fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Sata

Kotu ta bada belin matashi akan Naira 500,000 saboda satar wayar Naira 36,000

Kotu ta bada belin matashi akan Naira 500,000 saboda satar wayar Naira 36,000

Uncategorized
Hukumar 'yansandan Najeriya ta gurfanar da wani matashi da ake zargi da satar waya a gaban Kotun Ikorodu dake jihar Legas.   Matashin dan shekaru 25, Adekusibe Ogunlokun ana zarginsa ne da satar waya kirar Itel P36 da ake sayarwa akan Naira 36,000. Saidai bayan karanto masa zarge-zargen da ake masa, Matashin ya musantasu duka.   Mai Shari'a T.A Elias ya bada belin wanda ake zargi akan Naira 500,000 da kuma kawo mutane 2 da zasu tsaya masa. Sannan ya daga shari'ar zuwa 26 ga watan Maris. Magistrate T.A. Elias on Wednesday admitted him to bail in the sum of N500,000 and also ordered the defendant to produce two sureties in like sum. He adjourned the case until March 26, for mention.
An yankewa makanike bulala 15 saboda satar waya a Kaduna

An yankewa makanike bulala 15 saboda satar waya a Kaduna

Uncategorized
Wata kotu a jihar Kaduna ta yankewa matashi, Amos Dauda hukuncin Bulala 15 saboda satar wayar iPhone da kudinta suka kai 150,000.   Matashin dake zaune a Barnawa, Kaduna an gurfanar dashi a gaban Kotu bisa zarge-zargen shiga gidan Mutane ba tare da izini ba da kuma sata.   Ya amsa laifinsa da kuma neman kotu ta mai sassauci wajan hukunci. Kamfanin Dillancin labaran Najeriya,NAN ruwaito cewa, Alkalin Kotun, Ibrahim Emmanuel ya yankewa Amos hukuncin bulala 15 da kuma wanke harbar kotun. Earlier, the prosecutor, Insp. Leo Chidi told the court that one Stephen Francis reported the matter at the Gabasawa Police Station on Nov. 15. According to the prosecutor, the convict went into the complainant’s apartment while he was sleeping and stole his iPhone valued at N1...
Mahaifin da aka sace diyarsa shekaru 4 suka gabata ya saki sako me taba zuciya

Mahaifin da aka sace diyarsa shekaru 4 suka gabata ya saki sako me taba zuciya

Uncategorized
Mahaifi, Umar Sulaiman wanda aka sace diyarsa shekaru 4 da suka gabata wanda dan jihar Nasarawa ne, ya saki sako me taba zuciya ta shafinsa na Facebook.   Ya bayyana cewa shi da iyalinsa suna cikin wani hali na kunci a cikin shekaru 4 da suka gabata, saboda Rashin Khadija.   Ya bayyana cewa a rana irin ta yau ne aka sace diyarsa wadda yanzu shekaru 4 kenan. Yace yana murmushi da mutane amma maganar gaskiya a cikinsa takaici ne saboda bakin cikin dan da aka sace maka yafi na wanda ya mutu.   Yace Khadija a ranar da aka sace ki, Mahaifiyarki ta shiga wani yanayi wanda a washe gari aka haifi Kaninki amma bamu taba murnar zagayowar ranar haihuwarsa ba saboda bakin cikin saceki ya fi farin cikin Haihuwarsa yawa.   Yayi fatan Allah ya kare diyar tasa a...
Hotunan Yanda akawa wata mata Tumbur saboda satar Rogo

Hotunan Yanda akawa wata mata Tumbur saboda satar Rogo

Uncategorized
'Yan Banga a jihar Rivers sun yiwa wata mata me suna Comfort Eze tumbur saboda satar Rogo inda aka rika yawo da ita cikin unguwa sai da kowa ya ganta Tsirara.   Yan bangar garin Ovogo na karamar hukumar Emuoha dake jihar ne sukawa matar da ake zargi da sarar rogo wannan aika-aika.   Da take gayawa manema labarai yanda lamarin ya faru a hedikwatar kungiyar mata lauyoyi na jihar ta Rivers, Comfort tace sun mata tsirara suka dauki hotunanta suka saka a shafukan sada zumunta. Sannan kuma suka zagaya da ita kowa ya ganta tsirara.   Sannan kuma sun nemi ta basu Naira dubu 60 a matsayin diyyar satar da suke zarginta da ita, tace ta biya Naira Dunu 52 amma har yanzu suna neman ta biya sauran Dubu 20.   “They tore my clothes, carried me out and blindfolde...
An daure ma’aikaciyar Bankin First Bank, Oreoluwa Adesakin, Shekaru 98 saboda satar miliyan N49

An daure ma’aikaciyar Bankin First Bank, Oreoluwa Adesakin, Shekaru 98 saboda satar miliyan N49

