fbpx
Monday, August 8
Shadow

Tag: Shugaba Buhari

Dalilin da yasa Buhari bai kori shugabannin tsaro ba>>Garba Shehu Yayi Bayani Dalla-Dalla

Dalilin da yasa Buhari bai kori shugabannin tsaro ba>>Garba Shehu Yayi Bayani Dalla-Dalla

Uncategorized
A cewar Shehu, shugaban na da hurumin nadawa ko kuma sallamar kowane daga cikin shugabanin hafsosin tsaron na kasar, inda ya kara da cewa shugaban yana rike da shugabannin rundunonin ne matukar dai ya gamsu da ayyukan su. Mummunan kisan manoman shinkafa akalla 43 a Zabarmari da ke cikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Barno a ranar Asabar da ta gabata ya haifar da sabon kira ga korar shugabannin tsaron. Dangane da kiran da ‘yan Najeriya da dama suka yi, wadanda kuma ke son shugaban ya sauya fasalin tsarin tsaron kasar, Shehu ya ce shawarar korar ko rike kowane shugaban hafsoshin gaba daya na ga shugaban ne. Yayi magana ne a daren Litinin a wata hira da gidan talabijin na Arise TV wanda jaridar The PUNCH ke lura dashi. Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, “Ni ban sani...
Hotuna:Shugaba Buhari ya gana da gwamnan Ondo

Hotuna:Shugaba Buhari ya gana da gwamnan Ondo

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya gana da gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a fadarshi ta villa dake babban birnin tarayya, Abuja.   Ganawar tasu ta kasance a yau,Talata, kamar yanda sanarwa ta fito daga fadar. Gwamna Akeredolu ya je nunawa shugaba Buhari fom din sake tsayawa takarar gwamnan jihar sa ne a zango na 2. https://twitter.com/NigeriaGov/status/1272867963641696256?s=19 An ga shugaban kasar da gwamnan rike da Fom din ana daukarsu hotuna.
Shugaba Buhari bai soke wasu ayyukan Abba Kyari ba>>Fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari bai soke wasu ayyukan Abba Kyari ba>>Fadar shugaban kasa

Siyasa
Fadar shugaban kasa ta karyata Labarin dake yawo cewa shugaba Buhari ya saka sabon shugaban ma'aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari ya soke wasu ayyukan da marigayi, Abba Kyari yayi bada Umarninsa ba.   Jaridar Guardian ta ruwaito cewa shugaba Buhari ya saka Gambari soke ayyuka 150 wanda tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar,  Abba Kyari yayi ba tare da umarnin shugaban kasar ba. Saidai a Sanarwar da Me magana da yawun shugaban kasar,Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa ba gaskiya bane wancan Rahoto.   Yace a watan Fabrairu an shekarar 2019 'yan Najeriya suka zabi shugaba Buhari ya wakilcesu a matsayin shugaba kuma ba zai taba baiwa wani wannan damar shugabancin ba.
Ka canja Halin baiwa Tsaffi mukami, Ka rika nada matasa>>Kungiyar Daliban Najeriya ga shugaba Buhari

Ka canja Halin baiwa Tsaffi mukami, Ka rika nada matasa>>Kungiyar Daliban Najeriya ga shugaba Buhari

Siyasa
Kungiyar daliban Najeriya, NAN ta yaba da nadin da shugaban kasa,Muhammadu Buhari yawa Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin shugaban ma'aikatan fadar sa.   NAN ta taya Farfesa Gambari murna saidai ta bayyana cewa akwai bujatar shugaba Buhari ya rika duba matasa wajan bayar da mukamai. A sanarwar data fitar ta hannun shugabanta, Azeez Adeyemi, NAN ta kara da cewa ya kamata shugaba Buhari ya canja halinsa na nada tsaffi kawai a cikin gwamnatinsa ya rika duba matasa.   Sanarwar ta kara da cewa akwai matasa a ciki da wajen Najeriya da suka yi zarra a ayyukansu na taimakawa Al'umma da kawo ci gaba kuma idan shugana Buhari ya baiwa daya daga cikinsu mukami ba zasu bashi kunya ba.
Munawa shugaba Buhari matukar biyayya>>Shugaban Sojin Sama

