fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Tag: Sanata Shehu Sani

Yan Bindiga sun kashe dalibin kwalejin ilimi dake Zaria

Yan Bindiga sun kashe dalibin kwalejin ilimi dake Zaria

Siyasa
Yan bindiga a hanyar Birnin Gwari dake jihar Kaduna sun kashe dalibin kwalejin Ilimi dake Zaria me suna, Isa Shehu Abba dan kimanin shekaru 28.   Matashin yana kan hanyarsa ne ta zuwa karbar shaidar kammala karatu yayin da 'yan Bindigar suka kasheshi. https://twitter.com/ShehuSani/status/1310937957491183619?s=19   Sanata Shehu Sani ya bada labarin kashe dalibin ta shafinsa na Twitter.
A lokacin da tace mana zata rika cillawa ‘yan Gudun Hijira Abinci daga Jirgin sama duk bamu fahimci abinda take nufi ba sai yanzu>>Sanata Shehu Sani kan Auren Minista, Sadiya Umar Farouk

A lokacin da tace mana zata rika cillawa ‘yan Gudun Hijira Abinci daga Jirgin sama duk bamu fahimci abinda take nufi ba sai yanzu>>Sanata Shehu Sani kan Auren Minista, Sadiya Umar Farouk

Siyasa
Sanata Shehu Sani yayi magana kan auren da Ministar kula da Ibtila'i da Jinkai, Sadiya Umar Farouk ta yi da shugaban sojojin Saman Najeriya,  Air Marshal Sadiq Abubakar.   Ya bayyana ta shafinsa na sada zumuntar Twitter cewa, a lokacin da ta ce mana zata rika jefawa 'yan gudun Hijira Abinci daga jirgin sama, bamu fahimci abinda take nufi ba, Ina tayata Murna.   Duk da dai be bayyana sunanta ba, amma da dama sun yi ittifakin cewa da Ministar sanata Sani yake. https://twitter.com/ShehuSani/status/1309083857304670217?s=19
Dalilin da ka iya sa matasa su rika shiga Boko Haram>>Sanata Shehu Sani

Dalilin da ka iya sa matasa su rika shiga Boko Haram>>Sanata Shehu Sani

Tsaro, Uncategorized
Sanata Shehu Sani ya bayyana irin shatara ta arzikin da gwamnati kewa tubabbun 'yan Bindiga ka iya saka matasa su shiga harkar.   A sakon da ya fitar ta shafinsa na Twitter yake idan ka baiwa matashi me aikin N-Power Dubu 50 amma ka bada gidaje Shaguna da gonaki ga tubabbun 'yan Bindiga to matasan zasu shiga harkar 'yan Bindigar. https://twitter.com/ShehuSani/status/1306671155089223682?s=19
Daga kasar China Coronavirus/COVID-19 ta samo Asali amma Najeriya ta zama gidanta>>Sanata Shehu Sani

Daga kasar China Coronavirus/COVID-19 ta samo Asali amma Najeriya ta zama gidanta>>Sanata Shehu Sani

Uncategorized
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, daga kasar China cutar Coronavirus/COVID-19 ta samo Asali amma Najeriya sai ta zama gidanta.   Sanata Sani ya mayar da martanine akan labarin da Premium times ta buga na cewa gwamnati ta kashe Biliyan 31 cikin watanni 4 akan cutar Coronavirus/COVID-19. https://twitter.com/ShehuSani/status/1302562032793911296?s=19 Gwamnati dai ta bayyana hakane a matsayin Martani ga bukatar Kungiyoyin SERAP da CODE na cewa a musu bayanin yanda aka kashe kudin tallafin da aka samu akan cutar Coronavirus/COVID-19.
Wai matasa masu Jini a jika ne ke neman Atiku ya fito Zanga-zanga>>Sanata Shehu Sani

Wai matasa masu Jini a jika ne ke neman Atiku ya fito Zanga-zanga>>Sanata Shehu Sani

Uncategorized
A dazune dai muka kawo muku cewa matasan Najeriya sun nemi dan takarar shugaban kasa a shekarar 2019 karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya fito ya mudu jagora su yi zanga-zanga kan karin kudin man fetur.   Matasan sun danganta wannan kira nasu ne bisa makamancin irin wannan zanga-zanga da shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi a lokacin Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na kan mulki.   Sannan kuma sun bayyana cewa idan Atikun ya shiga zanga-zangar tasu babu wani jami'in tsaro da zai ci zarafinsu. Saidai Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa matasanne ya kamata suyi zanga zangar tunda sune masu jini a jika ba Atiku da ya fara tsufa ba. https://twitter.com/ShehuSani/status/1301574238969753601?s=19 Sanata Sani ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta.
Sanata Shehu Sani ya jinjinawa matasan da suka yi karan batta da ‘yan Bindigar da suka kaiwa garinsu hari a Katsina

Sanata Shehu Sani ya jinjinawa matasan da suka yi karan batta da ‘yan Bindigar da suka kaiwa garinsu hari a Katsina

