fbpx
Monday, May 23
Shadow

Tag: ‘yan Bindiga

Da Dumi Duminsa: Yan bindiga sun kashe sojoji 17 da wasu mutane uku a jihar Kaduna

Da Dumi Duminsa: Yan bindiga sun kashe sojoji 17 da wasu mutane uku a jihar Kaduna

Breaking News, Tsaro
Yan bindiga sun kai wani mummunan hari a sansanin sojoji dake karamar hukumar Birnin Gwari a jigar Kaduna. Inda suka kashe sojoji 17 da wasu mutane uku hadda yan banga guda biyu, kuma sun jigata sojoji 40 wanda yanzu haka suna asibitin soji na 44. Yan bindigar sun kai wanna harin ne da misalin karfe uku na dare, kuma an samu labari cewa sun tafi da makaman sojin bayan sun gama bude masu wuta.
Abin tausayi: Yan bindiga sun bude wuta sun kashe mutane goma, sun jigata 19 yayin da ake gudanar da bikin Zareeci na shekara-shekara a jihar Plateau

Abin tausayi: Yan bindiga sun bude wuta sun kashe mutane goma, sun jigata 19 yayin da ake gudanar da bikin Zareeci na shekara-shekara a jihar Plateau

Breaking News, Tsaro
Kusan mutane 10 ne suka rasa rayukansu yayin da 19 suka jigata bayan yan bindiga sun bude wuta yayin da ake gudanar da bikin Zareeci a karamar hukumar Bassa dake jihar Jos. Yan bindigar sun kai harin ne ana tsaka da gudana da bikin na Zareeci a daren ranar sati, wanda bayan bikin ne suke fara gudanar sabon kakar noma. Amma yan bindigar sun watsa bikin wanda suke gudanarwa a kowace shekara. Mutanen da suka jigata suna asibiti suna jinya yayin da kuma suka yi kira ga gwamnati data inganta tsaro akan hare-haren da aka kai masu.
Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sunyi garkuwa da mutane uku a Ayobo dake jihar Legas

Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sunyi garkuwa da mutane uku a Ayobo dake jihar Legas

Tsaro
Yan bindiga sun kai hari anguwar Ayobo dake jihar Legas tsakanin ranar juma'a zuwa lahadi inda suka mamaye wasu gudaje suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutane uku. Sakataren masu gidajen anguwar Mr. James ya bayyanawa manema labarai na NAN cewa yan bindigar da sukayi kashe mazaje biyu kuM sukayi garkuwa da mata biyu ran juma'a sun sake yin garkuwa da wani a ranar lahadi. Kuma ya kara da cewa yan bindigar sun tafi dasu ne cikij jejin dake bodar Legas da Ogun a cikin jirgin kwale-kwale. (more…)
Yan bindiga sun kona ofishin yan sanda na biyar a jihar Imo

Yan bindiga sun kona ofishin yan sanda na biyar a jihar Imo

Tsaro
Yan binda sun cigaba da kona ofisoshin hukumar yan sanda a jihar Imo, inda a ranar juma'ai suka kai hari ofishin jami'an na Mbieri dake karamar hukumar Mbaitoli. Ofishin ya kasance na biyar da yan bundiga suka kona a jihar Imo bayan sun kona ofisohin Okwelle, Omuma, Isu da kuma Umuguma. Hakan duk ya faru ne a cikin wata daya kacal da yan bindiga suka takurawa jihar suke ta kai hare hare a wurare daban daban.
Da Dumi Dumi: Yan bindiga sunyi garkuwa da miji da mata da yaransu biyu a jihar Kaduna

Da Dumi Dumi: Yan bindiga sunyi garkuwa da miji da mata da yaransu biyu a jihar Kaduna

Breaking News, Laifuka, Uncategorized
Yan bindiga sun kai wani mummunan hari a anguwar hayin Dan Mani dake karamar hukumar Igabi Jihar a Kaduna. Inda wani mazaunin anguwar ya bayyana cewa sun kashe wani mutun mai suna Auwalu Mai Maciji kuma sunyi garkuwa da wani Alhaji Hussaini da matarsa da kuma yara guda biyu. Ya kara da cewa yan bindigan sun kai su takwas kuma su mamaye anguwar ne da misalin karfe uku na dare, yayin da suka zo da manya manyan makamai a hannun su.
Da Dumi Dumi: “kar a sake yin taken Najeriya a makarantu”>>Yan bindiga suka gargadi yan jihar Imo

