fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Tag: Tallafin Coronavirus/COVID-19

Albishirinku: A yau, Gwamnatin tarayya ta bude shafin neman tallafi daga Biliyan 75 data ware, duba yanda zaku nema

Albishirinku: A yau, Gwamnatin tarayya ta bude shafin neman tallafi daga Biliyan 75 data ware, duba yanda zaku nema

Siyasa
A yau, Litinin ne gwamnatin tarayya zata bude shafinnan na Survival Fund wanda zata baiwa 'yan Najeriya daidaku da kuma kananan 'yan kasuwa tallafin kudi.   Ofishin dake kula da yanda za'a bayar da kudinne ya bayyana haka a jiya, Lahadi a Abuja inda ya fayyace lokutan da kowane kasuwanci zai iya amfani dashi dan yin rijista. Da Misalin Karfe 10 na safiyar yaune za'a bude shafin wanda kuma sanarwar tace za'a fara da bangaren Ilimi ne wanda sune zasu fara Rijista daga yau,21 ga watan Satumba na shwkarar 2020.   Sanarwar tace kasuwancin otal da gidajen Abinci kuma zasu fara tasu Tijistar ne daga juma'a me zuwa, 25 ga wata da Misalin karfe 12:00 na dare.   Sanarwar tace ranar Litinin me zuwa 28 ga watan Satumba ne za'a baiwa duka sauran kasuwanci dama su...
Gwamnati ta bayyana tsarin da zata bi waja rabawa kananan ‘yan kasuwa tallafin Dubu 50

Gwamnati ta bayyana tsarin da zata bi waja rabawa kananan ‘yan kasuwa tallafin Dubu 50

Siyasa
Tola Johnson, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan Kananan Masana’antu da Matsakaitan Masana’antu (MSMEs), ya ce kananan ‘yan kasuwa 100,000 za su samu N50,000 kowanne su. Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa karimcin wani bangare ne na tallafin cutar coronavirus warin karfafa tattalin arziki. Ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da aiwatar da asusun ceton rayuwa da kuma shirin tabbatar da tallafi ga kananan yan kasuwa a ranar Alhamis a Abuja. Johnson, mai kula da ayyukan, ya ce tsare-tsaren na daga cikin shirin Dorewar tattalin arzikin da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shi. “Bayan haka, akwai rajistar kyauta ta CAC kyauta ne ga kanana da masakaitan yan kasuwa amma gw
An kama kayan tallafin Coronavirus/COVID-19 na jihar Benue a kasuwar Kano

An kama kayan tallafin Coronavirus/COVID-19 na jihar Benue a kasuwar Kano

Uncategorized
Hukumar 'yansanda ta jihar Kano ta sanar da kama wasu kayan tallafin Coronavirus/COVID-19 da aka kai kasuwar Kano daga jihar Benue dan sayarwa.   Kwamishinan 'yansandan jihar, CP Habu Sani ya tabbatar da faruwar lamarin a yau, Laraba inda yace kayan da aka kama akwai katan din taliyar Indomi ta Dangote guda 1,958.   Yace darajar kayan sun haura Miliyan 4 inda yace ana shirin cire alamar da aka rubuta musu ta cewa ba na sayarwa bane dan fara sayar dasu.
Gidaje Miliyan 2.4 Zasu Ci Gajiyar Tallafin Gwamantin Tarayya>>Hadimin Shugaba Buhari

Gidaje Miliyan 2.4 Zasu Ci Gajiyar Tallafin Gwamantin Tarayya>>Hadimin Shugaba Buhari

Siyasa
Don tabbatar da tanadin abinci ga 'yan kasa, akalla gidaje miliyan 2.4 za su amfana da shirin tallafin na COVID-19 na Gwamnatin Tarayya, in ji wani mai taimakawa shugaban.   Dakta Andrew Kwasari, Mataimaki na Musamman (SSA), ga shugaban kasa kan harkar Noma, ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, ranar Lahadi a Abuja. Kwasari yana magana ne game da koma baya ga yawan ayyukan da kwamitin NSAC din ya bayar, don tabbatar da tattalin arzikin kasar daga illolin COVID-19. NAN ta ba da rahoton cewa za a samar da kayan tallafin ta hanyar shirin Noma da Abinci da Ayyuka (AFJP), a karkashin Sashin Noma na Tsarin Tallafin tattalin arzikin Najeriya (NESP), karkashin jagorancin SSA. Kwasari ya kara cewa, a kokarin magance matsalar tabarba...
Gwamnati ta ware Tiriliyan 2.6 dan tallafawa ‘yan kasuwa, ku yi amfani da wannan damar>>Boss Mustapha

Gwamnati ta ware Tiriliyan 2.6 dan tallafawa ‘yan kasuwa, ku yi amfani da wannan damar>>Boss Mustapha

Siyasa
Sakataren gwamnatin tarayya wanda kuma shine shugaban kwamitin gwamnatin tarayya dake kula da yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware Tiriyan 2.6 dan baiwa 'yan kasuwa da sauran harkokin tattalin arziki tallafi saboda zuwa Coronavirus/COVID-19.   Boss Mustapha ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai inda ya jawo hankalin mutane su yi amfani da wannan damar. Hutudole ya ruwaito muku cewa, Boss Mustapha ya godewa matasa saboda yanda suke bada hadin kai wajan yaki da cutar Coronavirus/COVID-19. Ya bayyana cewa idan aka ci gana da samun irin wannan hafin kai, za'a yi nasara a yaki da cutar.
Gwamnati ta fara rabawa Kanawa tallafin Coronavirus/COVID-19 na Miliyan 500 dan rage musu radadin talauci

