fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Sheikh Abduljabbar Kabara

Da Duminsa:Sheikh Abduljabbar Kabara ya tuba

Da Duminsa:Sheikh Abduljabbar Kabara ya tuba

Uncategorized
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwar waɗanda suka "fahimci cewa shi ne ya ƙiƙiiri kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu SAW" da ake zarginsa da yi. Cikin wani saƙon sauti da ya fitar a ranar Lahadi, an ji malamin na cewa "idan har waɗannan kalamai daga ni suke, ƙirƙirarsu na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni na gaggauta tuba". Ya ƙara da cewa: "Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin waɗancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi roƙon Allah ya haska wa al'umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan ƙarya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su." Cikin wata hira da BBC, Abduljabbar ya jaddada cewa yana neman afuwar waɗanda suke ganin kalaman da ake cewa y...
Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka Gwamna Ganduje a kotu kan hanashi wa’azi

Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka Gwamna Ganduje a kotu kan hanashi wa’azi

Siyasa
Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a kotu saboda take masa hakkinsa na dan kasa na gudanar da addininsa.   Ya muka kai karar babbar kotun tarayya inda yake neman ta dskatar da kwamishinan 'yansandan jihar da sauran hukumomi daga cin zarafinsa da hanashi rawar gaban hanshi akan addininsa.   Wakilin wanda ake kara, Rabiu Abdullahi ya bayyana cewa, an takewa Sheikh Abduljabbar Kabara hakkinsa na zama dan kasa da yin addinin da ya zaba.   Kotun ta dage ci gaba da sauraren karar har sai zuwa 18 ga watan Fabrairu.  
Nafi Sheikh Abduljabbar Kabara Ilimi, bai kamata malamai su zauna dashi ba>>Nazir Ahmad Sarkin Waka

Nafi Sheikh Abduljabbar Kabara Ilimi, bai kamata malamai su zauna dashi ba>>Nazir Ahmad Sarkin Waka

Nishaɗi, Uncategorized
Tauraron fina-finan Hausa,  Nazir Ahmad Sarkin Waka ya bayyana cewa ya fi Sheikh Abduljabbar Kabara Ilimi.   Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda yake martani ga mabiya Malamin da suke caccakarsa kan njna fushi da kalaman da aka zargi Malamin da yi.   Sarkin Waka ya bayyana cewa malamai bai kamata su zauna da Sheikh Abduljabbar Kabara ba saboda Soki Burutsu kawai zai ta musu ba Hujjar Hadisi da aya zai kawo ba.   https://www.instagram.com/tv/CLBZReCJnT6/?igshid=26b6vfsr3n0v  
Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya goyi bayan Gwamna Ganduje kan dakatar da Sheikh Abduljabbar daga yin wa’azi a Jihar

Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya goyi bayan Gwamna Ganduje kan dakatar da Sheikh Abduljabbar daga yin wa’azi a Jihar

Siyasa
Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya yaba wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje kan hana fitaccen malamin nan, Sheikh Abdujjabar Nasiru-Kabara yin wa'azi a jihar. A ranar laraba da ta gaba ne, Gwamna Ganduje ya hana Malam Abduljabbar Nasiru-Kabara yin wa'azi a jihar, inda ya bada umarnin rufe masallacin sa, wanda ke karamar hukumar Gwale a cikin garin Kano. An bayar da umarnin ne biyo bayan korafe-korafen da ake yi cewa mai wa'azin yana zagin sahabban Annabi Muhammad (S.A.W) a cikin tafsirinsa na addini. Tsohon Sarkin ya yi wannan yabo ne lokacin da yake gabatar da lacca daga Oxford, UK, yana mai cewa shawarar da gwamnatin jihar ta yi na hana Mista Nasiru-Kabara abin a yaba ne kuma ya kamata a goyi bayansa. A cewarsa, Musulmai a Kano masu bin tafarkin "Ahlussuna w...
Gwamnatin Jihar Kano ta Amince zata shirya Mahawara tsakanin Abduljabbar da Sauran Malamai

Gwamnatin Jihar Kano ta Amince zata shirya Mahawara tsakanin Abduljabbar da Sauran Malamai

Uncategorized
A karshe Gwamntin Jihar Kano Karkashin Jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje  ta amince zata shirya wata muharawa ta musamman tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malamai da ke jihar.   Sai dai Gwamntin jihar bata bayyana ranar da ta ware ba domin gudanar da Mahawarar.   Ana tsammaninn Gwamnatin jihar zata sanar da ranar nan ba da dadewa ba. Hutudole ya fahimci a sanarwar da kakakin gwamnan, Abba Anwar ya fitar, yace gwamnatin jihar Kanon ce zata shirya wannan muhawara.   Ya bayyana malaman da za'a shirya wannan mahawara dasu kamar su Malam Salihu Sagir Takai, Ali Haruna Makoda, Dr. Muhammad Tahar Adam, da sauransu.   A baya, Hutudole.com ya kawo muku yanda gwamnatin jihar Kano ta kulle masallacin Sheikh Abduljabbar Kabara da kum...
Gwamnatin Kano ta rusa makarantar Malam Abduljabbar

