fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana sirrin haddar Alkur’ani

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana sirrin haddar Alkur’ani

Ilimi
A hirar da aka yi da Shehin Malamin Addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayana sirrin Haddar Alkur'ani.   Yace ana samun yara masu shekaru 7 wasu ma da shekaru 5 suna haddace Alkur'ani.   Ga hirar da BBCHausa ta yi dashi Kamar haka:   Gaskiya ne da farko muna da asiri na Alkurani da iyayenmu suka samu a Borno wajen Bare-Bari, da shi muke amfani wajen haddar Alkur'ani. "Daga bisani lokacin da Sheikh Ibrahim Inyass ya bayyana ya ce ya roki Allah ya ba shi karamar haddar Alkur'ani, sai ya zama shi kenan an huta da nemo maganin karatun Alkur'ani Shehu ya riga ya roki Allah mutane su haddace Alkurani cikin sauki," in ji shi. ''Za ka samu yaro mai shekara bakwai ya hadadce Alkur'ani, har mai shekara biyar ma ya haddace Alkur'ani,'' in ...
Kada ku bar Kidnapping ku shiga Izala saboda ta fi Kidnapping Muni, Basa son Annabi(SAW)>>Sheikh Dahiru Bauchi ga Fulani

Kada ku bar Kidnapping ku shiga Izala saboda ta fi Kidnapping Muni, Basa son Annabi(SAW)>>Sheikh Dahiru Bauchi ga Fulani

Uncategorized
Shehin malamin addinin Islama, sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa Fulani su bar garkuwa da mutane da Fashi.   Yace amma fa kada wani ya yaudaresu, su bar Garkuwa da mutanen su shiga Izala, yace saboda Izala ta fi Garkuwa da mutane muni saboda ita basa son Annabi.   Hakan ya bayyana ne a wata hira da aka yi da shehin Malamin wadda ta rika yawo a shafukan sada zumuna.   Sheikh Dahiru Bauchi yace shiga Izala idan suka bar Kidnapping kamar tsallen Badakene, ko kuma su fita daga Tabo su shiga kashi.
Akwai kamanceceniyar halayya tsakanin Tinubu da Sheikh Dahiru Bauchi>>Inji Kungiyar ANEST dake kokarin ganin Tinubu ya zama shugaban kasa

Akwai kamanceceniyar halayya tsakanin Tinubu da Sheikh Dahiru Bauchi>>Inji Kungiyar ANEST dake kokarin ganin Tinubu ya zama shugaban kasa

Siyasa
Kungiyar ANEST dake kokarin ganin Tinubu ya zama shugaban kasa ta bayyana cewa akwai kamanceceniyar halayya tsakanin Tinubu da Shehin malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi.   Shigaban kungiyar, Musa Usman ya bayyana cewa shuwagabannin 2 na da kamancece niyar hallaya wajan jagoranci da kuma Karfafa zaman lafiya.   Ya bayyana hakane a Abuja, Yau Lahadi a wajan da ake kaddamar da kundin Tarihin Shekih Dahiru Bauchi me suna Lisanul Faidha. Kungiyar ta ANEST da Blue Bells ne suka shirya wannan gagarumin aiki.   Yacw sun yanke shawarar yin kundin tarihin Sheikh Dahiru Bauchi ne saboda yanda yake da kamanceceniyar hallaya da me gidansu, Bola Ahmad Tinubu wajan jagoranci da kuma taimakawa Al'umma, kamar yanda peoplesgazette ta bayyana.   Shima a n...
Za Mu Dauki Mataki Kan Hana Mu Karatun Allo Da Kuka Yi>>Martanin Sheikh Dahiru Bauchi Ga Gwamnonin Arewa

Za Mu Dauki Mataki Kan Hana Mu Karatun Allo Da Kuka Yi>>Martanin Sheikh Dahiru Bauchi Ga Gwamnonin Arewa

Siyasa
Shahararren Malamin addinin islama kuma shugaban darikar Tijjaniya, Sheik Dahiru Usman Bauchi, a zantawarsa da manema labarai, ya ce za su dauki mataki akan dukkanin gwamnonin da suka hana su yin karatun Allo a Jihohin su. Idan baku manta ba, a kwanakin baya gamayyar gwamnonin yankin Arewa, sun haramta makarantun allo tare da harmta barace-barace wanda har suka dinga diban almajiran Jihohin su, suna mai dasu garuruwan su na asali.   Haka zalike ya yiwa gwamnatin jihar Kaduna martani, kan amincewa da dokar yin dandaka ga duk mutumin da aka kama da laifin yin fyade, inda Mallam ya ce babu irin wannan hukuncin kwata-kwata a cikin shari'ar Musulunci.
General BMB ya kaiwa Sheikh Dahiru Bauchi ziyara

