Sunday, May 31
Shadow

Tag: Sallar Idi

Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Musulman Najeriya ta yi kira da a tsige gwamnonin da suka bari aka yi Sallar Idi a jihohinsu

Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Musulman Najeriya ta yi kira da a tsige gwamnonin da suka bari aka yi Sallar Idi a jihohinsu

Siyasa
Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Musulmai a Najeriya,MURIC ta yi kira da a tsige gwamnonin da suka bari aka yi sallar idi karama a jihohinsu.   Kungiyar ta bayyana cewa gwamnati ta baiwa gwamnonin shawarar kada a yi bukukuwan sallar Idi saboda kokarin da ake na dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 amma su ka yi kunne kashi. Tace idan dai har Kiristoci zasu hakura da bikin Easter saboda Annobar Coronavirus to ya kamata ace musulmai ma sun hakura da Idi saboda cutar.   A sanarwar da kungiyar ta fitar ta bakin shugabanta, Ishaq Akintola tace dan tana kare hakkin Musulmai ba zata yi shiru idan taga sun aikata abinda ba daidai ba.   Ta kara da cewa yanzu abinda gwamnonin suka bari aka yi ya saka rayuwar mutane cikin hatsari ta yanda sai nan da sati...
Jihohin Borno,Zamfara, Kano, Katsina, sun yi Fatali da Umarnin Sarkin Musulmi da na gwamnatin taraya inda suka yi tururuwa zuwa masallatan Idi

Jihohin Borno,Zamfara, Kano, Katsina, sun yi Fatali da Umarnin Sarkin Musulmi da na gwamnatin taraya inda suka yi tururuwa zuwa masallatan Idi

Uncategorized
Duk da kiran kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 da kuma sarkin Muslimi na cewa kada ayi taro da yawa a wajan Salar Idi amma jihohin Zamfara, Bauchi, Katsina, Kano, Borno basu bi waccan shawara ba.   A Sallar Idin da aka yi jiya, Masalata a Kano sun yi fitar farin dango inda wasu sun saka abin rufe hanci amma wasu basu saka ba, sannan maganar nesa-nesa da juna a masallatan idin da dama ba'a bita ba, Kamar Yanda Punch ta ruwaito. Hakanan a jihar Borno ma yawan mutanen da suka fito Sallah yasa dokar nesa-nesa da juna ta zama abu me wuyar aiwatarwa.   Hukumomi dai sun yi kira da kada a cakudu da yawa dan dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.   Shugaba Buhari da Iyalansa a Gida suka yi Sallah inda ya bayyana cewa yayi haka...
Ranar Asabar ce Sallar Idi a Jamhuriyar Nijar

Ranar Asabar ce Sallar Idi a Jamhuriyar Nijar

Uncategorized
Majalisar Malaman addinin Musulunci da ke jamhuriyar Nijar ta ce ranar Asabar ne Sallah karama a jamhuriyar bayan ganin jaririn wata a garuruwa biyar a fadin kasar.   Wata sanarwa da Majlaisar ta fitar ta ce an ga jariirn watan na Shawwal a birnin Magaria da ke cikin jihar Damagaram wato Zinder da kuma a garuruwan Maine-Soroa da N'guiguimi da N'Gourti da ke cikin jihar Diffa mai iyaka da jihar Borno a Najeriya.   Haka ma jinjirin watan Shawwwal ya samu fita a garin Oungoudague da ke cikin yankin Tsibirin Gobir dake gundumar Gidan Rounji a jihar Maradin Katsina.     Majalisar ta ce ranar Asabar ne 1 ga watan Shawwal. Hakan na nufin al'ummar jamhuriyar Nijar sun yi azumi 29.     Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Saud...
Ba zamu taba bari a yi taron addini da shagulgulan sallah a Kano, Legas, Ogun da Abuja ba>>Hukumar ‘yansanda

Ba zamu taba bari a yi taron addini da shagulgulan sallah a Kano, Legas, Ogun da Abuja ba>>Hukumar ‘yansanda

Tsaro
Shugaban hukumar 'yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya taya 'yan Najeriya murnar kammala azumin watan Ramadana lafiya inda yace lokacine da mutane da kansu suke komawa ga Allah tare da tsakake kai.   Ya jajantawa mutane kan halin da Sallah ta samu mutane a ciki na cutar Coronavirus/COVID-19 inda yace kada a manta da dokokin da aka tanada. Sanarwar hakan ta fitone daga gurin me magana da yawun hukumar,FCP Frank Nba inda ya jaddada cewa akwai dokar hana zirga-zirga da kuma hana taron addini dana al'ada da aka saba yi dan hana yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.   Yace zasu kai jami'an su guraren da ya kamata dan ganin cewa ba'a take doka ba sannan kuma zasu tsaurara tsaro a lokacin sallar da bayanya.   Ya kara da cewa zasu tsaurara tsaro a garuruw...
Ni da iyalina za mu yi Sallar Idi a gida>>Buhari

