
Cristiano Ronaldo ba zai taba zama matsala ba kuma shine gwarzon dan wasan duniya>>Pogba
Cristiano Ronaldo ya ciwa Manchester United kwallaye uku a wasan data lallasa Tottenham daci 3-2.
Bayan wasan, tauraron kasar Faransa dake taka leda a United, Paul Pogba ya yaba Cristiano Ronaldo da abokan aikinsa bisa kokarin da suka yi.
Inda ya bayyana cewa Ronaldo ba zai taba kawoma United matsala ba kuma yana farin cikin samun gwarzon dan wasan duniya a tawagar su.