Friday, May 29
Shadow

Tag: Real Madrid

Bale yace izgilin da masoyan Madrid yake mai yasa ya fara sarewa

Bale yace izgilin da masoyan Madrid yake mai yasa ya fara sarewa

Wasanni
Dan wasan kasar Wales din ya kasance abun cecekuce daga wurin wasu masoyan Real Madrid a wasanni da dama tun da Madrid suka siye shi daga kungiyar Tottenham a shekara ta 2013. A watan nuwamba, Bale yayi bikin murnar Euro 2020 a kasar shi ta Wales yayin da suka rike wata pasta wadda aka rubuta Wales Golf Madrid, kuma hakan ya kara sa masoyan Madrid din sun cigaba dayi mai izgili a lokacin daya koma kungiyar. Bale ya gayawa US GOLF cewa suna samun damuwa sosai a kowane wasa kuma in idan mutun bai yi kokari sosai ba akwai tsaro. Bale yace yaji mutane har 80,000 a filin wasa suna yin izgili akan shi saboda bai yi kokari sosai ba. Kuma wannan ingilin zai iya sa dan wasa ya fara sarewa. An tambaya Bale cewa me yasa mutanen suke yi mai haka?, sai yace wannan itace babbar tambayar d...
Iturralde Gonzalzez: kashi 90 bisa 100 na alkalan wasa masoyan Madrid ne

Iturralde Gonzalzez: kashi 90 bisa 100 na alkalan wasa masoyan Madrid ne

Wasanni
Tsohon alkalin wasa na kasa Eduardo Iturralde Gonzalez ya bayyana cewa kashi 90 bisa dari na alkalan wasan kasar Spain Masoyan Madrid ne, sai kuma sauran kashi 10 Masoyan Barcelona ne. Iturralde ya gayawa 'El Laguero cewa ko Barcelone suna so ko basa so kashi 70 bisa dari  na mutanen kasar Spain masoyan Madrid ne amma banda yan Catalonia.   Ya kara da cewa yanzu Barcelona suna da masoya da dawa saboda matasa sunga irin nasarorin da Pep Guardiola ya kawoma kungiyar.   Kuma an tambaya Iturralde cewa shin tsakanin Barcelona da Madrid su waye alkalan wasa suke fi nunawa banbanci?, sai Madrid suka fi so domin kamar kashi 90 cikin dari ne.
Wakilin Neymar, Wagner Rabeiro ya bayyana kungiyar da dan wasan zai cigaba da wasa bayan ya tattauna da shugaban Madrid

Wakilin Neymar, Wagner Rabeiro ya bayyana kungiyar da dan wasan zai cigaba da wasa bayan ya tattauna da shugaban Madrid

Wasanni
Wakilin Neymar Wagner Rabeiro yace dan wasan ba zai koma Barcelona ba idan aka bude kasuwar yan wasan kwallon kafa saboda abin da annobar Covid-19 ta saka duniyar wasan kwallon ciki.     Rabeiro ya gayawa TalkSport cewa yana ganin Neymar zai cigaba da wasa a kungiyar Paris Saint German saboda an samu canji a kasuwar yan wasa kuma tattalin arziki wasan kwallon kafa zai canja. A kakar wasan bara, Madrid sun so su siya Neymar bayan Robeiro ya tattauna da shugaban kungiyar Florentino Perez. A watan mayu na shekarar data tabbata, Robeiro ya ziyarce Perez a ofishin shi kuma ya tabbatar mai da cewa yana da burin siyan Neymar.
Varane ya bayar da tallafin euros 4,300 bayan yayi gwanjo daya daga cikin rigunan shi

Varane ya bayar da tallafin euros 4,300 bayan yayi gwanjo daya daga cikin rigunan shi