Gwamnatin Kano ta rusa makarantar Malam Abduljabbar

Siyasa
Gwamnatin Kano ta rushe inda Malam Abduljabbar Nasir Kabara ke bayar da karatu kusa da Jauful Fara, da ke filin mushe. An ɗauki lokaci ana rikici kan filin tsakanin malamin da mutane, sai dai shehin malamin ya yi iƙirarin cewa gwamnati ce ta mallaka masa shi. Cikin wata hira da wakilin BBC a Kano, Abduljabbar ya ce gwamnatin Kano ce ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso a wa'adinsa na ƙarshe - 2011 zuwa 2015 - ta mallaka masa filin. "Tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ne ya kira ni da kansa ya shaida mani cewa an ba ni filin amma sai dai har gwamnatin ta sauka ba a ba ni takardar mallakarsa ba," in ji Sheikh Abduljabbar. Sai dai gwamnatin kano ta yanzu ta ƙwace filin ne sakamakon koke da ta ce ta samu daga mutanen yankin, kan cewa filin mallakinsu ne. Kimanin wata biyu kenan ...
Gwamnatin jihar Kano ta maka Sheikh Abduljabbar Kabara a kotu

Gwamnatin jihar Kano ta maka Sheikh Abduljabbar Kabara a kotu

Uncategorized
Gwamnatin jihar Kano ta maka Sheikh Abduljabbar Kabara a kotu dan ganin an tabbatar da hukuncin da majaisar koli ta jihar ta dauka akansa.   Majalisar Koli ta jihar ta haramtawa Sheikh Abduljabbar Kabara wa'azi da kuma kulle masallacinsa da kuma hana shirye-shiryen da yake a kafafen Rediyo da na sada zumunta dan isar da sako.   Hadimin gwamnan,  Abubakar Aminu Ibrahim ta tabbatar da kai karar. Kuma an dakatar da Sheikh Abduljabbar Kabara daga dukkan wasu ayyukan wa'azi har sai an kammala bicike.   A jiya dai da yake mayar da martani kan wannan matakin, Sheikh Abduljabbar ya bayyana cewa, siyasa ce tasa aka dauki matakin akansa ba Addini ba, saboda ya nuna rashin goyon baya ga gwamna Ganduje a shekarar 2019.   https://m.facebook.com/story.php?stor...
Sheikh Abduljabbar Kabara ya bayyana dalilin da yasa Gwamna Ganduje ya hanashi wa’azi

Sheikh Abduljabbar Kabara ya bayyana dalilin da yasa Gwamna Ganduje ya hanashi wa’azi

Uncategorized
Sheikh Abduljabbar Kabara yayi zargin cewa gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya hanashi wa'azi ne saboda ya nemi kada a sake zabensa a zaben shelarar 2019.   An yi zabe me zafi sosai tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Dan takarar APC, Abba Kabir Yusuf.   A zantawarsa da Daily Trust,  Sheikh Abduljabbar Kabara ya bayyanawa cewa wannan mataki da gwamnatin Kano ta dauka na Siyasa ne bai shafi Addini ba.   Ya bayyana cewa dalilin wannan mataki a bayyane yake, saboda wanda ya dauki wannan mataki, mutum ne da yace baya yafiya, kuma ya kalubalanceshi a zaben 2019 inda shima ya sha Alwashin sai ya rama.   Da yake magana akan ko zai yiwa wannan doka biyayya, Sheikh Abduljabbar Kabara ya bayyana cewa shi dama me bin doka ne kuma yana ki...
Gwamnatin Kano ta Haramtawa Sheikh Abduljabbar Kabara Wa’azi

Gwamnatin Kano ta Haramtawa Sheikh Abduljabbar Kabara Wa’azi

Uncategorized
Majalisar zartarwar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa fitaccen malamin addinin Islama na jihar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa'azi a dukkanin faɗin jihar nan take. Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammadu Garba ne ya tabbatar da hakan ga BBC. Ya ce an tattauna batun yayin zaman majalisar na ranar Laraba bayan wasu rahotanni da ke nuna cewa malamin na yin kalaman da ka iya haifar da fitina a jihar. ''Gwamnati ta tsaya ta yi nazari, kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, har akwai rahotanni daga wajen manyan malamai da kuma hukumomin tsaro, dalilin da ya sa jami'an tsaro suka sanya kwamiti na musamman don duba irin waɗannan kamalamai da malamin ke yi'' a cewarsa. Ya ce sakamakon t...
Cikin Kaso 100, Shi’a tafi Sunnah gaskiya da kaso 75, shiyasa idan an ce min dan Shi’a bana musantawa>>Sheikh Abduljabbar Kabara

Cikin Kaso 100, Shi’a tafi Sunnah gaskiya da kaso 75, shiyasa idan an ce min dan Shi’a bana musantawa>>Sheikh Abduljabbar Kabara

Uncategorized
Wasu da dama na kallon malamin a matsayin mai bin mazahbar Shi'a, sai dai ya ce tuni ya daina musanta cewa shi ba ɗan shi'a ba ne. Ya ce bai ga dalilin da zai sa a dinga tsorata shi da cewa Shi'a ba aba ce mai kyau ba, inda ya ce a da idan aka tambaye shi yana cewa shi ba ɗan shi'a ba ne, ''amma a yanzu bayan da na yi bincike mai zurfi sai na gane ashe Shi'ar ma ta fi Sunnar hujjoji, sai na ga ba wani dalilin da za a dinga tsorata ni da wannan.''   ''Duk wanda ya tambaye ni ko ni ɗan shi'a ne, sai na ce masa mece ce Shi'a a gurinka? Duk amsar da ya ba ni ita ce za ta biyo bayan amsar da zan ba shi.   ''Idan ya ce zagin Sahabbai zan ce masa a ina na zage su har ka nasabta ni da shi'a? Sai ka ga babu amsa. Ni dai make-maken nan ne ba zan yi ba don ni ina ...