fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Taraba

‘Yan bindiga sun sace Shugaban kungiyar ‘yan kwadago na jihar Taraba

‘Yan bindiga sun sace Shugaban kungiyar ‘yan kwadago na jihar Taraba

Tsaro
Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar ranar Lahadi, sun yi awon gaba da Kwamared Peter Jediel, shugaban kungiyar 'yan kwadagon Najeriya reshen jihar Taraba (NLC). A cewar wani Dan'uwan wanda aka sace ya shaida cewa 'yan bindigar sun sace yayan nasa ne a gidan sa da ke Sunkani A karamar hukumar Ardo- Kola na jihar Taraba. Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun sace shine yayin da yake kallon talabijin a cikin Dakinsa inda daga bisani sukai Awon gaba dashi. 'Bana wajan Alokacin da aka zo garkuwa da Dan'uwan nawa sai dai matarsa ce ta shaida min hakan, duk kuwa da cewa babu yadda zamu iya wajan cetar Dan'uwan Namu kasancewar 'yan bindigar suna Dauke da Muggan makamai. Inji shi Koda yake harzuwa wannan lokaci rundunar 'yan sanda bata tabbatar da faruwar lamarin ba, sai dai wata Majiya dat...
Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su fara rike Bindiga>>Gwamnan Taraba

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su fara rike Bindiga>>Gwamnan Taraba

Tsaro, Uncategorized
Gwamnan jihar Taraba ya nemi gwamnatin tarayya ta lamuncewa 'yan Najeriya su rika rike Bindiga saboda matsalar tsaro da ta yi yawa.   Gwamna Darius Ishaku ya bayyana hakane a yayin ganwarda da shuwagabannin kananan hukumomi 15 na jiharsa ranar Talata. Sun je masa jaje ne kan yin garkuwa da kuma kashdaya daga cikin shuwagabannin kananan hukumomin jihar.   Gwamnan yace lamarin tsaro ya tabarbare sosai a Najeriya dan haka ne ya ke baiwa shugaban kasa shawarar a bar kowa ya rike bindiga, idan aka san cewa kowa na da Bindigar AK47, babu wanda zai je maka gida. Idam kuwa mutum yaje to yadan me ya tara. The security in this country has gone to the lowest ebb and we have to all wake up. We as leaders have given our advises severally as to the change to the security arc...
Yan sanda sun dakile yunkurin yin garkuwa da wani dan kasar China a Jihar Taraba

Yan sanda sun dakile yunkurin yin garkuwa da wani dan kasar China a Jihar Taraba

Uncategorized
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta ce jami’anta sun dakile yunkurin sace wani dan kasar China da ke hanyar Wukari zuwa Jalingo.   A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP David Misal, ya aike wa manema labarai ta kafar WhatsApp, ya ce an kashe daya daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwar ne a yayin musayar wuta.   Yunkurin satar a cewar sanarwar an soke shi ne a Gidin Doruwa, da ke cikin karamar hukumar Wukari.
Kalli hotunan matar tsohon Gwamnan Taraba da ta sake karbar Musulunci a Karo na 2

Kalli hotunan matar tsohon Gwamnan Taraba da ta sake karbar Musulunci a Karo na 2

Siyasa
Matar tsohon gwamnan Taraba, Hauwa Suntai bayan Mutuwar Mijinta, ta sake yin aure.   A baya dama Musulmace amma saidai ta koma Kirista bayan data auri gwamnan. Saidai daga baya, bayan rasuwar mijinta, ta sake aure, ta sake komowa cikin addinin Musulunci.   Hauwa 'yar Asalin Jihar Borno ce. Wanda ta aura din bayan mutuwar mijinta, dan uwane ga tsohiwar matar shugaban kasa, Turai 'yaradua, me suna Haliru Sa'ad Malami. A shekarar 2019 ne aka daura auren masoyan kuma bayan hakan a yanzu Rahotanni sun nuna cewa Hauwa ta sako komowa cikin addinin Musulunci. Tsohon Mijinta, Danbaba Suntai ya samu matsala ne tun bayan yin hadarin jirgin sama wanda daga baya ma sai Mutuwa yayi.
Akwai Bukatar Daukan matakin Gaggawa kan batun tsaron kasa >> Ishaku

Akwai Bukatar Daukan matakin Gaggawa kan batun tsaron kasa >> Ishaku

Tsaro
Gwamna Darius Dickson Ishaku na jihar Taraba ya koka kan yadda matsalar tsaro a fadin kasar ta fi karfin gwamnonin jihohi, don haka ya mika bukatar kafa ‘yan sandan jihohi domin shawu kan matsalar tsaro da ta addabi wasu sassan kasar. A cewarsa, kafa ‘yan sandan jiha shine mafita daga kalubalen tsaro da ake fuskanta a fadin kasar.  Ya ci gaba da cewa kafa 'yan sandan jihohi zai magance matsalolin satar mutane da makamantansu a fadin kasar. Ya ba da misali da Kasar Amurka wacce Najeriya ta kwafi tsarin mulkin ta, inda ya lura cewa kasar na da tarayya, jihohi, da kuma ‘yan sanda na cikin gida - tsarin da Gwamna Ishaku ke son Najeriya ta samar. Gwamnan  ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata babbar tawaga daga karamar hukumar Gassol ta jihar kan ziyarar godiya da ...
Da Duminsa: ‘Yan Bindiga sun sace dan majalisa

