tabbas.   Obasanjo ya bayyana hakane a lokacin da yake jawabi wajan kaddamar da wani gini da kungiyar matasan Yarbawa ta yi. Yace koda kana da aiki, yana da kyau ace mutum yana da wata sana'ar hannu da yake domin babu abinda ke da tabbas.   Obasanjo yace musamman yanzu da ake cikin Coronavirus/COVID-19 ya kamata matasa su shiga ayyukan da zasu farfado da tattalin arzikin kasar.   Yace kada rashin aikin yi ya hana mayasa shiga harkokin kasarnan a dama dasu. Yace suma suna da rawar da zasu taka.
Yara Miliyan 14 da basa zuwa makaranta ka iya zama ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane nan gaba>>Obasanjo

Yara Miliyan 14 da basa zuwa makaranta ka iya zama ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane nan gaba>>Obasanjo

Siyasa
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa idan ba'a dauki matakin daya kamata ba, yara Miliyan 14 da basa zuwa makaranta nan gaba zasu zama barazana ga Al'umma.   Obasanjo yayi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar Ilimi dasu yi kokarin ganin an shawo kan wannan matsala. Yace hakanan ya kamata a inganta Harkar Ilimi a kasarnan inda yace ba wai yawan makarantu ba amma a samar da ilimi mai inganci da zai taimaka matuka wajan kawar da matsalar samun dalibai da basu san abinda ya kamata ba.
Ko fulani, dangin Buhari sun san abubuwa basa tafiya daidai a kasarnan>>Obasanjo

Ko fulani, dangin Buhari sun san abubuwa basa tafiya daidai a kasarnan>>Obasanjo

Uncategorized
Tsohon shugaban kasa,Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa al'amuran tsaro sun tabarbare a kasarnan a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.   Yace dolene sai an kawo canji in ba haka ba kasar ka iya fadawa cikin yanayin da ba'a so. Obasanjo yavce matsalar tsaron kasarnan a bayyane take ta yanda koda dangin shugaban kasar, Fulani masu hankali sun san cewa akwai matsala a kasarnan.
Muddin ‘yan Arewa suka dage akan cewa dan kudu ba zai kara mulki ba to za’a ga tashin hankali mara misaltuwa a kasarnan>>Obasanjo

Muddin ‘yan Arewa suka dage akan cewa dan kudu ba zai kara mulki ba to za’a ga tashin hankali mara misaltuwa a kasarnan>>Obasanjo

Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya gargadi mutanen Arewacin Najeriya da cewa yana jin wata magana dake yawo tsakaninsu wadda suke cewa wai ba zasu maimaita kuskuren da suka yi akan Jonathan ba.   Yace wannan magana na nufin cewa wai dan Kudu ba zai kara mulkar Najeriya ba, yace wannan maganar bata kamata ba kuma zata karaqa masu tunain cewa hade Najeriya a matsayin kasa daya da aka yi a shekarar 1914 kuskurene karfin gwiwa. Yace muddin Arewar ta dage akan wannan aniya to tabbas zata kai ga kasarnan ta fada cikin tashin hankali mara misaltuwa. Yace kuma irin wannan abunne fa ya raba kasar Sudan gida 2.   Obasanjo yace raba Najeriya bashine mafita ba, a tashi tsaye a hada hannua yaki matsalar tsaro tare dan amfanin kanmu.
Obasanjo ya gargardi gwamnatan Africa akan rashin abinci bayan cutar corona:Yace a yi tanadi

Obasanjo ya gargardi gwamnatan Africa akan rashin abinci bayan cutar corona:Yace a yi tanadi

Siyasa
Tsohon shugaban kasan,  Chief Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnatan African da su fara Samar da abinci mai yawa don kare rashin abinci da zai iya faruwa bayan cutar corona. Shugaban ya bayarda da shawaran ne a dakin aje littattafai dake abeokuta lokacin da yake kaddamar da wani gurin kiwan kifi,  kamar yadda mai taimaka mashi ta ban garan labarai ya bayyana, Keyinde Akinyemi, a ranar litinin. Obasanjo yace wannan ya zama dole dan kuwa idan aka yi sake za'a iya shiga Matsala. A baya dai Hutudole ya kawo muku yanda wata kungiya ta yi gargadin cewa za'a iya samun matsalar Abinci a Najeriya.
Yanzu-Yanzu:Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya kori ma’aikatan sa daga aiki, yaki biyan Albashi

