
Man Fetur din da Najeriya ke siyowa a kasashen Turai yafi wanda ake samu a haramtattun matatan mai gurbacewa
Man fetur ɗin kasuwar bayan fage da ake samu a Najeriya ya fi ƙarancin guba a kan mai da dizal ɗin da dillalan Turai ke siyar mata, a cewar wani rahoto.
Ana dai fargabar cewa man da dillalan kayayyaki suke siyar wa Najeriya bayan an tace shi a nahiyar Turai yana shafar ingancin iskar da ake shaƙa a ƙasar mafi yawan jama'a a Afirka.
Wata ƙungiyar masu fafutuka da ake kira Stakeholder Democracy Network (SDN) ta kwatanta samfur 91 na man da ake shigarwa ƙasar da na Najeriya da ake samu a kasuwar bayan fage daga yankin Neja Delta mai arziƙin man fetur.
Nazarinta ya nuna cewa man fetur da dizal ɗin da ake kai wa ƙasar na ƙunshe da sinadarin sulphur sama da ninki 200 fiye da abin da Tarayyar Turai ta ƙayyade.
Idan aka kwatanta, da man fetur ɗin da aka ...