
Karya aka musu basu saci komai ba: Hukumar ‘Yansandan Najeriya ta yi martani kan Wannan Bidiyon da aka ga matasa na dukan ‘yansanda a Legas bisa zargin satar waya
Hukumar 'yansandan jihar Legas ta musanta cewa, wasu 'yansanda sun saci waya a kasuwar Computer Village wanda har ta kai ga ana dukansu.
Kakakin hukumar, Ademuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka inda yace hankalinsu ya kai kan waji Bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta inda aka ga wasu bata gari na dukansu bisa zargin sata.
Yace ba gaskiya bane, abinda ya faru shine, 'yansandan sun je aiki ne wajan dan kama kayan da basu da inganci, yace kawai shine wasu 'yan daba suka zo suna ihu suna zaginsu suna cewa barayi ne, suka koresu da gudu, ba tare da sun sami nasarar yin aikin ba.
Yace kwamishinan 'yansandan jihar Legas, CP Hakeem Odumosu ya bada umarnin yin bincike akan lamarin.
Kalli Bidiyon cin zarafin 'yansandan a Kasa:
The HP Ele...