Tsaro
A jiyane dai wasu matasa suka yi wa wasu 'yan Bindiga tara-tara bayan da suka kai musu hari, ga dukkan alamu mutane sun fara tashi tsaye inda a yauma an samu Rahoto makamancin haka.   Sanata Shehu Sani ya jinjinawa matasan bisa wannan karfin hali da suka nuna. Saidai yace ya kamata jami'an tsaro su kai musu dauki dan kada 'yan Bindigar su je ramuwar gayya. https://twitter.com/ShehuSani/status/1301151617790750722?s=19
Kisan Daliban Najeriya a kasar Northern Cyprus: Sanata Shehu Sani ya baiwa iyaye shawarar su dakata da kai ‘ya’yansu karatu kasar Waje

Kisan Daliban Najeriya a kasar Northern Cyprus: Sanata Shehu Sani ya baiwa iyaye shawarar su dakata da kai ‘ya’yansu karatu kasar Waje

Siyasa
Rahoton kisan dalibin Najeriya, Ibrahim Khaleel dan shekaru 25 a kasar Northern Cyprus da wasu karin dalibai 100 ya dauki hankula inda 'yan Najeriya ke ta mayar da martani kala-kala.   Sanata Shehu Sani ya baiwa iyaye shawarar su rika barin 'ya'yansu na karatu a Najeriya saboda Yanzu Duniya rikice-rikice sun mata yawa ga kiyayya. https://twitter.com/ShehuSani/status/1298143176591650816?s=19 Sanata Sani yace duk da Najeriyar ma bata tsira bane daga wannan tashe-tashen hankula amma dai a rika barin yara na karatu a gida zuwa matakin Digiri na farko akalla kamin ganin yanda al'amura zasu kasance.
Bai kamata ana nunawa ‘yan Shi’a da ‘yan IPOB karfin wuce kima ba>>Sanata Shehu Sani

Bai kamata ana nunawa ‘yan Shi’a da ‘yan IPOB karfin wuce kima ba>>Sanata Shehu Sani

Siyasa
A makon da ya gabatane dai aka samu arangama tsakanin 'yan Shi'a da jami'an tsaron 'yansanda inda rahotanni suka bayyana akalla mutane 3 sun rasa rayukansu.   Hakanan a jiya, Lahadi ne dai aka samu wata Arangamar tsakanin jami'an tsaro da 'yan Kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra.  Shimadai akalla mutane 3 ne suka rasa rayukansu inda hukumar DSS tace an kashe mata mutane 2.   Wannan yasa mutane suka fara bayyana ra'ayoyinsu akan wannan lamari. Daya daga cikin wadannan ra'ayoyi shine na Sanata Shehu Sani inda ya bada shawarar a daina nunawa 'yan Shi'a da 'yan IPOB karfi fiye da kima.   Sani ya fada ta shafinsa na Twitter cewa, duk da yake cewa akwai banbancin ra'ayi tsakanin 'yan Shi'a da IPOB da sauran Al'umma bai kamata ana amfani da karfin da ya wuce
A kur’ani da Baibul an fadi sunayen kasashen Egypt da Ethiopia amma me yasa muka fisu nuna tsauri akan Addini>>Sanata Shehu Sani

A kur’ani da Baibul an fadi sunayen kasashen Egypt da Ethiopia amma me yasa muka fisu nuna tsauri akan Addini>>Sanata Shehu Sani

Siyasa
Sanata Shehu Sani ya Tambayi 'yan Najeriya dalilin da yasa suka fi kasashen da har a Baibul da Qur'ani duk an ambacesu nuna tsaurin addini.   Shehu Sani yayi wannan tambayar ta shafinsa na sada zumunta inda yace kasashen Egypt da Ethiopia ne aka ambacesu a Qur'ani da Baibula amma me yasa muka fisu nuna tsaurin addini? https://twitter.com/ShehuSani/status/1297427443490467840?s=19 Ya kara da cewa wadannan kasashe sun riga iyaye da kakannin mu karbar Musulunci da Kiristanci amma mun fisu nunawa juna kiyayya da rashin hakuri da juna. A karshe ya tambayi ko menene dalilin hakan?
Bayan harin da matasa suka kaiwa Rarara, Sanata Shehu Sani ya baiwa mawakin shawara

Bayan harin da matasa suka kaiwa Rarara, Sanata Shehu Sani ya baiwa mawakin shawara

Siyasa
A jiyane muka samo muku wani Rahoto daga Rariya daya bayyana cewa an kaiwa mawakin siyasarnan, Dauda Kahutu Rarara hari a Katsina yayin da yake shirin wata waka da ya shirya a kan matsalar tsaro.   Rahoton yace a cikin tawagar da lamarin ya faru akwai tauraron fina-finan Hausa,  Ali Nuhu, Tijjani Asase da shahararren me shirya fina-finan Hausa,  Abba Mai shadda. Lamarin ya jawo cece-kuce da dama inda wasu suka jajanta, wasu kuwa ala kara suke. Shi kuwa sanata Shehu Sani shawara ya baiwa Rarara akan ya dena shigewa irin wannan matasa.   Sani da yake bayyana matsayinsa kan harin ta shafinshi na sada zumunta yace matasan sun wuce makadi da rawa inda yace shi Rarara ai nishadantarwa kawai yake.