
Ku rika yiwa jami’an tsaro sauki idan sun zo siyayya>>Shugaba Buhari ga ‘yan kasuwa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan kasuwa da su rika yiwa jami'an tsaro saukin kaya idan sun je saye.
Ya bayyana hakane a yayin da yake kaddamar da tambarin tunawa da 'yan mazan jiya na shekarar 2021. Shugaban yace a rika wa sojoji ragi idan sun ke siyayya alamace ta cewa ana musu godiya kan aikin da sukewa kasa.
Ya jinjinawa sojojin bisa sadaukar da rayukansu da suka yi na yakoki a yakin Duniya na 1 dana 2 da kuma ayyukan samar da tsaro da suka je kasashe daban-daban da kuma yakin basasar da suka yi a Najeriya da kuma wanda suke yi da masu tada kayar baya.
Shugaban ya bayyana cewa Duniya na bikin tunawa da 'yan mazan jiya ranar 11 ga watan Nuwamba amma Najeriya ta mayar da nata zuwa 15 ga watan Janairu saboda tunawa da yakin Basasa.
...