fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Tag: Saudi Arabia

Shin Tashin Duniyane ya zo?: Kalli Bidiyon yanda Sararin Samaniyar Masallacin Ka’aba yayi jaaa jawur

Shin Tashin Duniyane ya zo?: Kalli Bidiyon yanda Sararin Samaniyar Masallacin Ka’aba yayi jaaa jawur

Uncategorized
Tun a makon da ya gabata ne ake yada wani bidiyo da ke nuna yadda sararin samaniyar Masallacin Ka'aba da ke Saudiyya ya rikide ya zama ja jazur. Bidiyon wanda ya yaɗu kamar wutar daji musamman a shafin sada zumunta na Whatsapp, ya sa mutane da dama sun yi amanna cewa "Alamu ne na Tashin Alƙiyama." https://m.youtube.com/watch?v=9ZB9YE5ewqI A saƙon da ke tafe da bidiyon an rubuta cewa: ... "wannan ne abin da ya faru a Saudiyya a yau, iska mai tafe da guguwar rairayin hamada mai launin ja ta rufe sararin samaniyar Masallacin Harami da kewaye." Ganin yadda mutane da dama da ke ci gaba da yaɗa saƙon sun yi amannar cewa alamu ne na tashin Alƙiyama ya sa BBC ta bi diddigin bidiyon. https://twitter.com/iUmarKhattak/status/1372574526450589700?s=19 Mun tuntuɓi huk...
Hajj 2021: Duk wanda ba a yi wa rigakafin korona ba ba zai yi ibadar ba>>Saudiyya

Hajj 2021: Duk wanda ba a yi wa rigakafin korona ba ba zai yi ibadar ba>>Saudiyya

Tsaro, Uncategorized
Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta sharɗanta wa dukkan alhazai daga ƙasashen waje su yi allurar rigakafin cutar korona sau biyu kafin gudanar da aikin Hajjin shekara ta 2021. Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ma'aikatar na cewa wajibi ne a yi wa mahajjaci allura ta biyun, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da ita. mako ɗaya kafin ya isa Saudiyya. Kazalika, alhazai za su je da takardar gwajin cutar wadda ke nuna cewa ba sa ɗauke da ita wadda kuma aka yi kwana uku kafin isarsu ƙasar. Haka nan sai sun killace kansu na tsawon kwana uku. Alhazai za su fito ne kawai bayan gwaji ya tabbatar ba sa ɗauke da cutar. Ma'aiikatar ta kuma ƙayyade cewa 'yan shekara 18 zuwa 60 ne kaɗai za su yi aikin hajji na shekarar Hijira ta 1442. Sauran sharuɗɗ...
Cristiano Ronaldo ya ki amincewa da tayin £5.3M dan ya zama jakadan Kasar Saudi Arabia kan yawon bude ido

Cristiano Ronaldo ya ki amincewa da tayin £5.3M dan ya zama jakadan Kasar Saudi Arabia kan yawon bude ido

Wasanni
Rahotanni sun bayyana cewa tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya ki amincewa da tayin £5.3M dan ya zama jakadan kasar Saudiyya wajan yawon bude Ido.   Wannan yarjejeniya ta bukaci cewa Cristiano Ronaldo zai kai ziyara kasar sannan kuma za'a yi amfani da hotunansa wajan tallata jawo hankalin masu yawon bude ido cikinta.   Saidai ya ki amincewa da hakan. Wakilan kasar Saudiyyar sun kuma kusanci, Lionel Messi shima akan wannan tayi amma babu bayani kan ko ya amince ko kuwa a'a.   Telegraph tace wakilan 'yan wasan biyu sun ki su ce uffan kan lamarin. Cristiano Ronaldo has reportedly turned down a multi-million-pound offer to become the face of Saudi Arabian tourism. The deal amounted to €6million ...
Bidiyo: Wasu Matan Najeriya da suka makale a Saudi Arabia na kira gwamnati ta taimakesu ta dawo dasu gida

Bidiyo: Wasu Matan Najeriya da suka makale a Saudi Arabia na kira gwamnati ta taimakesu ta dawo dasu gida

