fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Senegal

Mane ya taimakawa Senegal ta zama kasa ta farko data cancanci buga gasar cin kofin Nahiyar Africa

Mane ya taimakawa Senegal ta zama kasa ta farko data cancanci buga gasar cin kofin Nahiyar Africa

Wasanni
Dan Kwallon kafar kasar Senegal me bugawa kungiyar Liverpool wasa, Sadio Mane ya taimakawa kasarsa da kwallo wadda suka samu nasara akan Guinea Bissau da 2-0.   Da wannan nasara, Senegal ta samu kaiwa ga buga gasar Cin kofin Nahiyar Africa a 2022.   A mintuna 82 ne Mane ya saka kwallon data basu nasara wanda a yanzu suna da maki 12 kenan.  
Hotuna: Shugaba Buhari ya aike da tawaga kasar Senegal dan yiwa jama’ar kasar ta’aziyyar Khalifa Ahmad Tijjani Inyass

Hotuna: Shugaba Buhari ya aike da tawaga kasar Senegal dan yiwa jama’ar kasar ta’aziyyar Khalifa Ahmad Tijjani Inyass

Siyasa
Tawagar gwamnatin tarayya da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aika zuwa kasar Senegal bisa jagorancin shugaban kamfanin Mai na kasa, NNPC, Mele Kolo Kyari dan mika ta'aziyyar rasuwar shugaban tijjaniyya, Khalifa Khalifa Ahmad Tijjani Inyas ta isa kasar.   Tawagar wadda ta hada da shugaban hukumar kula da shigi da fici ta Immigration, Muhammad Babandede ta gana da shugaban kasar Senegal din, Macky Sall inda suka mika sakon ta'aziyyar shugaba, Muhammadu Buhari. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1291804114612101121?s=19
Senegal ta bude masallatai da coci-coci

Senegal ta bude masallatai da coci-coci

Uncategorized
Kasar Senegal ta sassauta dokar kulle ranar Talata inda aka bude masallatai da coci-coci. An dai kyale masallatai su bude domin yin sallolin goman karshe. Har wa yau, an kuma rage tsawon lokacin dokar hana zirga-zirga da awa biyu. Yayin wani jawabi ta talbijin din kasar ranar Litinin, Shugaba Macky Sall ya ce akwai bukatar 'yan Senegal sun san yadda za su kasnace tare da kwayar cutar korona. Sanarwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da da kasar ta samu mutum 177 masu duake da cutar a ranar Litinin. Jimilla Senegal na da mutum 1,886 da ke dauke da cutar korona inda mutum 19 suka mutu.
Sadio Mane na gina Asibiti a garinsu

Sadio Mane na gina Asibiti a garinsu

Wasanni
Tauraron dan kwallon kasar Senegal me bugawa kungiyar Liverpool ta kasar Ingila wasa, Sadio Mane na gina Asibiti a kauyensu na Bambali.   Mane a cikin wani bayani da yayi ya bayyana cewa tun yana dan karamin yaro mahaifinsa ya rasu, yace a lokacin da mahaifinshi bashi da lafiya saida aka je wani kauye sannan aka samu asibitin da za'a dubashi.   Mane ya kara da cewa, akwai kanwarshi da itama a gida aka haifeta saboda babu Asibiti a garinsu.   Mane yana gina wani Asibiti dan amfanuwar jama'ar garinsu wanda nan da watanni 6 ake sa ran kammalashi. Hakanan a baya ya ginawa garin nashi wata makaranta.   Mane ya bayar da gudummawar Fan Dubu 40 ga gwamnatin kasar Senegal dan yaki da Coronavirus/COVID-19.