Saturday, March 28
Shadow

Tag: Premier League

Kungiyoyin kwallon kafa na Premier League sun fara ragewa ‘yan wasansu Albashi

Kungiyoyin kwallon kafa na Premier League sun fara ragewa ‘yan wasansu Albashi

Wasanni
Hukumar professional Footballers Association ta kira wani taron gaggawa ga yan premier lig da EFL don su tattauna akan yadda coronavirus take tasiri a harkar wasannin kwallon kafa. kulob Birmingham city sune suka fara sanar da yan wasan su cewa zasu rage masu albashi a ranar talata. Hukumar PFA tace in har ana so a magance wannan matsalar to yakama ta kira taron gaggawa don su tattauna akan yadda zasu cigaba da tafiyar da al'amuran su. Kulob din Birmingham city suna samun sama da euros 6,000 a sati amma yanzu an umurce su da  suyi hakuri su karbi kashi 50 bisa dari nadaga albashin su har na tsawon watanni 4. Hukumar EFL ta sanar cewa zata ba kungiyoyin kwallon kafa taimakon euros miliyan 50 na gajeran lokaci.  Kungiyoyin kwallon kafa da dama a nahiyar turai s
Arsene Wenger na son a kammala Gasar Premier League duk da Coronavirus/COVID-19

Arsene Wenger na son a kammala Gasar Premier League duk da Coronavirus/COVID-19

Wasanni
Tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewa duk da matsalar Coronavirus/COVID-19 da ake fama da ita a Duniya akwai bukatar a kamala gasar Premier League.   Wenger ya bayyana hakane a hirar da yai da TalkSport inda yace yasan Premier League na son kammala wasanninta na kakar wasan bana.   Yace za'aikata matsar da jadawalin buga wasannin har zuwa watan Yuni.   Shia dai Wenger na can kebe a kasarshi ta Faransa.  
An dakatar da gasar Premier League saboda Coronavirus/COVID-19

An dakatar da gasar Premier League saboda Coronavirus/COVID-19

Wasanni
Hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila tace an dakatar da wasannin gasar Premier League na kasar dama duka sauran wasu wasannin da ake bugawa.   Dakatarwar ta hada da gasar wasannin mata dadai sauransu.   Hakanan hukumar ta bada shawarar daina duk wasu aikace-aikace na kungiyoyi da suka hada da haduwar  yan wasa a guri daya da ganawa da masoya da kuma masu ziyarar bude ido.
An dage wasan Premier League da za’a buga yau tsakanin Arsenal da Manchester City saboda barzanar Coronavirus-COVID-19

An dage wasan Premier League da za’a buga yau tsakanin Arsenal da Manchester City saboda barzanar Coronavirus-COVID-19

Wasanni
An daga wasan Premier League Wanda za a buga yau, laraba a filin wasan Etihad tsakanin Arsenal da Manchester City saboda barazanar cutar coronavirus-Covid-19.   Hukumar gasar Premier League tace an samu labarin cewa mai horas da kungiyar olympiakos, Evangelos Marinakis na dauke da kwayar cutar coronavirus-COVID-19.   Arsenal ta tabbatar da cewa akwai yan wasanta da dama da suka je wajen Marinakis bayan sun buga wasan su na zakarun nahiyar turai wato (Europa league ) kuma wa'yan nan yan wasan yanzu haka sun kebance  kansu.   Kungiyar ta kuma cewa hukumar lafiya tace a shawarce wasan da za'a buga yau tsakanin Arsenal da Man city ya kamata a daga shi saboda a samu isashan lokaci a shawo kan matsalar.   Saboda haka hukumar Premier League ta aminta ce
Kalli kayatattun kwallayen da Manchester United ta ci Manchester City a yau da sauran abubuwan kayatarwa da suka faru a wasan

Kalli kayatattun kwallayen da Manchester United ta ci Manchester City a yau da sauran abubuwan kayatarwa da suka faru a wasan

Wasanni
A yau ne aka buga babban wasan hamayya a gasar Premier league ta kasar Ingila wanda ya faru tsakanin manyan kungiyoyin gasar, Manchester United da Manchester City inda City ta sha kashi da ci 2-0. Martial ne ya fara ciwa United kwallo ana mintuna 30 da fara wasa, sai kuma Scott Mctominay da ya ci kwallo ta 2 bayan karin lokaci ana gab da za'a tashi, kuskuren golan Manchester City, Ederson ne ya jawo mata kwallon ta biyu inda maimakon ya baiwa dan garinsu kwallon sai ya baiwa Mactominay. https://twitter.com/benjani254/status/1236734581249892352?s=19 An sako dan kwallon Najeriya me bugawa kungiyar wasa,Odion Ighalo ana mintuna kadan a tashi. Wannanne babban wasansa na farko a kungiyar a gasar Premier kuma ga dukkan alamu ya ji dadin buga wasa ya kuma yi rawar gani. Tun bayan komawar...

Premier League: Man United ta casa Man City a wasan hamayya

Wasanni
Manchester United ta doke Manchester City da 2-0, sai dai tana nan a matsayi na biyar a teburin Premier.   Wannan ce nasara ta biyu da United ta yi a kan City a jere a Premier a karon farko tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi murabus.   Anthony Martial ne ya fara jefa kwallo ta farko a minti na 30, kuma kwallo ta 11 kenan da ya zira a gasar ta bana.   Martial ne dan wasan da ya fara cin kwallo sau uku a wasan hamayyar Manchester a jere tun bayan Eric Cantona a 1993 da kuma 1996.   Sergio Aguero ya zira kwallo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sai dai an hana kwallon saboda ya yi satar gida.   Scott McTominay ya kara kwallo ta biyu a karshen lokaci bayan kuskuren da golan City Ederson ya yi.   United za ta buga wasanta na g...
Maki 9 ya ragewa Liverpool ta dauki kofin Premier League

Maki 9 ya ragewa Liverpool ta dauki kofin Premier League

Uncategorized
Kungiyar Liverpool ta lallasa AFC Bournemouth da ci 2-1 a wasan da suka buga na ranar Asabar inda Bournemouth ce ta fara cin kwallo mintuna 9 kacal da take wasa amma Mohamed Salah da Sadio Mane suka farke kwallon suka kuma kara.   Saidai da kyar liverpool ta sha a wasan dan kuma Bournemouth ta so ta kara mata kwallo wadda shiga raga kawai zata shiga dan ta tsallake gola amma James Milner ta fitar da ita, ya sha yabo sosai kan wannan bajinta.   https://twitter.com/my_supersoccer/status/1236291194264657927?s=19   https://twitter.com/LFC/status/1236413817627774976?s=19 Da wannan nasara,Liverpool ta yi nasara a karin farko tun bayan rashin nasara da ta jera wasanni 3 tana yi a baya.   Kwallon da Mohammed Salah yaci itace kwallonshi ta 80 a was...