
Na dauki Alhakin faduwar da APC ta yi a zaben Edo>>Shugaba Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a matsayin sa na shugaban jam'iyyar APC ba zai tsallake daukar alhakin faduwar zaben da jam'iyyar tasa ta yi a jihar Edo ba.
Yace kuma 'yan Najeriya su sani yana matukar girmamasu, kuma yana sane da alkawarin da ya dauka na yin mulki, kuma tsaronsu yana hannun Allah sannan yana hannun Gwamnati da yake jagoranta.
Yace yana son tafiyar da Najeriya akan gaskiya da rikon amana sannan kowa yayi aiki Tukuru dan cimma Nasara.