
Soja ya kashe yaro dan shekaru 10 a Kaduna saboda ya je ciro Mangoro a Bariki
Wani soja ya kama yaro dan shekaru 10 a jihar Kaduna inda ya lakada masa duka har ya mutu saboda ya je ciro Mangoro a Barikin Kotoko dake kusa da unguwar Hayin Banki.
Sojan ya kama yaron yaje ciro Mangoro amma yaron sai ya tsere. Sojan ya biyo yaron cikin unguwa inda ya kamashi ya tafi dashi barikin ya tsareshi ya rika gana masa Azaba har ya mutu.
Sardaunan Hayin Banki, Malam Ibrahim Hassan Wuyo ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace abokan aikin sojan sun nemi ya saki yaron amma ya ki, bayan da ya kasheshi ne sai ya kai gawarsa unguwar Kanawa ya yadda.
Yace zuwa yanzu dai an kama sojan inda aka mikawa 'yansanda shi. Kakakin 'yansandan Jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda yace sun fara Binciken lamarin.
“Th...