Uncategorized
Wasu matan Najeriya da suka makale a Saudiyya na ci gaba da aiko Bidiyo inda suke neman gwamnati ta taimakesu ta dawo dasu gida.   A baya ma dai munga yanda Bidiyon wata da ta yi ikirarin tana maganane da yawun matan Najeriyar dake zaune a Saudiyya ta fito ta bayyana cewa suna neman daukin gwamnati.   A wannan karin bidiyon sun kara yawa inda wasu suka aikewa tauraruwar fina-finan kudu, Toyin Abraham kuma ta saka a shafinta tana nema musu dsukin gwamnati.   Wasu kuwa sun saka a shafukan Twitter ne. https://twitter.com/toyin_abraham1/status/1291080257836060678?s=19   https://twitter.com/toyin_abraham1/status/1291080615878631426?s=19   https://twitter.com/toyin_abraham1/status/1291077771104485376?s=19
Saudiyya na son dawo damu gida kyauta amma Gwamnatin Najeriya tace sai mun biya kudin jirgi>>Daliban Najeriya da suka Makale a Saudiyya

Saudiyya na son dawo damu gida kyauta amma Gwamnatin Najeriya tace sai mun biya kudin jirgi>>Daliban Najeriya da suka Makale a Saudiyya

Siyasa
Daliban Najeriya dake karatu a kasar Saudiyya sun koka kan abinda suka zarga na cewa hukumomin Najeriya na zagen kasa wajan dawowarsu gida.   Daya daga cikin daliban me suna Ayo, ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya ta bayar da jirage a mayar da dalibai kasashensu amma ofishin jakadancin Najeriya dake kasar ya ki bada hadin kai. Yace akwai tsarin da ake bi kamin Saudiyyar ta bayar da jirgin, saidai Ofishin jakadancin Najeriya dake kasar ya aikewa Saudiyyar cewa ba sai ta bada jirgi ba, akwai jirgin da zai zo daga Najeriya ya dauki Daliban, yace amma fa an ce sai sun biya kudin jirgi yayinda shi kuma jirgin kasar Saudiyya kyauta zai mayar dasu gida.   Wani Dalibin yace sun kaiwa kasar Saudiyyar kuka inda tace Ofishin jakadancin Najeriya ne yaki bada hadin kai, dal...
An yi nasarar yi wa Sarki Salman na Saudiyya tiyatar mafitsara

An yi nasarar yi wa Sarki Salman na Saudiyya tiyatar mafitsara

Siyasa
An yi nasarar yi wa Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdul'aziz tiyatar mafitsara a asibitin King Faisal da ke Riyadh, babban birnin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya sanar a ranar Alhamis. Sanarwar ta ci gaba da cewa Sarki Salman zai shafe wasu kwanaki a asibitin don ci gaba da kula da lafiyarsa bisa shawarar tawagar lafiyar da ta duba shi. A ranar Litinin 20 ga watan Yulin nan ne Saudiyyar ta sanar da batun kwantar da Sarki Salman a asibitin Riyadh inda ake yi masa gwaje gwaje. Bayanai sun ce Sarkin mai shekara 84 na fama ne da rashin lafiyar da ta shafi mafitsara. Tun 2015 Sarkin ke mulki a Saudiyya - kafin zamansa Sarki ya shafe shekara kusan biyu a matsayin Yarima mai jiran gado kuma ya taba rike mukamin mataimakin firimiya a 2012. Ya kuma shafe sama da sh...
Ba za a buɗe Masallacin Harami Ranar Arafa da Ranar Sallah ba

