
Malamai sun ci abinci sun koshi, ana ta kashe mutane sun kasa magana>>Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun
Shehin Malamin Addinin Islama, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya bayyana bacin ransa kan yanda ake ta kashe mutane a Arewa amma malamai sun kasa magana.
Malamin yayi wannan maganane a wani faifan bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta inda aka jishi yana cewa.
Malamai sun ci sun koshi, suna kusa da gwamnati ana ta kashe mutane amma sun kasa magana.
Ya kara da cewa amma a daa da an yi abu kadan zaka jisu sun fito suna ta tsinuwa da Alqunut.