fbpx
Friday, February 26
Shadow

Tag: Ondo

Dole ce tasa Sunday Igboho ya fara korar Fulani>>Gwamnan Ondo ya kare me korar Fulani

Dole ce tasa Sunday Igboho ya fara korar Fulani>>Gwamnan Ondo ya kare me korar Fulani

Tsaro
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa dolece ta kawo Sunday Igboho me korar Fulani.   Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channelstv inda yace kuma lamarin sa ya sa Sunday Igboho din ya tashi tsaye ya kamata a magancesu.   Saidai Gwamnan yace baya goyon bayan aikata. Laifuka da kuma daukar doka a hannu.   “There are things that we do at times that you have to know what led to them. Those circumstances might not be justifiable, might not be legal, but again when you look at it, you’ll know we are a child of circumstance.   “I for one, I’ve always said that I will not support anyone taking laws into his own hands. That’s why I had to go to Ibadan.   “That’s why I will go to every other place in the South-West to pr...
Rundunar Soji tayi Nasarar kashe masu garkuwa da mutane a jihar Ondo

Rundunar Soji tayi Nasarar kashe masu garkuwa da mutane a jihar Ondo

Tsaro
Sojoji sunyi nasarar kashe a kalla mutane 4 da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne. Rahotanni sun rawaito cewa masu garkuwan sun toshe hanya, A yayin da suke kokarin yin awon gaba da wasu matafiya kafin sojoji su far musu wadanda aka ce suna sintiri a kan babbar hanyar. An gano cewa tuni masu garkuwar su ka yi awon gaba da wasu mutane kafin isowar sojoji wurin. Sai dai Wata majiya ta ce sojojin sun yi artabu da masu satar mutanen a musayar bindigar da ta dauki kusan awa daya, inda a karshe masu garkuwan suka arce cikin daji tare da barin wadanda sukai garkuwar dasu. Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda Mista Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce tuni rundunar 'yan sanda suka shiga daji don neman' yan fashin. Amma hukumomin Soji a jihar sun ce ba wa...
Saboda kallon da akewa matan Arewa cewa basu da hazaka yasa na dage>>Daliba daga Arewa data kammala jami’ar Ondo da maki mafi kyau

Saboda kallon da akewa matan Arewa cewa basu da hazaka yasa na dage>>Daliba daga Arewa data kammala jami’ar Ondo da maki mafi kyau

Uncategorized
A'isha Dauda ta kammala jami'ar Elizade Dake Ilara Mokin jihar Ondo da maki mafi kyawu a tsangayar koyon ilimin tattalin arziki.   Yar shekaru 22 data fito daga jihar Kaduna ta bayyana cewa, a ra'ayinta bata so ci gaba da karatun boko ba amma iyayenta suka matsa mata, tace dalili kuwa ta yi makarantu da yawa kamun ta kammala sakandare saboda Mahaifinta me yawan tafiye-tafiye ne. Tace burinta shine ta yi kasuwanci.   Da take bayyana irin rayuwar da ta yi a tsakanin wanda ba addini da al'adarsu daya ba tace ta dan samu matsala dan manyan kawayenta 2 ba 'yan Arewa bane. Tace saidai hakan ya karfafata, ta zama tana da son yin Karatu dan canja irin kallon da akewa matan Arewa cewa basu da hazaka. It has to be the religious and cultural differences. I am a Hausa Musl...
An sace matar shugaban ma’aikatan jihar Ondo

An sace matar shugaban ma’aikatan jihar Ondo

Tsaro
Rahotanni daga jihar Ondo na cewa an sace matar shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu watau, Olugbenga Ale.   Satar matar na zuwane jim kadan bayan da aka kashe wani basarake a jihar. An sace tane tare da direbanta da kuma wani da suke tare a daren jiya, Alhamis. Zuwa yanzu dai wanda suka sace ta din basu tuntubi yanda za'a yi su sakota ba.
An bukaci Mawadata da su kasance masu tallafawa Mabukata – A cewar Shugaban gidauniyar Zakka (ZSF)

An bukaci Mawadata da su kasance masu tallafawa Mabukata – A cewar Shugaban gidauniyar Zakka (ZSF)

Uncategorized
An yi kira ga MUSULMAI, musamman mawadata daga cikinsu, da su raba abin da suka mallaka ga matalauta da maƙwabta waɗanda basu da hali, domin samun rahama a wajan Allah kasancewar Sadaka wani Nau'ine na ibada kuma aiki ne na masu tsoran Allah. Wannan nasihar ta fito ne daga wani malamin addinin musulinci, Imam Abdulfatah Abdulsalam, a garin Akure, dake jihar Ondo, yayin rabon kayan tallafi, da kuma tsabar kudi ga marassa karfi a karkashin gidauniyar Zakka da Sadaqqah Foundation (ZSF). A cewar Imam Abdulfatah Daurewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma na samuwa ne muddin idan Mawadata su ka fidda dokiyoyin su wajan tallafawa mutanan da su ke da bukata. Hakanan Wani bawan Allah da ya amfana da tallafin kudi mai suna Taofiqah Suleiman, ya godewa Allah tare da nuna farin cikin...
Idan Najeriya na son ci gaba sai an saka dokar da zata hana haihuwa barkatai, A kasar China, Da daya aka yadda ma’aurata su haifa>>Gwamnan Ondo

