
Karin Kudin Man Fetur:Kwatanta Najeriya da Saudiyya kamar kwatanta baki da fari ne>>TUC ga Buhari
Kungiyar kwadago ta TUC ta bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa kwatancen Najeriya da kasar Amurka da yayi kan karin kudin mai shirme ne kawai.
Kungiyar ta kuma zargi shugaban kasar da goyon bayan cin hanci inda tace idan aka kwatanta Dumbin Arzikin Da Najeriya ta samu to zata iya Mulkar Duniya baki daya.
Shugaban Kungiyar, Quadri Olaleye ne ya bayyana haka inda yace a kowane bangaren ci gana ba za'a hada Najeriya da sauran kasashe ba ko da kuwa na Africa ne.