
Ba za’a iya Ci gaba da ciyar da ‘yan Gudun Hijira ba, Akwai rana 1 da muka kashe Sama da Biliyan daya wajan basu Abinci>>Gwamna Zulum
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya koka da cewa ci gaba da ciyar da 'yan gudun hijira ba tare da samar musu madora wajan samun na kansu ba abune da bazai dore ba.
Gwamnan ya bayyana hakane Ranar Alhamis din data gabata a yayin da ha karbi bakuncin wakilan majalisar tarayya da suka kai masa ziyara a fadarsa dake Maiduguri.
Ya jinjinawa gwamnatin tarayya kan samar da ma'aikatar kula da yankin Arewa maso gabas ta NEDC inda yace ta kawo saukin rayuwa ga yankin.
Saidai yace akwai matsalar karancin abinci a yankin. Gwamnan yace 'yan gudun hijirar ba zasu iya ci gaba da dogaro da abinda kungiyoyin agaji suke basu ba.
Yace abinda kawai zaka ji idan ka shiga sansanonin 'yan Gudun hijirar shine zaka ji suna cewa suna son komawa gidajen su. Yace...