Idan Najeriya na son ci gaba sai an saka dokar da zata hana haihuwa barkatai, A kasar China, Da daya aka yadda ma’aurata su haifa>>Gwamnan Ondo

Siyasa
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa dolene a saka dokar hana haihuwa barkatai indai ana son ci gaba da kuma raguwar matsalar aikin yi a kasarnan.   Gwamnan ya bayyana hakane a yayin wani taro na nemo mafita bayan zanga-zangar SARS da aka yi a Akure. Yace duk kasar da ta bar jama'arta sakaka babu kula da yanda ake haihuwa to bata shirya ci gaba ba.   Yace a kasar China Da daya aka amincewa ma'aurata su haifa dan haka dole Najeriya itama ta yi dokar da zata hana haihuwa barkatai. We must be able to control our population through population law. We are almost the size of China population. But in China today, there is a law that you can’t have more than one child. We must be deliberate about this population law.” he said.
Aiki ga me kareka: ‘Yansanda sun ceto mata 10 da aka sace dazu da safe a jihar Ondo

Aiki ga me kareka: ‘Yansanda sun ceto mata 10 da aka sace dazu da safe a jihar Ondo

Tsaro
Dazu da safene muka tashi da labarin cewa an sace wasu mata 'yan kasuwa a jihar Ondo su 16 a yayin da suke kan hanyar Akure zuwa Owo.   Tuni dai hukumar 'yansandan jihar ta sanar da cewa ta kubutar da 10 daga cikin matan wanda yanzu saura 6 suka rage a hannun 'yan Bindigar.   Kakakin 'yansandan jihar, ASP Tee Leo Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna kan kokarin ceto da sauran 6 da suka rage. Yace sai da aka yi bata kashi sosai kamin kubutar da 10. Sannan an kama 4 daga cikin masu garkuwa da mutanen.   Masu garkuwar dai sun nemi a basu kudin fansa Miliyan 11. 10 out of the 16 traders who were abducted on Saturday morning November 7, along the Akure-Owo highway by unknown gunmen, have been rescued by policemen attached to the Ondo police...
Yan bindiga sun sace mata 16 tare da wasu a jihar Ondo

Yan bindiga sun sace mata 16 tare da wasu a jihar Ondo

Tsaro
Akalla shugabanin kasuwa mata 16 da sauran fasinjoji ne ‘yan bindiga suka sace a babbar hanyar Akure zuwa Owo a cikin jihar Ondo. An ceto 10 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su yayin da hudu daga cikin masu garkuwar ‘yan sanda suka kama. Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Iyaloja na Isua Akoko dake karamar hukumar Akoko a jihar, Cif Mrs Helen Edward da sauran shugabannin mata suna daga cikin wadanda abin ya shafa. An rahoto cewa suna kan hanyarsu ta zuwa Akure, babban birnin jihar domin taron wata-wata na Iyalaje, iyalojas da shugabannin mata lokacin da aka sace su tsakanin Ogbese da Uso. Bayanai sun ce direban motar bas din wanda ya isar da wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda masu garkuwar suka sako ya ce masu garkuwar sun nemi shi ya koma gida ya sanar da dangin ...
Gwamnatin tarayya ta tallafawa wadanda gobara ta shafa a jihar Delta

Gwamnatin tarayya ta tallafawa wadanda gobara ta shafa a jihar Delta

Uncategorized
Gwamnatin Tarayya ta ba da gudummawar kayayyakin gini da kayayyakin abinci ga a kalla mutane 30 da gobara ta shafa a Kasuwar Igbudu da ke Warri, A karamar Hukumar Warri ta Kudu a Jihar Delta. Gobarar wacce ta afku a watan Agusta na shekarar 2020 ta lalata wasu kantuna da dama a Kasuwar. Kayayyakin wadanda hukumar bada a gajin gaggawa NEMA ta mika su ga wadanda gobarar ta shafa a ranar talata, Suun hada da kwanukan rufi, katako, da kososhi. Sauran kayayyakin sun hada da buhu 90 na shinkafa 10kg, buhuna 85 na garri 10k, buhu 85 na wake 10k, galan din mai 10 da sauransu. Shugaban da ke kula da ofishin hukumar NEMA A jihar Edo, Dahiru Yusuf shine ya mika kayan ga wadanda abin ya shafa.