
‘Yan Shi’a sun koka kan rashin lafiyar Zakzaky da matarsa inda suka bukaci gwamnati ta sakesu
Kungiyar IMN da aka fi sani da Shi'a ta bayyana damuwa kan rashin lafiyar dake damun shugabanta, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenat.
A wata sanarwa da kakakin kungiyar Abdullahi Muhammad Musa ya fitar yace ko kadan yanda ake tsare da Zakzaky da matarsa bai dace ba.
Yace yace akwai harsashi har yanzu a jikinsa sannan kuma Likitoci sun zo daga kasar India dan dubashi amma aka hanasu ganinshi. Sannan matarsa ma tana fama da wasu ciwuka dake bukatar kulawa dan hakane suke ganin ci gaba da rike Zakzaky kamar akwai wata Manufa da gwamnati ke son cimmawa.
Yace suna neman a saki zakzaky da matarsa ba tare da bata lokaci ba.