Da Dumi Dumi: “kar a sake yin taken Najeriya a makarantu”>>Yan bindiga suka gargadi yan jihar Imo

Breaking News, Laifuka
Yan bindiga sun turawa yan garin Owerri dake jihar Imo wasikar gargadi inda suka manna wasikar a wurare daban daban na garin. Wasikar tasu na cewa kar a sake yin taken Najeriya a makarantu, sannan kuma duk ranar litinin babu aiki a garin koda kuwa kamfani ne ko kutu, ko kuma keke napep. Yan bindigan sun kara da cewa basa son ganin jami'ai dauke da bindigu a yanken Biafra face yan ta'adda, idan kuma ba haka ba duk abinda ya faru ba ruwansu don sun rigada sunyi gargadi.
Da Dumi Dumi: yan ta’adda sun kashe mutane biyar, sunyi garkuwa da mutane 17 a jihar Kaduna

Da Dumi Dumi: yan ta’adda sun kashe mutane biyar, sunyi garkuwa da mutane 17 a jihar Kaduna

Breaking News, Laifuka
Yan ta'adda sun kashe mutane biyar sannan kuma sunyi garkuwa da mutane hudu a Dogon Dawa, layin Mahauta da Tabanni a karamar hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna. Wata kungiya a karamar hukumar ta bayyana cewa kwanan nan yan ta'addan sukayi garkuwa da mutane 17 a karamar hukumar. Shugaban kungiyar Ibrahim Abubakar Nagari ya bayyana cewa a ranar 15 ga watan maris yan bindigan sun hallaka Haruna Tanko da wasu mutane biyu, kukm sunyi garkuwa da mutane takwas.
‘Yan Bindiga Dubu 30 ne ke ta’asa a Arewa amma jami’an tsaron dake yaki dasu basu kai Dubu 6 ba>>Gwamna Matawallle

‘Yan Bindiga Dubu 30 ne ke ta’asa a Arewa amma jami’an tsaron dake yaki dasu basu kai Dubu 6 ba>>Gwamna Matawallle

Tsaro
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa, 'yan bindiga Dubu 30 ne ke a jihar Zamfara da wasu sauran Jihohi 5 na Arewa.   Ya bayyana cewa akwai gungun 'yan Bindiga sama da 100 a duka jihohin kuma a kowane gungu ana samun 'yan Bindiga akalla 300.   Alhaji Ibrahim Magaji Dosara, kwamishinan yada labarai na jihar ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a Kaduna, Ranar Juma'a.   Ya bayyana jihohin da Zamfra, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina da Naija. Inda yace kuma jami'an tsaron dake yaki da wadanna 'yan bindigar basu kai dubu 6 ba.   The Governor spoke through the newly appointed State Commissioner for information, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara, at a news briefing in Kaduna on Friday. He listed the states as follows Zamfa...
‘Yan Bindiga sun yaudare mu da Tubar karya suka samu kudin sayen makamai>>Gwamnan Jihar Naija

‘Yan Bindiga sun yaudare mu da Tubar karya suka samu kudin sayen makamai>>Gwamnan Jihar Naija

Tsaro
Gwamnan Jihar Naija, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa, 'yan Bindiga sun yaudaresu da sunan cewa sun tuba inda suka samu kudi dan sayen karin makamai.   Gwamnan ya bayyana hakane yayin da yake ganawa da 'yan Bijilante a karamar Hukukar Mariga inda yace sun dakatar da Sulhu da 'yan Bindigar saboda yaudarar da suka bullo da ita.   Yace suna da shaida akan yanda 'yan Bindigar suka rika tubar karya. Yace nan gana idan za'a musu Afuwa ba za'a rika basu kudi ba, saidai Sana'a. ”From experience, it has been discovered that the repentant bandits, after collecting cash from the dialogue option, they will purchase more weapons and return to their old ways of banditry.” Mr. Sani-Bello said.   ”Any bandit that surrenders his weapons and repents from his heinou...