
Dan wasan Manchester United Alex Telles ya kamu da cutar Covid-19
Alex Telles wanda koma kungiyar Manchester United a wannan watan daga Porto a farashin yuro miliyan 15.4 baya cikin tawagar Ole Gunnar Solskjaer da suka lallasa RB Leipzig 5-0 a gasar zakarun nahiyar turai daren jiya, yayin da kuma dan wasan mai shekaru 27 ya rasa wasan da Chelsea ta rike United 0-0 a gasar Premier League.
Alex telles ya zamo dan wasan United na biyu daya kamu da cutar bayan Pogba kamar yadda manajan kungiyar Ole ya sanar a jiya bayan sun kammala wasan su da Leipzig inda yake cewa, "Telles ya kamu da cutar korona saboda haka ne ya rasa wasu wasanni kuma babu alamun cutar a tattare da shi zai samu sauki bada dadewa ba".
Manchester United bata yi nasarar cin wasa a gidan taba tunda aka fara buga wannan kakar amma jiya ta fara samun nasarara gidan nata cikin salo bayan ...