Gwamnati ta fara rabawa Kanawa tallafin Coronavirus/COVID-19 na Miliyan 500 dan rage musu radadin talauci

Siyasa
Gwamnatin jihar Kano ta fara rabawa talakawa tallafin Coronavirus/COVID-19 da aka samar dan rage musu radadin talauci da annobar cutar ta zo dashi.   Hakan ya fito ne daga bakin memban kwamitin yaki da cutar, Abdulkadir Sidi. Yace mataumakin gwamnan, Nasiru Yusuf Gawunane ya jagoranci kaddamar da fara rabon a gidan ajiyar kayan abinci dake Kumbotso.   Yace tallafin da darajarsa ta kai Naira Miliyan 500 zai amfani gidaje miliyan 1.67 inda yace kayan tallafin sun hada da gishiri, Suga, Taliya, Shinkafa dadai sauransu.
Watanni 2 bayan bayar da tallafin Coronavirus/COVID-19 an ganoshi ajiye a dakunan ajiya,har yanzu gwamnatin jihar Naija bata rabawa mutane ba

Watanni 2 bayan bayar da tallafin Coronavirus/COVID-19 an ganoshi ajiye a dakunan ajiya,har yanzu gwamnatin jihar Naija bata rabawa mutane ba

Siyasa
Majalisar Jihar Naija ta gano kayan tallafin Coronavirus/COVID-19 da aka baiwa jihar watanni 2 da suka gabata wanda har yanzu ba'a rabawa mutane su ba.   Hakan ya bayyanane bayan da kwamitin dake saka ido kan Coronavirus/COVID-19 na majalisar ya ke ran gadi. Shugaban kwamitin, Abdulmalik Madaki Bosso ya bayyana rashin jin dadinshi inda yace mutane na cikin bukata duk da yake cewa an dage dokar kulle.   Jihar Naija ta samu tallafin tirela 88 daga gwamnatin tarayya da sauran mutane masu zaman kansu da kamfanoni ma duk sun bada tallafin, kamar yanda Dailytrust ta ruwaito.   Shugaban kwamitin kula da coronavirus a jihar,  Ibrahim Ahmad Matane wanda kuma shine mataimakin gwamnan jihar ya bayyana cewq dalilin da yasa ba'a raba kayan ba shine har yanzu tall
Yawan masu Amfana da tallafin Gwamnatin tarayya ya karu zuwa Miliyan 3.6>>Minista Sadiya Umar Farouk

Yawan masu Amfana da tallafin Gwamnatin tarayya ya karu zuwa Miliyan 3.6>>Minista Sadiya Umar Farouk

Siyasa
Ministar jin kai da kula da Ibtila'i,  Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa mutanen dake amfana da tallafin gwamnatin tarayya sun karu akan rijistar mafiya bujata zuwa Miliyan 3.6.   Ta bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a Abuja a ganawar da kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 yayi da manema labarai. Tace yanzu an samu karin jihohi a Rijistar. Tace kuma suna hada kai da majalisar Dinkin Duniya wajan ganin an baiwa kananan hukumomi 20 da cutar Coronavirus/COVID-19 tafi shafa tallafi na musamman.   A baya dai NCDC ta bayyana kananan hukumomi 20 da cutar Coronavirus/COVID-19 tafi shafa.
ICPC zata fara binciken zargin sama da fadi da kudin Talafin Coronavirus/COVID-19 a Najeriya

ICPC zata fara binciken zargin sama da fadi da kudin Talafin Coronavirus/COVID-19 a Najeriya

Uncategorized
Tun bayan samun bullar cutar coronavirus a Najeriya, wasu ‘yan kasa da ma kungiyoyi masu zaman kansu ke mika gudunmawar su domin yaki da cutar.     Fadar gwamnatin kasar ta ce an samu zunzurutun Naira miliyan 776.   Bayan da aka fara samun korafe-korafe akan yadda ake aiwatar da kudaden, Hukumar Yaki da Cin Hanci ICPC ta ce, za ta fara bincike akan lamarin.     A wata sanarwa da ke dauke da sa hanun Shugaban ayyuka na hukumar ICPC Akeem Lawal, ya bayyana cewa hukumar ta fara bincike akan zarge-zargen al’mundahana da wasu bangarorin hukumomin Gwamnati suka yi wajen rabon tallafin, da zargin rashawa wajen sayo kayan tallafin da kudaden zirga-zirga, da kudaden da aka kashe wajen wayar da kan al'umma a game da cutar.     L
Abincin da Buhari ya tura Kano bai lalace ba>>Gwamnatin Ganduje

Abincin da Buhari ya tura Kano bai lalace ba>>Gwamnatin Ganduje

Siyasa
Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta musanta zargin da wasu suke yi cewa ta bar kayan abincin tallafin da gwamnatin tarayya ta aika jihar ruwan sama ya dake su. Sanarwar da Kwamishinan watsa labaran jihar, Muhammad Garba, ya aike wa manema labarai ranar Talata ta ce ba gaskiya ba ne zargin da wasu ke yi cewa an bar kayan abincin ya lalace sakamakon dukan ruwan saman. "Gwamnatin Kano tana mai yin watsi da rahotannin da wasu masu bakar aniya suke yadawa cewa an bar hatsin da gwamnatin tarayya ta turo Kano mako biyu da suka wuce a matsayin tallafi a filin KASCO inda ruwan sama ya lalata shi," in ji sanarwar. Kwamishinan ya kara da cewa tun kafin a kawo tallafin ruwan sama ya dade da sauka a Kano kuma gwamnati ta dauki matakin rufe kayan a...