Da Duminsa: ‘Yan Bindiga sun sace dan majalisa

Tsaro
Yan Bindiga a jihar Taraba sun sace dan majalisa me wakiltar Nguroje.   Yan Bindigar sun sace Barrista Bashir Muhammad dake wakilci a majalisar jihar da misalin karfe 1:30 na darwn da ya gabata.   Iyalanshi sun shaidawa TheNation cewa har gida 'yan Bindigar dauke da muggan makamai suka kai masa hari suka saceshi.   Saidai babu rahoton wanda ya jikkata duk da harbe-harben da 'yan Bindigar suka yi na tsawon mintuna 45. A member representing Nguroje Constituency in the Taraba House of Assembly,  Barr. Bashir Mohammed has been kidnapped. A family source told The Nation that the lawmaker was kidnapped from his house behind SSS office area of Jalingo at about 1. 30. am Wednesday by a heavily armed gunmen.   According to the source, the gunmen...
Yan bindiga sun kashe sanannen dan ta’adda mai suna “Kinkon” a Jihar Taraba

Yan bindiga sun kashe sanannen dan ta’adda mai suna “Kinkon” a Jihar Taraba

Tsaro
A daren Litinin ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka harbe wani sanannen mai laifi, Salihu Zakari wanda aka fi sani da“ Kinkon ”a kauyen Tella, da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba. Salihu Zakari ya kasance yana ta'addancin Sabongida da Tella a cikin shekaru goma da suka gabata kuma shi ke da alhakin sacewa tare da kashe wasu 'yan kasa marasa laifi a karamar hukumar Gassol.   Kinkon ya hadu da ajalinsa ne da misalin karfe 9. na daren ranar Litinin lokacin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kira shi a waya don ganawa da su a wani wuri a kauyen na Tell.   Kinkon yana kan hanyarsa ta ganawa da wadanda suka kira shi da misalin karfe 9.00 na dare sai kwatsam suka harbe, daga nan akai kai shi asibitin, indai a can ya mutu.
Masu garkuwa da mutane sun kashe ‘yan kasuwar shanu 2, tare da yin awon gaba da wasu 2 a Taraba

Masu garkuwa da mutane sun kashe ‘yan kasuwar shanu 2, tare da yin awon gaba da wasu 2 a Taraba

Tsaro
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne a ranar Litinin sun kashe‘ yan kasuwar shanu 2 tare da yin garkuwa da wasu 2 a garin Andame da ke cikin karamar hukumar Karim-Lamido ta jihar Taraba. Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da miliyoyin Naira na’ yan kasuwar shanun wadanda aka ce sun zo daga Kano zuwa yankin don sayen saniya. Garin wanda ke da babbar kasuwar shanu ya fuskanci hare-hare da dama daga 'yan fashi da makami da masu satar mutane a tsawon shekaru. Wata majiya a yankin, ta shaida wa Aminiya cewa sama da ’yan kasuwa 12 masu garkuwa da mutane suka sace a garin kuma sun biya miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa a cikin makonnin da suka gabata. Yankin, an tattara shi ya hada iyaka da jihohin Filato, Bauchi da Gombe ana fuskantar ...
Matar wani magidanci, Babangida ta guntule masa mazakuta bayan dirkawa makwabciyarsu ciki a Taraba

Matar wani magidanci, Babangida ta guntule masa mazakuta bayan dirkawa makwabciyarsu ciki a Taraba

Siyasa
Lamarin ya farune a unguwar Appawa dake karamar hukumar Lau ta jihar Taraba.   Babbangida wanda aka fi sani da Bangis, na kwance kawai saidai ji yayi matarsa na gagara masa wuka a mazakutarsa. Hakan na zuwane kusan watanni 4 bayan da aka kama wata mata a jihar da ta yankewa mijinta mazakuta saboda zai kara aure.   Wani makwabcin Magidancin ya bayyana cewa, Babangida ya je aiki ya dawo yana hutawa kawai sai matar tasa ta far masa, amma yayi sa'a ya tashi ya kwace wukar itama ta jiwa kanta ciwo, an garzaya dashi Asibiti.   Da aka tambayeta Dalili tace a Baibul an gaya musu a yanke duk wani Abu dake sa mutum yana aikata Zunubi.   Jami'an 'yansanda na jihar dai basu ce komai ba zuwa yanzu, Kamar yanda Guardian ta bayyana.   “In the ...
‘Yan sanda sun cafke mutum 23 da ake zargi a Taraba saboda Satar tallafin Covid-19

‘Yan sanda sun cafke mutum 23 da ake zargi a Taraba saboda Satar tallafin Covid-19

Tsaro
A ranar Litinin ne rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba, ta ba da sanarwar kame wasu‘ yan mutane 23 da ake zargi da wawure dukiyar gwamnati da sunan masu zanga-zangar SARS. DSP David Missal, kwamandan rundunar, ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a Jalingo. Kakakin rundunar 'yan sandar ya bayyana cewa, rundunar' yan sandan ta cafke wasu mutane 23 tare da kame babura 6, motoci 3 dauke da kaya, da buhunan Shinkafa 8, da buhunan takin zamani 39, da katon na indomie 9, da gadaje 3 da kuma katan din macaroni 4.