Uncategorized
An gurfanar da wata ma'aikaciyar bankin First Bank, Oreoluwa Adesakin, a gaban kuliya bisa laifin zamba, sannan Mai Shari'a Muniru Olagunju na Babbar Kotun Jihar Oyo ya ba ta hukuncin daurin shekaru 98 a gidan yari. Amma za ta yi shekaru bakwai a kurkuku. An gano Adesakin da aikata laifin zambar kudi a bankin First Bank har zuwa N49,320,652.32. Ta kuma saci dala 368,203.00 na bankin, wanda ta canza zuwa amfanin ta. Adesakin, kafin banki ya gano ta ya kore ta, ta kasance mai gudanar da aikin ta na Canjin Kudi, wanda aka dorawa alhakin aiwatar da biyan ta hanyar hanyar tura kudi ta Western Union da kuma MoneyGram, Ofishin shiyya na Ibadan na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu'annati, (EFCC) ne ya gurfanar da mai laifin a kan tuhume-tuhume 14, da suka hada da sat...
An gurfanar da matashin da ya saci Mashin din dansanda a Kotu

An gurfanar da matashin da ya saci Mashin din dansanda a Kotu

Tsaro
An gurfanar da matashi Mumini Huseeni dan shekaru 20 a kotu a garin Osogbo na jihar Osun bayan da ake zarginshi da satar mashin din jancan na wani sajan din dansanda.   Har cikin barikin 'yansandan matashin ya shiga ranar 2 ga watan Yuli ya saci mashin din kuma ya amsa laifinsa. Matashin yayi rokon a mai sassaucin hukunci, inda shine ke kare kanshi a gaban alkalin dan bashi da lauya.   Alkalin ya daga sauraren karar dai ranar Yuli 27.
An kama matashin da ya saci wayar Alkali

An kama matashin da ya saci wayar Alkali

Siyasa
'Yansanda a jihar Ebonyi sun kama wani matashi me shekaru 20, Obiemezie Chiekezie da zargin sace wayar wata Alkaliya.   Mai Shari'a,  Mrs. Ezeugo Esther na atisaye inda take sassarfa a bakin titi, nan ne marashin ya warci wayarta ta runtuma da gudu. An dai yi kokarin kamoshi amma abin ya faskara. Saidai da aka bibiyi wayar an ganota a hannunshi inda aka kamashi ranar Laraba. An gurfanar dashi ranar Juma'a.   Da yake bayyanawa kotu laifin wanda ake zargi, Dansanda, Sabastine Alinona ya bayyana cewa, ya kwace wayar kirar Samsun x20 da darajarta ya kai Naira 180,000 ya ruga da gudu.   Babu dai lauyan da ya wakilci wanda ake zargi. Amma mai shari'a Mrs Nnenna Onuoha ta bada binsa akan Naira Miliyan 1 da kuma wanda zai tsaya masa mutum 1 wanda shima yana ...
Kotu ta daure matashin da ya shiga Ofishin ‘yansanda Yayi Sata

Kotu ta daure matashin da ya shiga Ofishin ‘yansanda Yayi Sata

Uncategorized
Hukumar kotu ta tsare wani matashi dan shskaru 18, Oladayo Taiwo a jihar Osun da aka kama da laifin shiga ofishin 'yansanda yayi Sata.   Kotun dake Ille Ife ta kama yaron da laifin satar kayan Atamfa Yadi 12 da kuma Dubu 4, da na'urar DVD, da fanka ta tsaye, da Shinkafa kwatar kwano, dadai sauransu. Matashin ya shiga Ofishin Insfecta Vitowanu Bukolane inda ya dauki wadancan abubuwa.
Kotu a Kaduna ta daure Abdullahi Sani da Budurwarsa saboda satar Kaji

Kotu a Kaduna ta daure Abdullahi Sani da Budurwarsa saboda satar Kaji

Uncategorized
Kotun Majistre dake Kafancan a jihar Kaduna ta daure wani mutum, Abdullahi Sani me kimanin shekaru 35 da budurwarsa Sarah Paul saboda satar kaji 64.     An yankewa Sani hukuncin watanni 38 a gidan gyara hali sannan kuma zai biya mai karar kudi, 600,000 yayinda ita kuma Sarah aka yanke mata hukuncin watanni 13 sannan zata biya me kajin 200,00 saboda hannu da aka sameta dashi a cikin satar. Me kare wanda ya kai kara, Esther Bishen ta bayyanawa kotu cewa Hillary Garba ya kai korafi ranar 21 ga watan Matu inda yake zargin Sani da kutsawa cikin gidansa ya sace kaji 64 wanda kudinsu ya kai Naira 781,970.   An kama Sarah Paul yayin da take tsaka da dafa daya daga cikin kajin. Duka dai masu laifin sun amsa laifinsu a gaban Kotu.