fbpx
Monday, August 3
Shadow

Tag: Shugaban kasa

Marigayi Isa Funtua ya taimakawa Gwamnati na>>Shugaba Buhari

Marigayi Isa Funtua ya taimakawa Gwamnati na>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana amininsa, Marigayi, Isa Funtua a matsayin mutumin kirki wanda ya taimaka wajan karfafa gwamnatinsa.   Shugaban kasar ya bayyana hakane a takardar da ya aikewa iyalan mamacin da aka rubutata da Hausa wadda shi da kanshi shugaba Buhati ya sa mata hannu, kamar yanda me magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya bayyana. Yace shugaban ya gayawa iyalan na marigayin cewa rashin ba nasu bane su kadai amma gaba daya Najeriya ce ta yi rashi.   Yace shugaban kasar ya kuma bayyana marigarin a matsayin mutum me saukin kai, dan Jarida, Dan Kwangila wanda ya gina gine-ginen gwamnati da dama a Abuja.
Ka hukunta wanda suka ci amanar aikin da aka basu>>PDP ta gayawa shugaba Buhari

Ka hukunta wanda suka ci amanar aikin da aka basu>>PDP ta gayawa shugaba Buhari

Siyasa
Jam'iyyar Hamayya ta PDP ta bayyana cewa maganar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta tabbatar da abinda ta dade tana fada cewa akwai barayin dukiyar talakawa a APC.   Tace kuma gwamnati na baiwa wadannan barayi kariya ta yanda ba'a iya hukuntasu. Saidai PDP tace tana kira ga shugaban kasar da yayi himma wajan hukunta wadannan maciya amanar. Sakataren watsa labaran jam'iyyar,  Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace a baya PDP ta samar da hukumomin yaki da rashawa da cin hanci kuma ta hukunta wadan da aka kama da laifi.
A karin farko shugaba Buhari bai yi Sallah a gida ba, Daurawa sunce sun yi rashinshi

A karin farko shugaba Buhari bai yi Sallah a gida ba, Daurawa sunce sun yi rashinshi

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a wannan sallar Layya da aka yi yayi ta a fadarshi ta Villa dake banban Birnin tarayya, Abuja saboda zuwan cutar Coronavirus/COVID-19.   A baya shugaba Buhari tun bayan da ya hau mulki a shekarar 2015 a Daura yake yin Sallah inda jama'a ke masa Rakiya zuwa Masallaci sannan su mai rakiya zuwa gida idan ya kammala sallah. Da yake jawabi a lokacin Sallar bana, Sarkin Daura, Me martaba,  Umar Farouk ya bayyana cewa sun yi kewar dan nasu.
Bidiyo: Yanda Garba Shehu ya dakatar da dan Jarida daga ci gaba da tambayar shugaba Buhari>>Sowore

Bidiyo: Yanda Garba Shehu ya dakatar da dan Jarida daga ci gaba da tambayar shugaba Buhari>>Sowore

Uncategorized
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan amsar da ya bayar bayan tambayar da aka masa kan me zai ce game da binciken NDDC da EFCC da ake.   Shugaban kasar ya bayyana cewa akwai wanda suka ci amanar talakawa a gwamnatin baya da gwamnatinsa. Sowore yace amsar da shugaban kasar ya bayar ba itace ya dace ya bayar ba akan tambayar da aka masa duk da dai da dama sun zargi cewa an yi sukullen Kwamfuka a cikin Bidiyon. https://twitter.com/YeleSowore/status/1289501278519795715?s=19 A karshe kuma ya bayyana cewa ana iya ganin kakakin shugaban kasar, Garba Shehu yana gayawa 'yan jaridar su dakatar da tambayar da akewa shugaba Buhatin, ta isa haka.
Wasu dana yadda dasu a Gwamnatina sun ci amanata>>Shugaba Buhari

Wasu dana yadda dasu a Gwamnatina sun ci amanata>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wasu da ya yadda dasu ya basu mukami a gwamnatinsa sun ci amanar da ya basu.   Shugaban ya bayyana hakane yayin da yake amsa tambayoyi kan cin hancin da aka samu a hukumomin EFCC da NDDC bayan kammala sallar Idi a yau. Shugaban ya bayyana cewa a gwamnatin da ta gabata akwai wanda suka ci amana, hakanan a wannan gwamnatin tasa ma akwaisu.   Yace ya bayar da umarnin bude Asusun ajiya na bai daya, TSA sanna ya umarci a sayar da kadarorin da aka kwato a saka kudin a ciki. Yace dalilinsa na yin hakan shine babu damar mayarwa da wanda suka saci kadarar koda bayan ya sauka daga mulki.
Za’a Binciki Dukkan Shari’ar Laifin Cin Hanci Da Rashawa Da Ta Gabata Da Ta Yanzu>>Shugaba Buhari

