
Yan Shi’a sun yi zanga-zangar neman sakin Zakzaky a Kaduna
Duk da haramta kungiyar da Gwamnatin tarayya data jihar Kaduna suka yi, kungiyar Shi'a ta IMN sun fita zanga-zanga a Kaduna dan neman a saki shugabansu, Sheikh Ibrahim Zakzaky.
'Yan shi'an sun yi zanga-zangar akan titin Ahmadu Bello Way zuwa Leventis. Sun nemi a saki Zakzaky da matarsa inda suka ce kotu ta bada belinsu amma basu san dalilin gwamnati na ci gaba da tsaresu ba.
Zanga-zangar na zuwane shekara 5 bayan kama Zakzaky a Zaria inda mabiya kungiyar suka yi Arangama da sojoji.