fbpx
Friday, October 23
Shadow

Tag: Sergio Ramos

Sergio Ramos ya samu rauni yayin da Cadiz ta lallasa Real Madrid 1-0 a gidan ta

Sergio Ramos ya samu rauni yayin da Cadiz ta lallasa Real Madrid 1-0 a gidan ta

Wasanni
Zidane da tawagar sa sun sha kashi a gidan su a hannun kungiyar Cadiz wadda tayi nasarar cin kwallo guda a wasan tun kafin kafin aje hutun rabin lokaci, yayin da kuma wasan ya kasance karo na farko da kungiyar tayi nasarar cin wasa tsakanin tada Real Madrid a tarihin ta na shekaru 110. Kaftin din Real Madrid Segio Ramos ya samu rauni a gwiwar kafar shi ta hagu tun kafin aje hutun rabun lokaci kuma har aka dawo daga hutun bai dawo wasan ba wanda hakan yasa aka maye gurbin shi da Eder Miltiao. Real Madrid zata buga wasan Champions League da kungiyar Donetsk a gidan ta ranar laraba kuma zata ziyarci Barcelona ranar sati mai zuwa a gasar La Liga. Saboda haka da yiyuwar Sergio Ramos ya rasa wa'yan nan wasannin idan har raunin nshi mai tsanani ne yayin da kuma ya zamo dan wasan na 14 daya ...
Labaran kasuwar yan wasa: yayin da Juventus da PSG suke harin siyan Sergio Ramos

Labaran kasuwar yan wasa: yayin da Juventus da PSG suke harin siyan Sergio Ramos

Wasanni
Kaftin din Real Madrid Sergio Ramos ka iya komawa kungiyar zakarun kasar Italiya Juventus ko kuma zakarun League 1 Paris Sanit German yayin da shi kuma Paul Pogba da yiyuwar ya koma Barcelona. Ramos ya kasance a kungiyar Real Madrid tun shekara ta 2005 yayin da dan wasan Sifaniyan yayi nasarar lashe kofunan La Liga guda biyar da kuma Champioms League guda hudu da Copa Del Rey da dai sauran su. Kwantirakin dan wasan mai shekaru 34 zai kare ne a shekara mai zuwa wanda hakan yasa manyan kungiyoyin nahiyar guda biyu suke takarar siyan zakaran dan wasan duniyan. Mundo Deportivo sun bayyana cewa Barcelona zasu fara harin siyan yan wasan da kwantirakin zai kare saboda matsalar rashin kudin da kungiyar take fama da shi kuma dan wasan manchester United Pogba da dan wasan Munich David Alaba ...
Burin Real Madrid na wannan kakar shine ta lashe gabaya kofunan nahiyar turai>>Sergio Ramos

Burin Real Madrid na wannan kakar shine ta lashe gabaya kofunan nahiyar turai>>Sergio Ramos

Wasanni
Tauraron dan wasan Real Madrid na baya, Sergio Ramos ya shirya tsaff domin ya taimakawa Real Madrid ta kara lashe kofin La Liga bayan ta karbe kofin daga hannun Barcelona a kakar data gabata. Real Madrid zata fara buga wasan ta na wannan kakar ne ranar lahadi tsakanin ta da Real Sociedad. Sergio Ramos ya bayyana cewa yanzu sabon kaka ya gabato, bayan sun lashe kofin La Liga da Supercopa De Espana a kakar data gabata kuma zasu cigaba da yin kokari sosai a wannan kakar bayan da shirye shiryen da suke yi a filin su na Valdebebas duk da cewa shi yana tare da tawagar kasar shi ta Sifaniya. Dan wasan mai shekaru 34 da cewa tasri da kuma burin Real Madrid na wannan kakar shine ta lashe gabadaya kofunan nahiyar turai kuma zasu yi kokari sosai domin su fara buga wannan kakar da nasara.
Messi na da damar Barin Barcelona in yana son hakan>>Ramos