Za’a Binciki Dukkan Shari’ar Laifin Cin Hanci Da Rashawa Da Ta Gabata Da Ta Yanzu>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaba Muhmmadu Buhari ya yi alkawalin cewa duk binciken da ake ci gaba da yi a baya da kuma sabbin laifukan cin hanci da rashawa za a bi diddigin su. Shugaban ya yi wannan alkawarin ne ranar juma'a a cikin sakon da ya aike yan Najeriya bayan sallar Eidi da suka yi tare da dangin shi da mataimakan shi a farfajiyar gidan gwamnatin tarayya, Abuja. Ya ce abin takaici ne cewa wasu jami’an gwamnati da aka amince da su a yaki da matsalar cin hanci da rashawa a gwamnatocin da suka gabata, sun ci amanar da aka ba su, ya kuma kara da cewa gwamnatinsa ta jaddadawa  kwamitin binciken na musamman don tabbatar da cewa an bincika dukkan kara. Ya kuma ba da tabbacin cewa za a sami karin kayan aiki ga sojojin kasar, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro don magance matsalar rashin tsa
Ko ‘yan Najeriya sun shaida mun yi iya bakin kokarin mu kan tsaro>>Shugaba Buhari

Ko ‘yan Najeriya sun shaida mun yi iya bakin kokarin mu kan tsaro>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun shaida cewa gwamnatinsa ta yi iya bakin kokarinta kan harkar tsaro.   Shugaban ya bayyana hakane ga manema labarai a fadarshi bayan sallar Idi da yayi da iyalansa da kuma wasu manyan jami'an gwamnati. Shugaban ya bayyana cewa a lokacin da gwamnatinsa ta karbi Mulki ta gaji matsalolin tsaro na Boko Haram da kuma 'yan Bindiga tsagera a kudu. Yace kuma 'yan Najeriya sun shaida ci gabam da aka samu a wadannan bangarori.   Yace amma abinda ke faruwa yanzu a Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya abin damuwane sosai.   Yace daga Rahotannin da yake samu, yasan cewa jami'an tsaro zasu iya kara kaimi dan maganin wadannan miyagu.   Shugaban ya kuma sha alwashin sake samarwa da jami'an ts...
Bayan kaiwa Gwamna Zulum Hari, Majalisa ta kara yin kira ga shugaba Buhari ya kori shuwagabannin tsaro

Bayan kaiwa Gwamna Zulum Hari, Majalisa ta kara yin kira ga shugaba Buhari ya kori shuwagabannin tsaro

Siyasa
A karo na 2, majalisar Wakilai ta sake yin kira ga shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya canja shuwagabannin tsaro, kwanaki 2 bayan kaiwa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum hari.   Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Ndudi Elumelu ne ya bayyana haka inda yace wannan hari ya kara tabbatar da cewa shuwagabannin tsaron sun gaza. Yace dan haka suna sake kira da babbar murya cewa shugaban ya koresu ya canja wasu.   A baya dai da majalisar ta cewa shugaba Buhari ya kori shuwagabannin tsaron,  ya mayar da martanin cewa shine ke da ikon dorawa da saukesu ba majalisar ba.
Shugaba Buhari da iyalansa yayin Murnar Sallah

Shugaba Buhari da iyalansa yayin Murnar Sallah

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari kenan a wadannan hotuna inda yake tare da iyalansa a fadarshi ta Villa yayin da suke murnar sallah.   Uwargidan shugaban kasar, Hajiya A'isha Buhari ce ta saka hotunan inda ta taya 'yan Najeriya murnar Sallah ta kuma jinjina musu saboda kiyaye dokokin Coronavirus/COVID-19. https://twitter.com/aishambuhari/status/1289162926788694016?s=19 Tace 'yan Najeriyar su yi amfani da kudin tallafin da CBN ya basu dan inganta rayuwarsu.