
Samar da tsaro ba abune me yuwa da za’a ce ya gagari gwamnati ba>>Aminu Waziri Tambuwal
Gwamna jihar Sokoto ya caccaki gwamnatin tarayya akan matsalar tsaro.
Yayi wannan caccaka tasa ne a wajan wani taro da aka hada ta kafar sadarwar Zamani inda yace abune me sauki samar da shugabanci da kuma tsaro a kasarnan.
Yace abu na farko dai akwai karancin 'yansanda da sauran jami'an tsaro wanda kuma akwai 'yan Najeriya masu karfi a jika da a shirye suke su nada gudummawa ta fannin.
Ya kuma bayyana cewa, misali a jiharsa ta Sokoto ana samun hadin kai tsakanin shuwagabannin tsaro ba kamar yanda yake faruwa a gwamnatin tarayya ba.
“It is not rocket science; it can be done. We need to recruit more hands and there are many patriotic Nigerians, eminently qualified, able-bodied people that are ready and willing to serve this country in our securi