Wasanni
Har yanzu Varane yana son Lens sosai dakuma makarantar Kungiyar domin a nan ne ya fara buga wasan kwallon kafa, kuma yanzu haka yayi gwanjo daya daga cikin rigunan shi domin ya bayar da tallafin kudin ga asibitocin dake garin su. Kungiyar Lens sun saba siyan gwanjon rigunan tsofaffin yan wasan su, kuma yanzu sun siya rigar dan wasan Madrid din a farashin euros 4,350. Yanzu kungiyar sun tara euros 23,800 yayin da suka siyar a rigar Daniel Leclerq a farashin euros 6,500. Kuma yafi tsada akan ta Varane. Dan wasan baya na Madrid din ya zamo daya daga cikin zakarun kasar faransan da suka taimaka wajen lashe gasar kofin duniya a shekara ta 2018. Varane da Banzema sune kadai yan wasan faransan da suka lashe gasar champions lig har sau hudu. Kuma yadda yake rayuwar shi ba tare...
Real Madrid zasu bar Gareth Bale da James Rodriguez su bar kungiyar a kyauta idan aka bude kasuwar yan wasan kwallon kafa

Real Madrid zasu bar Gareth Bale da James Rodriguez su bar kungiyar a kyauta idan aka bude kasuwar yan wasan kwallon kafa

Wasanni
An samu labari cewa kungiyar Real Madrid zasu bar Gareth Bale da James Rodriguez su bar kungiyar a kyauta idan bude kasuwar yan wasan kwallon kafa, duk da cewa su manyan yan wasa ne kuma duniya ta san su amma Real Madrid zasu bar su su tafi domin su rage tsarin biyan albashin su. Saboda yanayin anayin albashin da suke dauka, an cire masu farashi saboda kungiyoyin da suke harin siyan su baza su iya siyan su ba kuma su cigaba da biyan makudan kudade ba. Manema labarai na Daily Mail sun ce shugabannin kungiyar Madrid sun cirewa yan wasan farashi saboda su siyar dasu cikin sauki. Shugaban gasar la liga Javier Tabas yace kungiyoyin la liga musamman Madrid da Barcelona zasu ragewa yan wasan su farashi saboda annobar cutar coronavirus. Kuma hakan zai sa kungiyoyin nan guda biyu su r...
Hotuna da Bidiyo: Yanda Kungiyar Real Madrid ta yi Atisaye a yau

Hotuna da Bidiyo: Yanda Kungiyar Real Madrid ta yi Atisaye a yau

Wasanni
Kungiyar Real Madrid ta dawo da Atisaye a yau a karin farko tun bayan da aka dakatar da wasanni dalilin Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 Eden Hazard wanda ya dade be bugawa kungiyar wasa ba saboda jinya shima an ganshi a yau yana motsa jiki tare da abokan aikinsa. Saidai kash,Armashin wasan ba kamar yanda aka sababa, Za'a bugane babu 'yan kallo dan dakile yaduwar cutar. Abbar Coronavirus/COVID-19 ta sa an dage buga wasanni wanda hakan ya tana tattalin arzikin kungiyoyi da dama suka rika ragewa 'yan wasansu Albashi. Abin jira a gani shine wasannin zasu yi Armashi kamar a baya kuwa? https://twitter.com/realmadriden/status/1259843334551584768?s=19   https://twitter.com/realmadriden/status/1259875920833200129?s=19
Real Madrid sun cigaba da atisayi a karo na farko tun bayan dakatar da wasannin kwallon kafa

Real Madrid sun cigaba da atisayi a karo na farko tun bayan dakatar da wasannin kwallon kafa

