fbpx
Monday, August 15
Shadow

Tag: Zakka

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kafa Kwamiti na Musamman Don Tattara Zakka

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kafa Kwamiti na Musamman Don Tattara Zakka

Siyasa
An kafa kungiya ta musamman a Kano wadda zata tilasta karɓar Zakka daga attajirai da ƙungiyoyi don sadaka. Zakkah wani nauyi ne na addini da yake bukatar musulmai su ba da wani bangare na dukiyoyinsu kowace shekara don sadaka. An yi amannar cewa gudummawar na tsarkake abin da ake samu kowace shekara wanda ya wuce abin da ake buƙata don samar da mahimman bukatun mutum ko iyali. Kwamitin mai wakilai 11 ne Hukumar Zakkat da Hisbah ta Jihar Kano ta kafa. Shugaban hukumar, Usman Yusuf ya ce "Yayin da watan Ramadana ke karatowa, akwai bukatar baiwa marassa karfi da kuma tallafa musu." Zai ziyarci bankunan Musulunci da mashahuran mashahuran attajirai don tunatar da su abubuwan da ke kansu. "Wannan kwamitin, kamar yadda daga yau zai je Tahir Guest Palace, Ni'i...
Ba zamu yi wasa da shari’ar Musulunci ba a lokacin mulkina>>Gwamna Matawalle

Ba zamu yi wasa da shari’ar Musulunci ba a lokacin mulkina>>Gwamna Matawalle

Uncategorized
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa ba zai yi wasa da zakka ba wadda daya ce daga cikin abinda Shari'ar Musulunci ta bukaci masu hali su bayar.   Gwamnan ya bayyana hakane yayin da yake karbar Rahoto na musamman da aka yi kan gyaran hukumar Zakka ta jihar.   Yace zakka a matsayin daya daga cikin shika-shikan Musulunci dolene a bata kulawar data kamata musamman a garuruwan Musulmai.   Gwamnan ya bayyana cewa ba zai taba yin watsi da hukumar Zakka ta jihar ba. Ya kuma ce zai yi dukkan mai yiyuwa dan ganin ya bada goyon bayan da ya kamata.   Ya kuma godewa kwamitin zakkar da yayi wannan aiki na bincike da gabatar da Rahoto.  
Yanzu ne lokacin da ya kamata a bada zakka>>Matar Gwamnan Kaduna

Yanzu ne lokacin da ya kamata a bada zakka>>Matar Gwamnan Kaduna

Kiwon Lafiya
Matar gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta jawo hankulan musulmai inda tace wannan lokaci da ake ciki shine mafi dacewar bada zakka.   Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace itama zata bayar da tata zakkar. https://twitter.com/hadizel/status/1247102933726105600?s=19   https://twitter.com/hadizel/status/1247105991130386432?s=19 Ta bayyana cewa itama zata bayar da zakkarta amma a dunkule zata bayar ga wata kungiya da zata sayi kayan abinci ta rabawa mutane. https://twitter.com/hadizel/status/1247118161868197888?s=19 Saidai daga baya Ta tambayi shawarar ko ta sayi kayan abinci ta raba ko kuwa ta bayar da tsabar kudi? https://twitter.com/hadizel/status/1247131511759011841?s=19 Daga baya an bata shawarar bada kudin kamar yanda ...