
Dangote yayi kira ga gwamnatin tarayya ta hana shigo da tumatur kamar yanda ta hana shigo da shinkafa
Shugaban dake kula da kamfanin sarrafa tumatur din Dangote dake Kadawa, Kura a Kano, Abdulkarim Kaita ya bayyana cewa suna kira ga shugaban kasa da ya haramta shigo da Tumatur kasarnan.
Ya bayyana hakane a jiya, Alhamis yayin da yake rabawa manoma 5000 irin tumatur a matsayin wani tsari na tallafawa manoman karkashin shirin babban bankin Najeriya, CBN.
Yace ta hanyar hana shigo da Tumatur dinne kawai gwamnati zata karfafawa manoma su rika nomashi. Yace a baya sun je ofishin Kwastam ds wannan bukata amma basu yi nasara ba.
“We are appealing to the Federal Government to put a total ban on the importation of tomato like what it did to rice,” Kaita said.
“It is only by putting a total ban on tomato importation that the government can encourage farm...