Wasanni
A yau ranar litinin 11 ga watan mayu yan wasan kungiyar Madrid suka cigaba da yin atisayi amma ba a kungiyance ba, kuma sun kasu kashi biyu yayin da kashi na farko suka je filin atisayin karfe 9 su kuma na biyu suka je karfe 11. Javier Tabas ya sanar cewa ana sa ran cigaba da buga wasannin gasar La Liga 12 ga watan yuni idan har kunyoyin sun bi dokokin da aka tsara masu. Yan wasan da suka yi atisayi karfe 9 sun hada da Ramos, Kroos, Lucas Vasquez, Modric, Hazard, Casemiro, Bale, Cavajal, Nacho da Altube. Su kuma yan wasan da suka yi atisayi karfe 11 sun hada da Mariano, Asensio, Rodrigo, Mendy da Valverde. Sun yi atisayi ne bayan su Ramos sun bar filin, sun bi dokokin da aka tsara masu kuma basu mu'amalanci junan suba amma sai dai basu sa abun rufe fuska ba.
Coronavirus: Madrid zasu kara ragewa yan wasan su kashi 30 bisa dari nadaga albashin su

Coronavirus: Madrid zasu kara ragewa yan wasan su kashi 30 bisa dari nadaga albashin su

Uncategorized
Real Madrid zasu kara ragewa tawagar Zinedine Zidane kashi 30 bisa dari a kakar wasa mai zuwa bayan sun rage masu kashi 10 a wannan kakar wasan saboda annobar cutar coronavirus da tasa an dakatar da wasannin kwallon kafa. An tilatawa gabadaya kungiyoyin La Liga na nahiyar turai cewa dole ne su karbi ragin albashi saboda cutar coronavirus ta dakile gabadaya hanyoyin samu kudi na wasanni kwallon kafa a fadin duniya. Gabadaya albashin da kungiyar Madrid suke biyan yan wasa 11 na farko ya kai euros miliyan 283, kuma idan suka rage kashi 30 bisa dari zasu samu ragin euros 100 a shekara. Sergio Ramos da Gareth Bale sune yan wasan da suka fi sauran yan kungiyar Madrid daukar albashi mai tsoka, a kowace shekara suna daukar albashin euros miliyan 14.5 yanzu kuma da aka rage albashin z...
Madrid zasu fara gudanar da atisayi ranar litinin 11 ga watan Mayu

Madrid zasu fara gudanar da atisayi ranar litinin 11 ga watan Mayu

Wasanni
Annobar cutar Covid-19 tasa an dakatar da wasannin kasar Spain tun ranar 12 ga watan maris yayin da gwamnatin kasar tasa dokar zaman gida domin a rage yaduwar cutar. A lokacin da gwamnati tasa dokar zaman gida, yan wasan 11 na farko suna cigaba da yin atisayi a cikin gidajen su yayin da su kuma Hazard da Asensio zasu amfana da wannan dokar da gwamnati tasa har su warke daga raunukan da suke fama kafin a cigaba da buga wasanni. Hukumar la liga sun sanar cewa zasu dawo kan aiki a tsakiya watan yuni, yayin da kungiyar Madrid zasu fara gudanar da atisayin su a ranar litinin 11 ga watan mayu ba tare da yan kallo ba kuma ba ba'a kungiyance ba.
Sakamakon gwajin cutar Covid-19 da kungiyar Real Madrid suka yi ya bayyana

Sakamakon gwajin cutar Covid-19 da kungiyar Real Madrid suka yi ya bayyana

Wasanni
Gabadaya yan wasan 11 na farko a kungiyar Real Madrid sunyi gwajin cutar coronavirus a ranar laraba bayan an ba kungiyoyin La liga damar cigaba yin atisayi. Amma sai dai kafin a fara yin atisayin yan wasan sunyi gwajin cutar Covid-19. A cewa manema kabari na ESPN, sakamakon gwajin da yan wasan Madrid suka yi ya nuna cewa gabadayan su basa dauke da cutar Covid-19, saboda haka Madrid zasu fara gudanar da atisayin su bada dadewa ba. Manema labaran sun kara da cewa manajan Madrid Zinedine Zidane tare da sauran kochinan su da dukkan sauran ma'aikatan da suke da alaka da yan wasan basa dauke da cutar Covid-19.