General BMB ya kaiwa Sheikh Dahiru Bauchi ziyara

Nishaɗi, Uncategorized
Tauraron mawakin Hausa, Bello Muhammad Bello wanda aka fi sani da General BMB ya kaiwa shehin Malamin addinin Islama,  Sheikh Dahiru Usman Bauchi ziyara.   A sakon da ya saka a shafinsa na sada zumunta, BMB ya bayyana cewa ya kai ziyara gidan malam kuma an karbeshi hannu biyu-biyu inda ma har aka masa addu'a. https://www.instagram.com/p/CFFl-zgpUz9/?igshid=11qj45u979glf
Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Almajiranci A Nijeriya, Cewar Sheikh Dahiru Bauchi

Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Almajiranci A Nijeriya, Cewar Sheikh Dahiru Bauchi

Uncategorized
Shararren Shehin Malami, Shiekh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana rashin amincewar sa da gwamnonin Arewa bisa kokarin hana almajiranci da suke yi.   A hirar da jaridar The Sun tayi da shi, Sheikh Dahiru ya ce ana kokarin takewa mutanen da sukayi imani da shirin almajiranci hakkinsu kuma yana daya daga ciki. Shehi ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ta baiwa kowani dan kasa daman zuwa inda yaga dama domin yin addinin da yaga dama.   Yace: "Kundin tsarin mulkin kasa ta bamu yancin yin addininmu duk yadda muka ga dama. Abinda mukafi girmamawa a addini shine AlKur'ani.   Tun da addini ta basu dokokin da za'a bi amma suka ki biyayya, shin wani hakki suke da shi na baiwa Alkur'ani umurni? saboda haka, ba zamu yarda da haramta Almajiranci da gwamnonin Arewa s...
Zamu kada ku zabe saboda hana Almajirci>>Sheikh Dahiru Bauchi da Malaman makarantun Allo ga Gwamnoni

Zamu kada ku zabe saboda hana Almajirci>>Sheikh Dahiru Bauchi da Malaman makarantun Allo ga Gwamnoni

Siyasa
Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya Shaik Dahiru Bauchi da malaman makarantun allo sun yi barazanar daukar mataki kan gwamnonin da suka hana almajirci a jihohinsu. Martanin malaman ga dokar hana karatun almajirci da gwamnonin suka yi, ya ce za su kayar da gwamnonin a zabe kuma almajirai na da ‘yancin yin addini da neman ilimi a duk inda suke so a Najeriya. “Almajirai da alarammomi na da ‘yancinsu a matsayin ‘yan Najeriya su yi addini, su kuma zauna a inda suke so kuma ba za mu lamunci duk salon tauye mana hakki da sunan dokar hana almajirci ba, ana dibar almajirai daga wata jiha zuwa wata kamar dabbobi”, inji Shaikh Dahiru. Sanarwar tasu na zuwa ne bayan gwamnonin Arewacin Najeriya sun haramta tsarin karantun da kuma bara, tare da mayar da almajiran gaban iyayensu ...
‘Yansandan farin kaya sun gano jikan Sheikh Dahiru Bauchi da aka yi garkuwa dashi da kuma kudin fansar da aka biya

‘Yansandan farin kaya sun gano jikan Sheikh Dahiru Bauchi da aka yi garkuwa dashi da kuma kudin fansar da aka biya

Tsaro
'Yansandan farin kaya na DSS sun bayyana cewa sun gano jikan shehin malamin addinin Islama, Dahiru Usman Bauchi me kimanin shekaru 3 da wani Umar Ahmad yayi garkuwa dashi.   An dai sace jikan malam din a ranar Sallah 22 ga watan Mayu.   An gano Umar me kimanin shekaru 27 da yaron daya sata a Kano, a Otal din Liberty daki me lamba 37 dake Sabon Gari. Daraktan DSS na Kano,Muhammad Alhassan ya bayyana cewa kwamishinan 'yansandan Kano, Mr. Habu Sanine ya labarta musu maganar garkuwa da yaron.   Umar ya bukaci a bashi kudin fansa har Miliyan 10 inda daga baya aka tattauna ya komo Miliyan 6, har an tura mai Miliyan 2.5 a wani asusun Ajiyar Banki amma daga baya sai aka ganoshi.   Alhassan yace duka Yaron da kuma wanda ya saceshi suna cikin koshin...
Sarki Sanusi zai iya dawowa kan sarautarsa>>Sheikh Usman Dahiru Bauchi

Sarki Sanusi zai iya dawowa kan sarautarsa>>Sheikh Usman Dahiru Bauchi

Siyasa
Sheikh Dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin manyan malaman da suka sha yi magana kan rikice-rikicen da suka yi ta faruwa a tsakanin tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ce in Allah Ya ga dama zai iya dawo da tubabben Sarkin kan sarautarsa:     Me Shehi zai ce kan tube Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Gwamnatin Jihar Kano tayi?   Duk abin da mutane suke nufi ba abin da zai zartu sai wanda Allah Yake nufi ya zartu. Ainihin shi Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya gaji kakansa cikin samun sarautar Kano kuma ya gaji kakansa a cikin fita daga sarautar. Allah shi Ya shigar da shi sarautar Allah kuma ne Ya karbi sarautar. Kafin wani lokacin in Ya ga dama sai Ya maida shi kan sarautarsa. Allah Yana da ik...