
Jarirai 29,439 ne za’a haifa a Ranar sabuwar shekara a Najeriya>>UNICEF
Asusun dake kula da kananan yara na majalisar dinkin Duniya, UNICEF ya bayyana cewa Jariri 29,439 me za'a haifa a yau, Ranar Sabuwar shekara a Najeriya.
UNICEF ta bayyana cewa a gaba dayan Duniya za'a haifi jarirai 371,504 ne kuma yawan wanda za'a haifa a Najeriya ne zasu kai kaso 6 cikin 100 na gaba daya jariran.
Saidai majalaisar tace a cikin jarirai 8 da za'a haifa, 1 ne zai kai shekaru 5.
Hakanan hukumar ta bayyana cewa yaran matan da za'a haifa zasu fuskanci cin zarafi idan ba'a dauki matakin da ya dace ba.