Yanzu-Yanzu:Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya kori ma’aikatan sa daga aiki, yaki biyan Albashi

Siyasa
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya kori ma'aikatansa da dama dake kula da dakin karatunsa dake Ogun.   Obasanjo a takardar da Hutudole ya hango a Sahara Reporters ta korar aikin ya bayyana matsalar tattalin arzikin Coronavirus/COVID-19 a matsayin dalilin koarar aikin. Saidai ya bayyana cewa bawai kora bace, dakatarwace da babu ranar dawowa aiki. Daya daga cikin wanda aka koran ya shaidawa Sahara Reporters cewa dama suna bin bashin albashin watanni da dama, hutudole ya fahimci cewa asha ruwan tsuntsaye ake musu na biyan albashin inda za'a biya na wata daya a tsallake watanni sannan a sake biya.   Ya kara da cewa, koda a wannan shekarar Albashin watan Janairu kadai aka iya biyansu sai rabin na watan Afrilu.
Shekaru 5 na mulkin Buhari sun fi na Obasanjo da Jonathan amfanar ‘yan Najeriya>>cewar ‘yan Najeriya

Shekaru 5 na mulkin Buhari sun fi na Obasanjo da Jonathan amfanar ‘yan Najeriya>>cewar ‘yan Najeriya

Siyasa
Wata tambaya da Tsohon Sakataren hukumar zabe me zaman Kanta,INEC, Hakeem Baba Ahmad yayi a shafinshi na sada zumunta ta bayyana cewa Shekaru 5 na mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari sun fi na sauran shuwagabannin da Najeriya ta yi a baya.   Hakeem dai ya saka tambayar cewa wanene daga cikin shugabannin Najeriya,Muhammadu Buhari, Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo shekarunshi 5 na farko suka fi amfanar 'yan Najeriya? https://twitter.com/baba_hakeem/status/1250577199062822913?s=19 Sakamakon wannan tambaya da Hakeem yayi ta bayyanar da cewa Mulkin Shugaban kasa,Muhammadu Buharine ya fi amfanar Mutane,kamar yanda ake iya gani a Sama.
Wasikar Obasanjo ga Sarki Muhammadu Sunusi II bayan da aka Tsigeshi

Wasikar Obasanjo ga Sarki Muhammadu Sunusi II bayan da aka Tsigeshi

Siyasa
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya baiyana batun sauke tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a matsayin 'alheri' da mara kyau '.   A cikin wata wasika, inda ya yi magana da Sanusi da cewa “Maigirma kuma dan'uwana,” ya kuma ce masa “ya ji labarin bakin ciki da albishir da kwamitin Majalisar zartarwa na gwamnatin jihar Kano ta yi”.   Obasanjo ya ce cire Sanusi abin bakin ciki ne domin bai cancanta ba, amma yana da kyau saboda tsohon Sarkin ya “biya farashin”. sai dai bayyi bayani dalla-dalla ba.   Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cire Sanusi a safiyar Litinin daga kan karagar mulki, lamarin da ya kawo karshen wata kyakkyawar alakar da ke tsakanin tsohon Sarkin da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.   A karshe tsohon shu...
Nnamdi Kanu: Ya yiwa Gowon, Olusegun Obasanjo martani kan kalaman da suka yi ga Inyamurai

Nnamdi Kanu: Ya yiwa Gowon, Olusegun Obasanjo martani kan kalaman da suka yi ga Inyamurai

Siyasa
Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra(IPOB) ya yiwa tsohon Shugaban Kasa, Janar Yakubu Gowon, tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kuma tsohon hafsan soji, Janar Theophilus Danjuma, ihu bisa ga kiran da suke yi na sake fasalin kasar.   Janar Yakubu Gowon (retd), wanda ya halarci wani taro wanda Gidauniyar Shugabanci ta Igbo ta shirya a ranar Alhamis, ya yarda cewa an bar ƙabilar Igbo a baya a siyasar Nijeriya.   Ya ce, "Na yi imani da cewa an yi wa Igbo rashin dai dai, batun tsarin mulki ya kama a magance shi tare da samun daidai to, da kuma dawo da kwarin gwiwa ga kowa.   Haka Shima Obasanjo ya yi Allah wadai da halin da ake ciki a kasar nan a cikin jawabin da ya yi a ranar Asabar a bikin gabatarwa na tunawa da Frederick Fase...