fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: ‘Yan Banga

Yan bindiga sun sace wasu ma’aurata kuma sun nemi N15m a matsayin kudin fansa

Yan bindiga sun sace wasu ma’aurata kuma sun nemi N15m a matsayin kudin fansa

Tsaro
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani malamin mai suna Mista Paul Aluola da matar sa a Ewatto, karamar hukumar Esan South East da ke jihar Edo.   An sace ma'auratan ne yayin da suke kan hanyar Ewatto-Ubiaja kusa da gadar Ena River inda rahotanni suka ce 'yan bindigar sun bude wuta a kan motarsu wanda ya tilasta su tsayawa sannan suka dauke su zuwa cikin dajin da ke kusa da Okhuessan.   Wata majiyar dangi ta tabbatar wa manema labarai da yammacin ranar Talata cewa masu garkuwan sun bude tattaunawa da dangin kuma suna neman kudin fansa na Naira miliyan 15.
A bamu dama, a shirye muke mu yi maganin ‘yan ta’adda>>Kungiyar ‘Yan Banga

A bamu dama, a shirye muke mu yi maganin ‘yan ta’adda>>Kungiyar ‘Yan Banga

Tsaro
Kungiyar 'yan banga ta kasa, VGN ta bayyana cewa, a shirye take ta yaki ta'addanci a Najeriya idan aka bata dama.   Kungiyar ta bayyana hakane a yayin da ta gudanar da wani tattakin nuna goyon baya ga jami'an tsaro a Abuja, jiya Litinin. Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar, Mukhtar Dahiru ya bayyana cewa yaki da matsalar tsaro aikin kowa da kowa ne shiyasa suke nuna jajircewarsu da kuma niyar taya jami'an tsaro aiki.   Yace suna kira ga majalisa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari su basu damar shiga harkar tsaro ta kasa a hukumance dan suma su bada gugummawarsu.