Kalli malamar data saka rigar kariya tabar dalibanta hakanan lokacin da zasu hau kwale-kwale
Wannan wata malamar makarantace data dauki dalibanta zuwa gurin yawon bude ido, wanda zasu hau kwale-kwale a tsallake ruwa dasu, abinda ya dauki hankulan mutane akan wannan hoton shine yanda matar ta saka rigar kariya wadda koda, abin Allah kiyaye, jirgin ruwan ya nutse to ita bazata nutse ba, amma ga duk daliban nata nan babu me irin wannan rigar kariyar.
Mutane da dama sun bayyana wannan hoton da cewa yayi nunine da irin rashin adalcin dake faruwa a gurare daban-daban, haka kuma ya jawo hankulan mutane cewa su lura da irin mutanen da suke barwa 'ya'yayensu su kular musu dasu.