Saturday, March 28
Shadow

Tag: Tsaro

Sojoji 47 ne Boko Haram suka kashe mana>>Rundunar sojin Najeriya

Sojoji 47 ne Boko Haram suka kashe mana>>Rundunar sojin Najeriya

Siyasa
Hukumar sojin Najeriya ta yi magana kan harin  kwantan Bauna da mayakan Boko Haram suka kaimata.   Me magana da yawun sojin, Majo Janar John Enenche ya bayyana cewa sojoji 47 ne aka kashe musu lokacin kwantan baunan sannan kuma suma sun kashe wasu yan ta'addar har suka kwace musu mota daya.   Channelstv ta ruwaitoshi yana cewa yana jajantawa iyalan mamatan sannan kuma hukumar soji zata jajirce wajan ganin ta yi nasara a yakin.    
Yawan sojojin Najeriya da Boko Haram ta kashe a harin kwantan bauna sun kai akalla 100

Yawan sojojin Najeriya da Boko Haram ta kashe a harin kwantan bauna sun kai akalla 100

Uncategorized
Rahitanni daga jihar Borno na kara bayyana kan harin kwantan bauna da Kungiyar Boko Haram bangaren ISWAP ta kaiwa sojojin Najeriya.   A rahoton farko wanda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito yace sojoji 70 ne suka mutu a harin.   Saidai a Rahoto  shahararren me kawo rahoto ka  rikice-rikice da ta'addanci a Najeriya, Ahmad Salkida ya saki, na cewa sojojin da aka kashe a kalla sun kai 100.   Salkida ta shafinshi na HumAngle ya bayyana cewa akwai kuma sojoji da dama da suka bace sanan wanda suka ji rauni a harin an garzaya dasu Asibiti.   A cikin sojojin da suka mutu, akwai kusan manayn sojoji guda 4. Akwai kuma mafarauta 4 da aka rutsa dasu a harin.   Sannan akwai sojoji da ba'a san iya yawansu ba da maharan suka yi garkuwa dasu
Coronavirus/COVID-19: Shugaban ‘yansandan Najeriya ya bukaci a rage zuwa ofishin ‘yansanda in ba dole ba sannan ‘ya sandan su rage kama mutane

Coronavirus/COVID-19: Shugaban ‘yansandan Najeriya ya bukaci a rage zuwa ofishin ‘yansanda in ba dole ba sannan ‘ya sandan su rage kama mutane

Kiwon Lafiya
Shugaban 'yansandan Najeriya,Muhammad Adamu ya  bukaci 'yan Najeriya da su rage zuwa ofishin 'yansanda in ba wai abin ya zama dole ba.     Ya fitar da sanarwarne ta hannun me magana da yawun rundunar,Frank Mba inda yace suma 'yan sanda su kula da lafiyar jikinsu kan yanda ake fama da cutarnan na Coronavirus/COVID-19.   Ya bukaci 'yansandan da kansu rage kamawa da tsare mutane indai ba abinda ya shafi ta'addanci ko fashi da makami ko kisa da sauran laifikan da ba'a bayar da beli akansu ba.   Ya bukaci bincike da tantance masu laifi kamin a tsaresu.   Sanarwar ta kara da cewa, 'yansanda su ta batar su  tsaida dokar hana taruwar mutane da gwamnatin tarayya ta saka a yankunan da suke aiki.   Sanna kuma a kulle makarantun horar da '
Za A Fara Daukar Sabbin ‘Yan Sanda Har Guda 10,000

Za A Fara Daukar Sabbin ‘Yan Sanda Har Guda 10,000

Uncategorized
Ministan kula da al’amuran 'yan sandan Nijeriya, Muhammad Dingyadi ya bayyana cewa nan bada jimawa ba hukumar 'yan sanda za ta fara daukan sabbin kuratan 'yan sanda 10,000 a duk fadin Nijeriya, kamar yadda PUNCH ta ruwaito.   Punch ta ruwaito hakan na daga cikin cika alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na samar da sabbin jami’an 'yan sanda 40,000 a tsawon shekaru hudu na wa’adin mulkinsa.   Dingyadi ya bayyana cewa sun fara tsara yadda daukan aikin zai kasance, wanda suke sa ran zai kara adadin jami’an Yansandan Najeriya tare da taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.   Minista Dingyadi ya bayyana haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin bikin kaddamar da littafi mai suna; “Introduction to law enforcement: A trai
Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Kai Wasu Hare-hare a Sambisa

Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Kai Wasu Hare-hare a Sambisa

