
Buhari ya aika da sakon ta’aziyyar mutuwar tsohon shugaban kasar Nijar, Tandja
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Mamadou Tandja, tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar.
Ya mutu a ranar Talata yana da shekaru 82 bayan shekaru da rashin lafiya.
A ranar Laraba, Buhari ya ce Nijar ta yi rashin wani tsohon shugaba wanda ke da kwarewar soja, siyasa da kuma mulki.
Shugaban ya yaba da irin gudummawar da marigayin ya bayar a fagen soja da kuma fagen siyasar kasarsa.
Shugaban na Najeriya ya yi fatan Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar, dangin Tandja da sauransu karfin gwiwar jure rashin.
"Gwamnati da mutanen Najeriya na tare da dukkan mutanen Nijar a wannan lokacin na bakin ciki," sanarwar ta'aziyyar Buhari da kakakin shi, Garba Shehu ya fitar.