Messi na da damar Barin Barcelona in yana son hakan>>Ramos

Wasanni
Tauraron dan kwallon kungiyar Real Madrid,  Sergio Ramos ya bayyana cewa dan wasan Barcelona, Lionel Messi na da damar barin kungiyar idan yana son hakan.   Messi ya tadawa Barcelona hankali bayan da ya bayyana cewa yana son barinta biyo bayan cin gyada da Bayern Munich ta musu a wasan gasar Champions League 8-2. Ramos da yake magana da manema labarai ya bayyana cewa, Messi na da damar barin Barcelona idan yana son hakan amma maganar gaskiya zaibso ya tsaya saboda yana haskaka gasar La Liga da kungiyarsa kuma shima yana son wasa da gwani.
Sergio Ramos zai iya cigaba da buga wasan kwallon kafa har ya kai shekaru 40>>Rafeal Van Der Vaart

Sergio Ramos zai iya cigaba da buga wasan kwallon kafa har ya kai shekaru 40>>Rafeal Van Der Vaart

Wasanni
Sergio Ramos shine gwarzon yan wasan baya na duniya kuma zai iya cigaba da buga wasa har sai ya kai shekaru 40 a cewar tsohon abokin aikin shi Rafeal Van Der Vaart. Ramos ya taka muhimmiyar rawa wurin dakatar da Barcelona a wannan kakar, yayin da yace kwallaye 11 kuma suka lashe kofin La Liga. Madrid sun siyo Ramos yana matashi daga Sevilla a shekara ta 2005, kuma yana matashin yayi aiki tare da Van Der Vaart wanda yayi shekaru biyu a Madrid kafin ya koma tottenham a 2010. Rafeal yaga yadda tsohuwar kungiyar tashi ta kara lashe La Liga kuma yaga yadda Ramos yayi kokari sosai wurin lashe kofin. Hakan ne yasa Van Der Vaart yake tunanin bai ga wani dalilin da zai sa Ramso ya fara tunanin yin ritaya ba a yanzu, yayin daya bayyana manema lanarai cewa a ganin shi Sergio Ramos shine gwa...
Sergio Ramos ya bugawa Real Madrid wasanni 450

Sergio Ramos ya bugawa Real Madrid wasanni 450

Wasanni
Tauraron dan kwallon kungiyar Real Madrid,  Sergio Ramos ya bugawa kungiyar tasa wasannin La liga 450.   Ramos ya bugawa na 450 ne a jiya a karawarsu da Getafe wanda shine ma yaciwa kungiyar kwallo 1 tilo ta hanyar bugun daga kai sai gola wadda ta bata damar ci gaba da rike matsayinta na 1 a saman teburin La liga da tazarar maki 4 tsakninta da Barcelona. https://www.instagram.com/p/CCKIhCao-Lc/?igshid=1poq0g88d7ycl Kungiyar ta yi murnar wannan nasara da Ramos ya samu inda ta saka hotonshi shinda shugaban Kungiyar, Florentino Perez suna rike da riga me dauke da 450.
Sergio Ramos ya kafa sabon tarihi a gasar La Liga yayin da ya samu rauni bayan sun tashi wasan jiya

Sergio Ramos ya kafa sabon tarihi a gasar La Liga yayin da ya samu rauni bayan sun tashi wasan jiya

Wasanni
Kwallon da Sergio Ramos yaci wadda tasa Madrid suka kasance 1-0 ta zamo tarihi a gareshi yayin daya kasance dan wasan baya daya fi cin kwallaye masu yawa a gasar La Liga, daga baya kuma Banzema da Mikel suka ci kwallayen nasu wanda suka as aka tashi wasan 2-1. Ramos ya kafa tarihi a wasannin gasar La Liga kuma ya kerewa tsohon tauraron Barcelona Ronald Koeman, yayin da kwallayen shi suka kai 68 a gabadaya wasannin daya buga. Dan wasan mai shekaru 34 ya samu rauni a gwiwar shi bayan an tashi wasan, kuma kyamarar talabijin ta dauko hotunan shi yayin da aka sa mai kankara a gwiwar tashi.