
Shin wai Me zai hana ku kutsa cikin dajin Sambisa ku mamaye ko ina ku farauto ‘yan Boko Haram duk inda suke?>>Sarkin Musulmi ya tambayi sojojin Najeriya
Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya kakubalanci sojojin Najeriya da cewa, me zai hana su shiga dajin Sambisa su mamayeshi?
Ya bayyana hakane a ziyarar da ya jagoranci sarakunan gargajiya suka kaiwa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum dan ta'aziyyar mutane 43 da Boko Haram tawa yankan Rago a Zabarmari.
Ya kuma jawo hankalin gwamnoni da su tashi tsaye dan kare martabar tsaro a jihohinsu.