Siyasa
Kakakin Rundunar Air Commodore Ibikunke Daramola, ya ce harin ya biyo bayan wani rahoton sirri da suka samu ne dake nuna cewa mayakan Boko Haram sun yi kaura zuwa wani yanki na dajin daga inda suke shirye-shiryen kai wani babban hari ga sojoji da fararen hula.   Jiragen yakin Najeriyar sun afka wa ‘yan ta'addan, duk da cewa wasu daga cikinsu sun yi yunkurin tserewa amma jiragen sun same su gab da lokacin.   Wannan sabon farmaki mai taken "Operation Decisive Edge" na zuwa ne biyo bayan kammala shirin operation “Rattle Snake 3”.   A cewar babban hafsan hafsoshin saman kasar, Air marshall Sadique Abubakar, an samu gagarumar nasara. Ya ce “an kona kimanin sansanonin Boko Haram guda ashirin tare da kashe ‘yan ta'addan.”   Babban hafsan sojin saman
Masu garkuwa da mutane Sun Sace Dalubai 4 a Katsina

Masu garkuwa da mutane Sun Sace Dalubai 4 a Katsina

Uncategorized
Wadanda ake zargi da masu satar mutane ne a ranar Litinin da daddare sun sace daliban Rufus Giwa Polytechnic guda hudu a kan hanyarsu ta zuwa jihar Zamfara don halatar taron wayar da kai ga masu yiwa kasa hidma (NYSC) Wanda zai gudana a ranar talata.   Wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da maza uku da wata mata an sace sune a kusa da Funtua a cikin jihar Katsina da misalin karfe 11:30 na dare inda masu garkuwa da mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da su a kan hanya.   Sakamakon wannan matakin, jami’an tsaro sun bada shawararsu ga masu ababen hawa don gujewa tafiye-tafiye a cikin dare musamman a wuraren da akwai barazanar tsaro.
Najeriya ta soke layukan waya sama da miliyan 2 saboda dalilan tsaro

Najeriya ta soke layukan waya sama da miliyan 2 saboda dalilan tsaro

Siyasa
Hukumar sadarwar Najeriya ta sanar da soke layukan waya miliyan 2 da dubu 200 wadanda ake amfani da su ba tare da yi musu rajista kamar yadda dokar kasa ta tanada ba.   Shugaban hukumar Farfesa Umar Danbatta ya sanar da daukar matakin wanda yace ya shafi layukan kamfanonin sadarwa da dama.   Farfesa Danbatta yace hukumar san a kokari wajen ganin cewar kowanne layin waya daga cikin miliyan 184 da aka yiwa rajista na dauke da bayanan masu amfani da su da ake iya tantancewa koda yaushe ba tare da samun matsala ba.   Shugaban hukumar ya sha alwashin cewar zasu dinga gudanar da bincike lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da cewar ba’a sake samun irin wannan matsala ba.   Idan dai ba’a manta ba a watan Satumbar bara ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami ya
Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Wasu ‘Yan Agajin Izala Guda Biyu ‘Yan Gida Daya A Zamfara

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Wasu ‘Yan Agajin Izala Guda Biyu ‘Yan Gida Daya A Zamfara

Uncategorized
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da 'yan agajin kungiyar Izalah reshen Talata Mafara guda biyu 'yan gida guda. Imrana Isah Magami Da Sharhabilu Isah Magami sun je ziyarar mahaifiyarsu ne a garin Bagega dake kusa da Anka suka hadu da masu garkuwa da mutanen a hanyarsu ta tafiya, kuma sun sanya kudin fansa naira miliyan daya. Ya Allah ka yi masu mafita.
Boko Haram na mika kansu ga sojin Najeriya

Boko Haram na mika kansu ga sojin Najeriya

Uncategorized
Rundunar sojin Najeriya tace ana cigaba da samun mayakan kungiyar Boko Haram dake mika kan su ga dakarun dake aiki a karkashin rundunar Lafiya Dole dake Maiduguri.     Jami’in yada labaran sojin dake kula da ayyukan soji Kanar Aminu Ilyasu yace an samu karin mayakan da suka mika kan su ga dakarun gwamnati.   Kanar Ilyasu ya kuma bayyana cewar, dakarun su na cigaba da samun galaba akan mayakan a Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da suka hada da Borno da Adamawa. Jami’in yace dakarun su sun yi nasarar murkushe mayakan boko haram da suka nemi kutsa kai karamar hukuma Madagali dake Jihar Adamawa, inda suka kasha 3 kana sauran suka tsere dauke da harin bindiga.   Kanar Ilyasu ya kuma bayyana kubutar da wata mata da ‘dan ta da sojoji suka yi a Ng