Munawa shugaba Buhari matukar biyayya>>Shugaban Sojin Sama

Tsaro
Shugaban sojojin Sama na Najeriya, Air Vice Marshal Sadiq Abubakar ya jaddada biyayyar sojojin saman ga shugaban kasa,Muhammadu Buhari.   Ya bayyana hakane a wani taron bikin Sallah na shekara-shekara da aka shirya a Barikin sojan dake Yola. Da yake magana ta bakin wakilunsa,Air Commodore Muhammad Yusuf, Shugaban sojin ya bayyana cewa suna nunawa shugaba Buhari biyayya musamman saboda goyon bayan da yake basu.   Ya kara da cewa suna shirya wannan bikin cin abinci ne duk Sallah dan su taya sojojin dake bakin daga a Yankin Arewa maso gabas Murnar Sallah.   Ya tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa zasu samu tsaro da zai basu ci gaba da al'amuransu na yau da kullun.
Dama can na san Buhari ba zai taba iya gyara ko daya daga cikin Matsalolin Najeriya ba>>Alhaji Tanko Yakasai

Dama can na san Buhari ba zai taba iya gyara ko daya daga cikin Matsalolin Najeriya ba>>Alhaji Tanko Yakasai

Uncategorized
Uban kasa kuma me fada aji a jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa shi dama can bai tana goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.   Ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi ta hanyar sadarwar zamani wadda ya samu halarta. Yace tun lokacin shugaba Buhari na yakin neman zabe dama shi be goyi bayanshi ba saboda yasan cewa ba zai iya aikinba.   Yace to yanzu gashi shekaru 5 yana akn Mulki amma har yanzu Shiru babu wani bayani.   Yace abu daya yayi tsammani a mulkin Buhari, Watakila ya gyara wutar lantarki ta yanda masana'antun Kano zasu tashi mutane su samu aiki, hakanan a Enugu da Legas amma bai yiyuba.
Sarkin Ilori ya yi wa Buhari godiyar nadin Gambari, dan jihar shugaban ma’aikatansa

Sarkin Ilori ya yi wa Buhari godiyar nadin Gambari, dan jihar shugaban ma’aikatansa

Siyasa
Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, ya yi godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.     A wata sanarwa da mai ba shi shawara a kan harkokin yada labarai, Mallam Abdulazeez Arowona, ya sanyawa hannu, Sarkin ya ce nadin wata karramawa ce gagaruma ga daukacin al’ummar Masarautar Ilori.     Sai dai kuma har yanzu Fadar Shugaban Kasar ba ta tabbatar da nadin Farfesa Gambari ba.   Mashawartan shugaban kasar a kan al’amuran yada labarai da ma jami’an ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya sun ki su ce uffan a kan lamarin.     Sai dai sun bukaci manema labaran da suka tuntube su da su jira sanarwa a hukumance.   zai gaj...
SUNAYE: Jakadu 42 da Buhari ya aika majalisa don amincewa da zabin su

SUNAYE: Jakadu 42 da Buhari ya aika majalisa don amincewa da zabin su

Siyasa
Shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya karanta wasikar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Zauren majalisar Dattijai ranar Talata.     A wasikar Buhari ya roki majalisar ta amince da sunayen jakadu 42 da yake so ya nada a kasashen duniya.     Ga sunayen su C. O Nwachukwu (Abia), A. Kefas (Adamawa), R. U Brown (Akwa Ibom), G. A, Odidibo (Anambra), O. C Onowu (Anambra), Y. S Sulieman (Bauchi), E. S Agbana (Bayelsa), B. B.M Okoyen (Bayelsa), G. M Okoko (Benue), A. M Garba (Borno), M. I Bashir (Borno).     Others are, M. O Abang (Cross River), A. E Alote (Cross River), G. E Edokpa (Edo), A. M Maduwike (Enugu), Adamu Lamua (Gombe), Innocent Iwejuo (Imo), A. S Abubakar (Jigawa), Y. A Ahmed (Jigawa), S. D Umar (Kaduna), A. A Sule (Kano...
Shugaba Buhari ya nada, Ibrahim Gambari sabon shugaban ma’aikatansa

Shugaba Buhari ya nada, Ibrahim Gambari sabon shugaban ma’aikatansa

Siyasa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon ministan ayyukan harkokin waje Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa.     Gambari mai shekaru 75, ya rike mukamai da dama a kasa Najeriya da waje da majalisar dinkin duniya.     Gambari zai maye gurbin marigayi Abba Kyari da Allah yayi wa rasuwa a dalilin fama da yayi da Coronavirus.     Sarkin Ilori, Ibrahim Sulu-Gambari, ya aika da sakon godiya ta musamman ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari, bisa wannan nadi da yayi wa Ibrahim Gambari sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.     A wasikar, Maimartaba Ibrahim Sulu-Gambari, ya ce wannan abu basu aka yi wa ba kawai, an karrama jihar ne gaba daya.