Ni da iyalina za mu yi Sallar Idi a gida>>Buhari

Siyasa
Shugaban Najeriya Muhammadu ya ce shi da iyalinsa za su yi Sallah Idi a gida. A sanarwar da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma'a, ya ambato Shugaba Buhari yana cewa zai yi Salar Idi a gidan ne domin yin biyayya ga umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar cea kowa ya yi sallar Idi a gida. "Na dauki matakin ne bisa umarnin da Sultan na Sokoto kuma Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayar na dakatar da yin sallar Idi a kasa baki daya, " a cewar Shugaba Buhari. Saidai a wannan karin shugaban ba zai karbi gaisuwar Sallah kamar yanda aka saba yi a baya ba daga masu rike da mukaman siyasa da shuwagabannin al'umma ba, kamar yanda sanarwar ta bayyana.
Ku yi Sallar Idi a gida>>Gwamnatin tarayya ga Musulmai

Ku yi Sallar Idi a gida>>Gwamnatin tarayya ga Musulmai

Uncategorized
Gwamnatin tarayya ta bukaci musulman kasar da su yi Sallar Idi a gida ba tare da haduwa a Masallaci ba.   Wannan kiran ya zo ne daga bakin me tsare-tsare na kwaitin shugaban kasa dake yaki da cutar Coronavirus/COVID-19,  Sani Aliyu a jiya,Talata, Yayin da yake ganawa da manema labarai.   Yace Sallar idi na da muhimmanci amma duk da haka suna kira ga 'yan uwa musulmai maza da mata da su yishi a gida.   Yace kwamitin nasu zai yi aiki da gwamnatocin jihohi dan ganin an yi aiki da unarnin shugaban kasa ama duk da haka ba zaa ki bin abinda ya dace da al'ummar jihohin ba.   Saidai yace duk wata shawara da za'a dauka be kamata ta zama wadda zata mayar ma da gwamnati hannun Agogo baya bace.   Shima kuma a jawabinsa,shugaban Kwamitin, wanda
Sallar Idi: El-Rufa’i yayi watsi da bukatar limaman Kaduna

Sallar Idi: El-Rufa’i yayi watsi da bukatar limaman Kaduna

Siyasa
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i yayi watsi da bukatar da tawagar limamai da malaman jihar Kaduna, ya hana a fita ranar Asabar, ranar da ake saran za a yi idin sallah karama.     A ranar lahadi, 17 ga watam Mayu, tawagar limamai da malaman suka bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta duba yiwuwar  sassauta dokar kulle a jihar domin rage wa al’umar jihar wahalhalun da suke ciki.     A sanarwar da limaman da malaman suka fitar, sun jadadda mahimmancin lura da mataken kare yaduwar cutar COVID-19 a lokacin da suka bukaci a duba yiwuwar sassauta dokar kullen domin jama’ar jihar su sami sa’ida.     Haka zalika sun yaba wa gwamnatin jihar bisa kwararan matakan da take dauka domin kare yaduwar cutar a jihar Kaduna.   &n
Za’a yi Sallar Idi amma a masallatan Juma’a>>Sarkin Musulmi

Za’a yi Sallar Idi amma a masallatan Juma’a>>Sarkin Musulmi

Uncategorized
Mai Martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku ya ce bana za a gudanar da Sallar Idin ne a masallatan Juma’a.     Hakan dai sabanin yadda al’ummar Musulmi suka saba taruwa ne a duk shekara don gudanar da sallar ta idi bayan kammala azumin watan Ramadan.     Mai Martaba ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da wasu shugabannin al’umma da ke cikin jihar Sokoto su 86, dangane da abin da ya shafi sallar idi da kuma wasu batutuwa daban.     Ya kuma bukaci shugabannin da su gargadi jama’arsu akan yin biyayya da wannan matsaya da aka cimma a jihar Sokoto da ma wasu jihohin kasar.     Mai Martaban ya kuma yi kashedi ga jama’a akan cewa kada su yi tunanin ana yunkurin hana su sallar Idi ne, amma an dauki
Ka gaya mana zamu samu damar yin Sallar Idi ko kuwa a’a?>>Kungiyar Limaman Kano ta Tambayi gwamna Ganduje

Ka gaya mana zamu samu damar yin Sallar Idi ko kuwa a’a?>>Kungiyar Limaman Kano ta Tambayi gwamna Ganduje

Uncategorized
Kungiyar Kimaman Kano ta nemi gwamnatin jihar ta sanar da ita matsayinta kan sallar Idin karamar sallah, shin zata samu yi ko kuwa a'a?   A yanzu haka dai gwamnatocin jihohi sun kulle garuruwansu inda aka hana tarukan Ibada dana bukukuwa kuma mafi yawanci ana zaune a gida saboda dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 da har yanzu ba'a gano rigakafi ko maganinta ba.   Shugaban kungiyar Limaman,Sheikh Ibrahim Khalil ne ya bayyana haka bayan wani taro da kungiyar ta yi, yace mabiyansu nata ta tambayarsu shin za'a samu yin sallar Idi kuwa? Shiyasa suke son amsar wannan tambaya dan su san abinda zasu gaya musu.   Ya kuma kara da cewa, membobinsu sun nuna rashin jin dadinsu kan yanda gwamnati a damar data bayar na kwanaki 2 a rika fita Kasuwa, watau Alhami...