fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Tag: PSG

Kalli yanda Neymar ya fashe da kuka bayan da suka ci Dortmund 2-0

Kalli yanda Neymar ya fashe da kuka bayan da suka ci Dortmund 2-0

Wasanni
Bayan da PSG ta yi nasara a wasan da suka buga da Borussia Dortmund,  Dan wasa kungiyar, Neymar ya fashe da kukan murna.   Neymar dinne ya fara ciwa PSG kwallo a wasan na yau.   An ganshi zaune yana kuka inda abokan aikinshi suka zo suna bashi baki.   Kusan shekaru 4 kenan PSG bata wuce wannan matakin ba a gasar ta Champions League.   https://twitter.com/allabout_neymar/status/1237868094296485896?s=19
PSG ta fitar da Dortmund daga Champions League,  Neymar ya kafa Tarihi

PSG ta fitar da Dortmund daga Champions League, Neymar ya kafa Tarihi

Wasanni
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta lallasa Borussia Dortmund da ci 2-0 a wasan zagaye na biyu na kungiyoyi 16 da suka rage na gasar Champions League da aka yi a daren Laraba. Neymar ne ya fara ciwa PSG kwallo wanda a lokacin murnar cin kwallon saida ya kwaikwa yi irin murnar cin kwallon da dan kwallon Dortmund, Erling Braut Haaland ke yi. Bernat ne ya ciwa Liverpool kwallo ta 2. Neymar ya ci jimullar kwallaye 35 kenan a gasar ta Champions League.   Bayan kammala wasan, sai da 'yan wasan PSG suka zauna kasa suka kwaikwayi murnar cin kwallo ta Haaland. Dan wasan Dortmund, Can ya samu jan kati na kaitsaye bayan da ya ture Neymar a wasan.   Da wannan sakamako PSG ta kai ga wasan Quarterfinals na gasar ta Champions League.
Bisa zargin Kamuwa da cutar Coronavirus-Covid-19 Mbappe ya kauracewa Atisaye

Bisa zargin Kamuwa da cutar Coronavirus-Covid-19 Mbappe ya kauracewa Atisaye

Wasanni
Paris Saint Germain (PSG) a ranar Talata ta yiwa tauraron matashin dan wasanta, Kylian Mbappé gwaji don ganin ko yana da cutar COVID-19 tun bayan da dan wasan ya kauracewa Atisaye har na tsawan kwana biyu (Litinin da Talata) inda aka rawaito dan wasan na fama da ciwo a Makogaro , in ji rahoton jaridar Faransa, L’ Lquipe.   A sakamakon gwajin da kawararrun likitocin kungiyar (PSG) suka sanar ya tabbatar da dan wasan bai kamu da cutar COVID-19 ba.   Ana tunanin Mbappe shine dan kwallon kafa na farko da aka fara masa gwajin cutar COVID-19, wanda ya bazu ko'ina cikin Duniya a cikin 'yan makonnin nan.   Har yanzu ba a tabbatar da matsayin Mbappe ba game da wasan da kungiyarsa zata buga da Borussia Dortmund na gasar Champions League zagaye na 2 na kungiyoyi 16 da...