
Hukumoni sun saki masu zanga-zangar SARS da aka kama a Legas da Ogun, An yafe musu
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya bayyana cewa, ya bada umarnin sakin matasa 3 masu zanga-zanga da aka kama a jihar.
An kama matasan, Adeniji Sodiq, Mutairu Faruq da Olatoye Joseph inda 'yansanda ke neman kotu ta basu damar tsaresu tsawon kwanaki 60 dan bincikwn laifin da suka aikata.
Ana zarginsu da yunkurin kisa da kuma lalata wata mota ta Miliyan 100. Ga sanarwar da hukumar 'yansanda ta bayar bayan kamasu.
“That you, Adeniji Sodiq ‘m’, Mutairu Faruq ‘m’, Olatoye Olalekan Josep ‘m’ on the same date, time and place in the aforesaid magisterial district did attempt to kill one Ajagbusi Taofik ‘m’ by hitting him with dangerous weapons and thereby committed an offence contrary to and punishable under Section 320(1) of the Criminal Code, Laws of Ogun State, ...