
Da Dumi Dumi: PDP ta tantance mutane 17 dake neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyarta, ta dakatar da guda biyu
Jam'iyyar PDP ta tantance mutane 17 dake naman kujarar shugaban kasa a karkashin tutar ta ranar juma'a a babban birnin tarraya Abuja.
Ta fara tantance su da misalin karfe 11 na safe har izuwa karfe bakwai na yamma kuma gabadayansu sun hallacin taron.
Bayan sun kammala tantancewar shugaban kwamitin, David Mark ya bayyana cewa sun dakatar da mutane biyu domin basu cancanta ba.
Amma sai dai bai bayara da wasu bayanai akan mutane biyun da suka dakatar ba, inda yace sauran guda 15 sun tsallake.