fbpx
Friday, August 12
Shadow

Tag: Sifaniya

Spain ta yiwa wasanni dakatarwar sai baba ta gani

Spain ta yiwa wasanni dakatarwar sai baba ta gani

Wasanni
Gwamnatin Spain ta sanar da dakatar da dukkanin wasannin kwallon kafa ciki har da gasar La liga har zuwa lokacin da za ta kammala yakar annobar cutar corona da ke ci gaba da kisa a kasar.     Tun farkon watan Maris din nan ne hukumar kwallon kafar kasar ta umarci dakatar da wasannin na makwanni 2 da nufin dakile yaduwar cutar, sai dai a yau Litinin ma’aikatar wasannin kasar ta fitar da sanarwar da ke nuna cewa babu ranar dawowa wasannin har sai anga abin da hali ya yi game da cutar ta Corona.     Karkashin gasar ta Laliga dai, yanzu haka Barcelona ce ke jagorancin teburi da maki 58 bayan doka wasanni 27 tazarar maki biyu tsakaninta da babbar abokiyar dabinta Real Madrid da ke matsayin ta biyu. Matakin na Spain na zuwa bayan gwajin da aka yiwa Dan ...
Mutane 532 ne suka kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 a kasashen Iran da Sifaniya a yau

Mutane 532 ne suka kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 a kasashen Iran da Sifaniya a yau

Kiwon Lafiya
Rahotanni daga kasar Iran, daya daga cikin kasashen da Cutar Coronavirus/COVID-19 ta yi kamari ta bayyana cewa mutane 129 ne suka mutu a yau, Lahadi.   Hakan ya kai yawan mutanen da suka mutu a kasar zuwa 1,685. Me hulda da jama'a na ma'aikatar lafiya ta kasar, Kianouche Jahanpour ya bayyanawa manema labarai cewa an samu karin mutane  da suka kamu da cutar 1,028 wanda ya kai yawan wanda suka kamu a kasar zuwa 21,638.   A kasar Sifaniya ma Kanfanin dillancin Labarai na AFP ya bayyana cewa mutane 394 ne suka mutu a ra a daya.