Ba za a buɗe Masallacin Harami Ranar Arafa da Ranar Sallah ba

Uncategorized
Manjo Janar Mohammed Bin Wasl Al-Ahmadi, mataimakin shugaban jami'an tsaro na Masallacin Harami yayin aikin Hajji, ya faɗa ranar Talata cewa masallacin zai ci gaba da kasancewa a rufe a ranakun Arafa da Idin Babbar Sallah saboda hana bazuwar cutar korona. Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruewaito shi yana cewa: Dakatar da sallah a cikin masallacin da harabarsa zai ci gaba da aiki. Mun shawarci mutanen garin Makkah da su karya azuminsu na Ranar Arfa a gaidajensu,'' in ji shi.Manjo Janar Al-Ahmadi ya yi wadannan jawabai ne a yayin wani taron manema labarai inda ya sanar da kammala matakin farko na tsara Aikin Hajjin bana. Ya ce tsarin tsaro na hajjin bana zai mayar da hankali ne kan tsaro da jin kai da batun lafiya.Mun mayar da hankali ne bana kan batun lafiya saboda y...
Yanzu-Yanzu: An kwantar da Sarki Salman na Saudiyya asibiti

Yanzu-Yanzu: An kwantar da Sarki Salman na Saudiyya asibiti

Siyasa
An kwantar da sarki Salman Bn Abdul'aziz na Saudiyya a wani asibitin Riyadh inda ake yi masa gwaje gwaje.   Bayanai sun ce Sarkin mai shekara 84 na fama ne da rashin lafiyar da ta shafi mafitsara. Da safiyar yau Litinin ne Kamfanin dillacin labaran Saudiya SPA ya ruwaito cewa an kwantar da Sarki Salman asibitin na Riyadh ba tare da wani cikakken bayani ba.   Tun 2015 Sarkin ke mulki a Saudiyya - kafin zamansa Sarki ya shafe shekara kusan biyu a matsayin Yarima mai jiran gado kuma ya taba rike mukamin mataimakin firimiya a 2012.   Ya kuma shafe sama da shekaru 50 a matsayin gwamnan Riyadh.   Labarin rashin lafiyar Sarki Salman Yanzu ya sa hankali ya karkata ga makomar Saudiyya musamman zamanin Muhammad Bin Salman, Yarima...
Saudiyya za ta daina aiwatar da hukuncin kisa kan kananan yara

Saudiyya za ta daina aiwatar da hukuncin kisa kan kananan yara

Siyasa
Saudiyya ta sanar da cewa daga yanzu ta daina yanke hukuncin kisa kan wadanda suka aikata laifuka yayin suna yara kanana.     Hukumar da ke kula da hakkin dan Adam ta kasar ce ta bayyana haka.     Sarki Salman ya sanya hannu kan dokar tabbatar da sanarwar wadda ta zo kwana biyu bayan da Sarkin ya hana yi wa masu laifi bulala a kasar.     Hukumar kula da hakkin yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya - wadda kasar Saudiyya mamba ce ta hukumar ta ce irin wannan hukunci bai kamata a rika yanke shi kan kananan yara ba.     Masu fafutukar kare hakkin bil Adama na cewa Saudiyya na cikin jerin kasashe masu gallaza wa al'ummarsu a duniya.     Sun ce ana matukar hana mutane fadan albarkacin bakinsu musamma...
Saudi Arabia ta bude Masallatan ta bayan tsaftace su daga coronavirus

Saudi Arabia ta bude Masallatan ta bayan tsaftace su daga coronavirus

Kiwon Lafiya
Hukumomin Saudi Arabia yau juma'a sun bude Masallatan da suka fi kima a Duniyar Musulmi wato Ka’abah dake Makkah da kuma Masallachin Annabi Muhammad (SAW) dake Madinah domin cigaba da gudanar da ibadah bayan rufe su da akayi jiya domin tsaftace su daga kamuwa da cutar coronavirus.   Saudiya ta hana masu ziyarar Umrah daga kasashe 25 da kuma baki yan yawon bude ido ganin yadda cutar corona ke cigaba da yaduwa a kasashen duniya.   Gwamnatin Saudi tace ‘yan kasashen Yankin tekun Fasha da suka yi tafiye tafiye zuwa wasu kasashen da basa yankin dole sai sun zauna a kasashen su na kwanaki 14 kafin su ziyarci Makkah.   Ya zuwa yanzu hukumomin Saudiyar sun sanar da samun mutane 5 da suke dauke da cutar.