
Kungiyar PSG zata kashe yuro muliyan 6 sakamakon korar kocin ta, Thomas Tuchel
A makon daya gabata ne kungiyar zakarun kasar Faransa ta kori kocin ta Thomas Tuchel bayan ya shafe kakanni biyu yana jagorantar kungiyar, yayin da kuma tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino yake shirin maye mata gurbin shi.
Kungiyar Paris Saint German ta kammala tattaunawa da kocin nata wanda ta kora Thomas Tuchel akan ya ya bar kungiyar cikin gaggawa, kuma hakan zai sa mai kungiyar Naseer Al Khelaifi ya kashe yuro miliyan 6.
Yayin da kuma Pochettino wanda yake shirin maye gurbin Tuchel a matsayi sabon koci ya amince da kwantirakin da kungiyar Paris din tayi mai, a cewar gwanin kasuwar kwallon kafa Fabrizio Romano.